← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 138

Sashe 21

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Galala din da ta yi hawayenta bai daina zuba a gurbin idannuwanta ba ya saka shi fadin" kin ga wannan da ya saida maki da kika ce giya, sai da ya maimaita sunnan yana zarro ido yana kallonki, kin san me yasa ya yi haka? Domin da kika zo kin ambaci sunnanta bayan du wanda yake mashayi idan ya zo wajen nan kudinsa kawai yake cakewa mai siyarwar ya san kalar da kudinsa zai siyan masa, yar budurwa baki ga sai da ya yi mamaki ba? Dan ya ga cewar baki saba ba, yau ne zaki fara, shi yasama ya zuba maki kankarar nan dan ya dan rage kaifinta a harshenki, aman ba hakan na nufin kaifin nata zai ragu ba gaskiya domin yau ne zaki fara sha, kuma kin ji na rantse maki idan kika sha wannan giyar gaba dayanta zata kasheki ne, dan babar giya ce mai tsada mai karfi, to ke wai mema akai maki da zafi da zaki fara akidar nan?"

Ita da a hayacinta take, ta tabata wannan bawan Allahn sai ta masa tassss da fitsara, aman a yanzun sai ta samu kanta da rike giyar nan taf a hannunta tana kallonsa ta ce" Ka ga mijina ne ya sakeni, mahaifinsa ne ya ce ban cencenci a hada zuria da ni ba, shine aka sake ni"

Bakinsa ya tabe yana amsar kofin giyar ya ce" Sun yiwa kansu asara ai, a kan ya sake ki ne zaki sha giya? Ko shi kadai ya rage a jinsin maza a duniya? Idan su basa sonki dan wani dalili nasu wani saboda dalilin da suke kinki zai so ki, aman idan kika saka kanki a rayuwa irin ta giya kin san me kika cirarwa kanki? Wahala, yar budurwa kin cirarwa kanki wahala ne, kin ga mu bamu iya abu ba, idan muka fara bamu da hankali, bamu iya yi a kadan kadan ba, zamu yi ta kwabra ne ta yadda zata yi mana ila, kin ga giya anfaninta daya ne tak ko mace biyu shine zata saka fatarki ta yo luwai luwai idan kina shan mai tsada sannan zata saka gashinki ya ringa tohowa sosai idan kina shan mai tsada fa, bayan wannaj dukan wani wulakantarwa na duniya zaki hadu da shi sannan ki je kiyama ki hadu da ubangininki, kin ga tun ina yaro dan shekara goma sha biyar yawo da abokanai na koyi taba giya, maganar da nake maki saboda giya babu abinda ban gani ba na gidan duniya, ni dai ban ajiye nawa ba sai na mahaifiyata da nake gurgura ba dare ba rana, y'ata daya a duniya a makaranta a zageta a cikin kawaye a yi mata gori, ke bara na kadaice maki bani da wata daraja ni na sani dan dole ake cakuluwa da ni..........yanzun ki yanke shawara cikin biyu, Au ki tashi na kaiki gidanku, ko kuma ki fara kashe rayuwarki dan kato ya sake ki"

Ido take kikiftawa tana kallonsa kafin take sake kallon kwalbar da ya ajiye mata a gabanta

Idonta ta rintse da yake ta sarra mata kafin taa mike a hankali tana bude bakinta da kuryarta da ta disashe sosai ta ce" Ka ga banma yi sallah ba kuwa, mu je kawai"

Da kwatance har suka karaso kofar gidansu

Ta jima tana kallon kofar da tunanin Allah ya sa yayarta tana gida

A hankali ta kama kofar ta bude ta zirra kafafuwanta kasa zata fita ta ji yana fadin" Dukan mace ta duniya tana da kima, ko me ta zama a rayuwa kuwa tana da daraja, idan ta hadu da wanda ya san darajarta zata kasance macen da ta fi kowa haskawa a duniya, yar budurwa kar ki manta cewar ko me kika gani na rayuwa ke din halita ce mai daraja,, uwa ce ke, y'a ce ke, kanwa ce ke, yaya ce ke, kin ga abubuwan da yawa , idan ba ke fa Walahi babu rayuwa kwata kwata, kar ki shiga gidanku ki dora kuka , ki je ki godewa Allah, zan dawo gobe in sha Allah"

Tabas ta samu nutsuwa a zuciyarta, tabas koda ace bata dawo normal ba, domin abu ne mai matukar wahala, ita a yanzun ALKALAMIN KADARRARTA ya daina firgitata ya dawo bata tsoro, aman kuma ta ji dama dama a zuciyarta na tunasar da wannan mutumen ya yi mata cewar kai kanta da ta yi gidan giya ba shine mafita a rayuwarta ba

A hankali ta tura ta shiga tana gaishe da baba mai gadi dake morewa da kazar da aka miko masa

Da kallo ya rakata da tarin tambaya a ransa na yannayinta, ko hujab babu a jikinta ba wani mayafi hakan ya sa ya ringa adu'ar Allah ya sa ba sakinta mijinta ya yi ba

A hankali ta kama kofar ta shiga da Salama a bakinta tana waige waige

Yayarta dake zaune tana kwaba lalen da take son kunsawa ta dago da sauri tana sauke dubanta a kanta

Yannayinta ya saka gabanta yankewa ya fadi da karfin gaske har sai da ta zabura tana sakin lallen a kasa tana sake kallon kanwar tata da son mikewa lokaci daya haka kuma bakinta ya kwashi inda inda tana fadin" SHUWWAR, me menene? Ina lulubinki shuwwewwwwwwwwww" maganarta ta katse sakamakon faduwa da ta yi ta dalilin kushin dake ajiye domin idannuwanta sun rufe sam ta kasa ganninsa sai da ta tabeta ya kifar sannan ta ankara

Da sauri SHUWWAR ta idasa isowa tana kamata tana fadin" Subahannalah Aunty Hal anta mash-ghouul?"

Hannunta da ta riketa ta kama tana kallonta ta ce" Na zata ko , ko , na zata ko ya sake ki ne da na ga baki da lulubi bayan matan aure sunna suturta jikinsu ne, kin ga ki ringa saka lulubi dan aure ba abin wasa bane"

Dan murmushi ta yi mai ciwo a hankali ta dora kanta a saman kirjin Nahidt dake yi mata nasiha hakan ya saka Nahidt yin tsiittt lokaci daya kafin a hankali muryarta na rawa ta ce" SHUWWAR me yake faruwa?"

SHUWWAR ta dago tana kallonta , ta maida kanta saman kirjinta a hankali ta ce" Ya sakeni, sai dai shi saki daya ya min, kin ga hakan na nufin ta yiwu idan na kuma yin wani auren zai zaunu"

Wannan karron maimakun zuciyar Shuwwar din ta nemi gazawa ta yar uwarta ce ta nemi gazawa
Muryarta a sanyaye ta ce" Shima ya sake ki ne dan an ce ni karuwa ce?"

Ido SHUWWAR ta rintse na kalmar da yayarta ta kirayi kanta a hankali ta girgiza kan nata tana fadin" Aa, bakima shigo cikin maganar ba, kin san me na fahimta.......hasalima ke din kin zamto mahadin Kadarratah ne, aman da ke ko ba ke dole ne rubutacen al'amari zai kasance a kaina, wannan sakin bama dan ke akai min ba, wani soja ne ya saka aka daukomu dan a yi kuraya, a nan dai wa'adin auren nawa ya cika"

Lebenta ta dantse tana son hanna kanta kuka, aman sai da abin ya gagareta ta fashe da kuka tana rike SHUWWAR a jijinta ta ce" Shin mun fi kowa aikata laifi ne da muke fuskantar irin wannan hukuncin a wajen al'uma, menene laifinmu? Me muka yi da zafi haka?, SHUWWAR I'm sorry, I'm sorry dear"

SHUWWAR ta karra kwontar da kanta a sanyaye ta ce" Haka nawa ALKALAMIN KADARRAR yake, Aunty ina tunanin bani da rabon yin aure a duniya"

Wanu kukan NAHIDT ta fashe da shi wanda ya fitar da Zahra'u dake kicin tana soya masu zabuwa da sauri tana fadin" Kamar kuka nake ji NAHIDT"

Jikinta ne ya yi wani irin mutuwa tunda ta ga SHUWWAR rungume a jikin NAHIDT din

Tunda Shuwwar ke koke kokenta idan an saketa bata taba jin tana zubar da hawaye irin na yau ba,
A yau itama da kanta ciwon sakin Shuwwar din ne yaa ringa sukanta a kirjinta har ta kasa tsayuwa a kan kafafuwanta ta karasa da sauri tana dukawa a kusa da su ta rungume su gaba dayansu a jikinta

Kukansu suka sha su su uku
NAHIDT dake kuka tana fadin" Shikenan dan bamu da kowa sai a ringa wulakantamu?, Shi yasa ban sakawa kaina soyayar na yi aure a zuciyata, domin na rigaya na sani cewar babu wanda zai iya jin kaina, babu wanda zai aureni ya zauna da ji domin Allah, ya zamana dan iskama ta kirki yake so mai fitacen usuli, kowa idan ya tashi ta kirki yake so ido rufe, mu kuma da muka kasance a haka ba sai mu karre a haka ba?, Aman SHUWWAR bata cencenci haka ba, Shuwwar ya cencenci ta samu gida ta zauna da mijinta, bata takawa kowa ba, bata kashewa kowa ba, idan takamar mazajen dake sakinta dan ina fita ina harkar badala ina samun naa abincina ne daga yau na daina, walahi na daina, su aureta su kilace min ita dan Allah ba dan halina ba"

A sanyaye SHUWWAR ta sake riketa a jikinta tana fadin" Da ace zasu dube mu bayan mun tuba su dauke mu ba dan su ringa goranta mana ba, su kula da mu domun Allah, aman kin ga Aunty, ko sun aure mun dan su wulakantamu ne, kina gani fa irin soyayar da yake nuna min aman ana kaini ko kallo ban ishe shi ba, yakan shiga ya fita aman banda dakina"

NAHIDT tana kallonta ta ce" kina nufin har yau da ya sake ki babu abinda ya shiga tsakaninki da shi?"

A hankali SHUWWAR ta sada kanta tana jin nauyin irin maganar nan ainun

Fauziya da ta kasance mai sanyin cikinsu aman yau itace da fadin" Dama tun usil bai mana ba, bakya gannin kama yake da munafukai? Fin karfinmu kika yi, a yanzu da ya kasance bai taba ki ba Alhmdulilah, matsiyaci algungumi kuma walahi sai mun kwaso kayanmu harda akwatunnanki!"

Ita kam so take ta kwonta ta huta dan kanta ciwo yake yi mata, dan haka ta nemi da su sama mata wajen kwonciya so take ta kwonta

A wannan daren ta samu soyaya a wajen yan uwanta taamkar zasu maida ita cikin cikinsu, domin a shinfida daya suka kwana gaba dayansu har akai kiran sallar asubah
Chapter 21 · 0% Book details