← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 138

Sashe 93

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nahidt ta juya gareshi itama ta rike shi kam tana girgiza kanta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, mu kuwa da muna da gata menene hukuncin da ya dace da dukkan wanda ya aikata maku haka?, A yanzu na fara tunanin ba da kafarku kuka barmu ba, domin a gidanmu Jaddah baku bari ko kuda ya rabe mu........, shuwwa take cewa baku mutu ba, sai na ce ta yi hakuri kun mutu ta yi hakuri, sai Mama ta nanma ta ce tana ji a jikinta baku mutu ba"

Tunda aka fara kayaniyar nan CHIEF OF ARMY ya samu ya fitar da dayar matar tasa da dukan wani sojan dake iya kallon abinda yake faruwa kafin ua dawo shima ya zauna kusa da matarsa sunna kallonsu zuciyoyinsu a karye gaba dayansu

Kamar an ciro a bakinsa, tunda ya samu lafiya kamar da karfi aka budi bakinsa, domin maganarsa ta yanna cikin ihun a kaishi nesa da kasar nan da ta yanzu ba iri daya bace ya budi baki ya ce" ku yi shiru"

Sai kuma ya yi kitttt da bakinsa, kafin ya sake daukan furucinsa yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une....... Nahidt, Ebtisemmmmmmmm, ashe zan ganku a duniya?"

Gaba daya sai da zuciyar kowa ta karaya a dakin nan, sun kasa sakin junna haka kuma sun kasa daina aikawa junna tambayoyi kowane so yake dan uwansa ya fada masa abinda ya same shi bayan baya nan,

Da kyar Mamansu ta sasauta nata kukan tana rike da kumatun Shuwwa ta ce" Me kuka gani a rayuwa y'ayana?, Ina da ina kuka je? Me ya same ku a wannan katuwar duniyar da ta yiwa yaro girma?, Abansu kana kallon jaririyarka yadda ta girma ?, Oh Ebtinahhhhhhhh"

A hankali IBTISAM ta sake komawa cikin jikinta ta lafe tana ta sauke ajiyar zuciya tana jin a yau bata tunanin idan akoy abinda zai nisantata da kirjin nan na mahaifiyarta, komai girmansa kuwa, itama riketa ta yi tana ta shafa bayanta da kanta a sanyaye idannuwanta a lumshe tana ta jin bugawar zuciyarta ta sake budar bakinta tana kallon Nahidht ta ce" Yar gidan Papanta, ku fada min, ku fada min abinda ya same ku , duda na ganku a hannu mai daraja a gida mai daraja, aman na kagu na san kafin nan me ya same ku, na kagu na san me da me kuka gani na rayuwa koda na rana daya ne na tabata kun san abubuwan rayuwa sosai, oya telll me "

Gabanta ne ya kwonci kwonci ya fadi, dogon hancinta kuwa da ya jajajir sai ya done , watau ta rasa wadataciyar iskar ja ta shi du irin girmansa

Jiki a mace ta sada kanta ta kasa furta masu koda A ne,

Hakan ya sa Mahaifiyarta tsatsareta da idannuwa gabanta na faduwa

Zata sake yi mata magana Maman Muhayta dan yi gyaran murya a sanyaye ta ce💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 5️⃣4️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Zata sake yi mata magana Maman Muhay ta dan yi gyaran murya a sanyaye ta ce" Maman SHUWWAR inaga me zai hanna ku ci abinci ku dan huta kafin ku yi zaman nan?"

Mama ta kalleta da mamakin jin wani sunna kuma, hakama Abansu sai ya samu kansa da maimaita sunnan a cikin ransa yana jin sam bai san sunnan ba, kai sunnanma sam bai yi masa ba, dan haka sai ya bude bakinsa ya ce" Wacece SHUWWA ?"

Da sauri ta dago tana kikifta ido tana kallon Mahaifinta, sai kuma ta kalli Mama da sauri tana ji kamar ta ce gaskiya a yafe mata sunnan nan ta yafe shi duniya da kiyama, to yau itace zata cewa mahaifinta dan wani abu daban ya sa ta tsani sunnan da ya saka mata? Sunnan nan nata fa ta sh kama rigima irin ta mata da miji sunna gardamar sunnan da ya fi dadi ita ta ce na Nahidt shi kuma yace haba dai na Ebtisemmmmmmmm dinsa ya fi dadi, sai kuma kwatsam a ce taa cenza? Kar dai ya gaura mata mari daga dawowarsa?

Da sauri ta sada kanta gannin ya kalleta sakamakon Mama da ta kalleta hakan na masa nuni da IBTISAM dinsa ce ta dawo Wata wai SHUWWAR ? To wa ya cenza mata sunnan kuma?

A nutse ya ce" Ku yi hakuri Hajia, ku yi hakuri dan Allah, aman idan ba damuwa zan so a fada min maganar nan da mamansu ke son sani itama, domin zan iya rantsewa tunanin inda suke ya saka na iya jurewa, ba zan iya cin komai ba sai na ji abubuwan nan"

Ai kam ido hudu sukai da Nahidht din da SHUWWA

Sai kuma suka sake sasada kawunansu

Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce" In sha Allah ni zan fada maku abinda na sani, aman dan Allah ina mai rokarku da ku fuskanci alkhairin dake tare da nanauyan kadarku baki daya, ku yi hamdallah ga ubangiji tunda har ya kasance ku dukanku kunna raye, to fa mai saukin kennan......"

Da ido suke kallon Mama tana bayani a sanyaye a nutse, tun sunna sama har suka dawo kasa suka zazauna suka rike hannayensu su dukansu kowace zuciyarta tamkar zata buga dan tsoro haka iyayensu dake sauraron maganar sunna gannin tamkar a wai ne har Mama ta dire aya wada shima Chief of army sai yau ya ji wannan maganar da tarin tausayi yake kallon yan matan da iyayensu suka yi mutuwar zaune sunna kallon Mama

Tabas maganar ta dake su, idan a dazu mahaifinsu bai zubar da hawaye ba a yanzun kam idannuwansa zubarwa suke ba kakautawa, wai a haka Mama bata budi bakinta t fadi sana'ar me Nahidt din ke yi dan ciyar da yar uwarta da ita kanta ba, sai dai dan hausa ba bagwari bane, a dukan maganar ba'a fadi ga wanda ya dauki nauyinsu kafin yanzu ba, bakuma aka fadi ga sana'ar da suka yi dan ciyar da kansu ba, dole mutun zai gane wani abin a ciki

Jiki na rawa Nahidt ta ce" Dan Allah ku yi hakuri"

Mama a hankali ta dora kanta a gefen kafadar mijinta tana tuna rayuwarta, a lokacin da ta biyewa soyaya ta samu d'an d'anta ta yadda ta gudu saudiya, watau dai ita ayar nan bata mantuwa bata tsanlake?
Hasbunnalahu wani'imal wakim,
Muryarta na rawa ta ce" Kunna nufin kunnga Hamza? Hamza har ya kusa aurenki?, Sannan kun ga ahalina har sun nuna sun neme ni?, Kunna nufin Hajara ce ta ce maku mun mutu?, Kunna nufin ku din nan ne kuka yi rayuwa kamar ta wulakantatu?"

Da sauri Shuwwa ta rarafa ta koma kusa da kafar Mama, sai dai tun kafin ta zauna mahaifinta dake hawaye ya saka hannunsa ya share a kausashe ya ce" Ki dawo nan ki zauna ki fuskanceni Ebtisammmmm, kece harda su cenza sunna? Marainci hauka ne,? Nahidt dan bama nan kika wulakanta kanki? Ba gwara ace aikatau kuka yi a gidan masu iko suka wulakanta ku ba, ba gwara ace wankau kuke yi ko tallah kuke dorawa a kawunnanku ba?, Yanzun a duniya ana rasa masu tsawatarwa da babar bulala a cikin anguwanni dan hanna halaya irin na mutanen banza ba?, Da ba dan Allah ya sa MUHAMMAD na tare da ku ba da an tozartaku a cikin kasata? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une"

Dad ne ya mike tsaye da sauri yana kallonsa

Sai kuma ya juya wajen Mama , ya sake juyowa yana kallonsa
Gaban goshinsa ya dafe ya juya ya fice a falon yana mai danna kira

Bata jima tana ringin ba aka daga

Hankalinsa a tashe ya ce" Na san kana da labarin batan magajin garin nan harma kannin mahaifinsa ya hau kujerarsa, ka san ni mahaifin nasa ne ya rikeni na tsayin shekara hudu a lokacin da na je karatu harma ya bani talafi , zaman da na yi tare da shi na san ya malaki d'a daya tal wanda bayansa bai sake samun haihuwa ba du kiwa da irin yadda yake da mata, MUHYIDEEN yana fita da ji fada ina gannin yannayin da yake yi idan yana cikin hali na farin ciki ko akasin hakan, ka ga muryar bakon nan, da yannayinsa gaba daya sai yake tuno min shi, baban abin tashin hankalin wai anya tunda wannan bawan Allahn ya bata an neme shi kuwa? Ni kaina ba shi ba, ko mahaifinsa na manta kwata kwata da shi bayan mutumen nan shi ya bada ni cikin zakarun da za'a zaba su zama manyan sojojin kasa, ka ga yanzun kamar daga sama wai sai nake ta tunaninsa dan wannan bawan Allahn na magana, haka Takawa yake lokacin nan sai ka ga magana ta gagareshi,aman idan bakinsa ya bude kuma sai ka sha mamaki, uwa uba irin yadda yake nuna fushinsa haka takawarmu yake fa........ MUHYIDEEN wanene wannan mutumen?"
Chapter 93 · 0% Book details