← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 138

Sashe 33

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali SHUWWAR ta girgiza kanta tana fadin" Mun je, mun sake zuwa, mun fadawa mutane sun tayamu nema bamu ga gawarwakinsu ba har aka yi suturar mamata ranar juma'a , a lokacin kuma aka hanna mu shiga dan karancin shekarunmu aka koremu, daga baya mun je kaburbura mun yi ta bin sunnaye aman kun san yawan wajen da girmansa har aka kamo mu aka dawo da mu kasar nan bamu samu muka gama zagayen makwontan ba, sai dangana muka yi kamar yadda makociyarmu ke fada mana cewar mu yi hakuri mu bisu da adu'a, sun rigaya sun rasu babu yadda muka iya hakan muka yi hakuri har aka gama aikin haji aka koma daga nan aka dawo da kame, muka taki rashin sa'a wata fita da mukai zamu je gidan da muke goge goge aka kama mu aka kawo mu kasar nan"

Innalilahi wa inna ilaihi raj'une..... shine abinda aban Hamza ke maimaitawa kansa a kasa yana girgiza kan nasa
Gogon Hamza ta yi gagawar fadin" Dan Allah bayan Buzuwar bata da wani sunnan ne? Yar budurwa kamar na ji kin ambaci wani sunnan bayan wancen?"

Du irin yadda ta cika da tsoron maimaita sunnan da ta taba gani a takardar mahaifiyarta haka ta budi bakinta ta ce" *TINNANA* "

"Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam, dan girman Allah yaya wadinnan yayan Tinanarmu ne, walahi y'ayanta ne Innalilahi wa inna ilaihi raj'une TINANA ta rasu? Ta rasu bamu nemi gafarayar junna ba? Ta rasu bamu nemi afuwar juya mata baya da nuka yi dan ta samu ciki ba? Ta koma ga mahalincinta da mikinmu a zuciyarta? Wayo Allahna"

Hamza da cikinsa ya juya daga zaunen da yake ya yi raf da hannun babansa yana zarro ido ya juya yana kallon baban nasa bakinsa na rawa ya ce" Babana mu je a daura auren mana, daga baya sai a dawo a tatauna inaga kamar sun san su Shuwwana ne ko?"

Da tausayi mahaifinsa ya kalle shi yana jimke hannunsa da kyau ya maida dubansa kan CHIEF OF ARMY da ya yi dan gyaran murya ya kalli NAHIDT, ya kuma kallon Hamza, ya kalli Shuwwa ya maida dubansa kan iyayen nasu, a tausashe ya furta" Subahannalah Astagfrullah, subahannalah "

Gogon Hamza ta girgiza kanta tana fadin" Wani daurin aure Hamza, wadinnan kannenka ne uwarku daya da su Hamza, mamanku daya fa da su, ai ka san ba maganar aure tsakanin jini daya ko Hamza"

Ido ya zarro yana son mikewa tsaye jikinsa na rawa haka Shuwwa itama ta mike tsaye lokaci daya idannuwanta na firfitowa waje ta juya da sauri tana kallon Hamza sannan ta juyo tana kallon NAHIDT da ta yi mutuwar zaune hannayenta bibiyu saman kanta

Maimakun ta ji salati ya fito daga bakinta sai wani ihu da ya fito da karfi ta kurma shi tana dora hannayen nata itama su biyu a saman kanta
Idannuwan nan nata masu rukowa waje ta karra rukowa a birkice ta furta" Auntyyyyyyyyy" sai kuma luuuuuuuu ta tafi sakamakon juwar da ta kwasheta ta nemi makata da kasa

A tatare suka nemi tareta ana ta di kira da salamewa daidai wayar Chief of army ta kuma daukan tsuwa hakan ya sa cike da tausayi ya mike yana amsawa

A birkice NAHIDT ta kalli Malan tana fadin" Muhammad, ba za'a daura auren ba kennan?"

Malan gannin sun rikice yana kallonta ido cikin ido ya ce" Na zata farin cikin kun hadu da ahalinku ya fi komai a yanzu NAHIDT ?"

Hamza dake rike sa Shuwwar wace ta dora kanta a damtsen hannunsa idannuwanta rufe ruf ya ce" Haba Aban shuwwa, wani irin farin ciki kake so mu tsinci kanmu a ciki? Tabas ni na ji farin cikin gannin kannenaina, aman hakan na nufin ta haramta a gareni? Aure na uku kennan fa zai lalace min kamar masu bakin uwa ? Ita kuwa na biyar fa kennan idan ban mantaa irgen ba fa?"

Malan zai kuma yin magana Ganaral ya ce" Son, dube ni, ka kwontar da hankalinka mana, na san kana kulace da yan uwan mahaifiyarka aman inaga wannan abin farin ciki ne ga kowa koda hakan na nufin an fasa daurin aurenka ai Allah zai baka wata, itama hakuri zata yi haka Allah ya nufa da rayuwarku ku dukanku"

NAHIDT ta karkata kanta ta ce" Ba zaka gane bane Baba, ba zaka gane ba walahi, wayo Allahna Shuwwa tashi mu tafi kin ji? Tashi"

"Ina zaku je? Kuma kun yi mana fushin ne? Kuma ba zaku sauraremu bane? Daga nan babu inda zaku nufa da ya fi garin Tanus" gogonsu ta fada da dan alamu na iya gaskiyarta ta fada kennan hakan ya saka Shuwwar kureta da ido tana kankance idannuwanta dake ruruwa da ruwan balaki tana niyar yin wata maganar dan ba wannan mata amsa daidai da abinda ta aikata mata CHIEF of army ya sake yin magana a Karro na biyu da alamu na yanke hukunci kamar yadda ya saba yana kallon malan da abokinsa da Aban su Hamza ya furta " My freind Bismillah "

Yana gama fada ya yi gaba kadan hakan na nunin yana son yin magana da su a kebance

Watau amintakar dake tsakanin CHIEF OF ARMY da tsohon GANARAL baban Hamza amintaka ce dadadiya mai karko, sun jima tare hakan ya sa du rike sirri irin na soja sun san sirrikan junna, zan iya cewa da ba dan nisa dake tsakaninsu ba da kulun sunna mane da junna ne, aman koda nisan nan bai hanna masu motsi kadan kwalawa junna kira dan su sanar da damuwar junna wa junnansu ba a ko wani irin lokaci, kai kira ko na tsakaninsu da matayensu ne sukan sanarwa junnansu, zan iya cewa CHIEF OF ARMY tunda ya rasa amininsa sai ya samu yake amintakar da tsohon ganaral, duda bambancin shekarun dake tsakaninsu aman kuma sun san junna sunna mutunta junna

A nutse ya furta" A bayane yake maganar ahali ce ta kama, a yanzu inaga magana ce mai karfin gaske ta kama, Kai ka isa da su dukansu , kai ka isa da Hamza, kai kuma Malan ka isa da yan matan gidanka, so barin wannan lamari a haka inaga zai sake traumatiz kwonciyar hankalin yarinyar cen da kuma shi kansa Hamza, déception na soyaya baban abu ne mai ilar gaske da ba kowa ke iya shanyewa ba, nd furucin yayartan cen ya sakani a cikin halin tunani da ta ce kennan dan iyayensu sun rasu shekenan ba zasu auru ba?, What's t wrld ? Whts t prblm da har zasu rinha fuskantar haka? Ban zauna da su ba aman yannayin shigar yayar da ya saka ta ratso gabanmu haka duda a gigice take na fuskanci akoy lamari na rashin jin magana a cikin zamansu, but ba shine dalilin da zai sa a ringa sake turesu ba, ya dace ne a janyo su, a nuna masu soyaya, summa ai y'aya ne kau? , Idan ba damuwa inaga kar ku fasa daura masu aure a yau"

Dukan furucinsa da yake yi sun matukar nutsu sunna kuma fahimta har zuwa furucinsa na karshe wanda ya saka kowanensu ya masa kallo irin nasa na rashin fahimta, harma amininsa ya dan kamo h💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣7️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Dukkan furucinsa, sun nutsu ne, sunna fahimtarsa, kuma har kasan zuciyarsu sun gane , sun kuma gamsu da bayanansa har kawo wajen da ya furta a daura aurensu, hakan ya sa kowa ya dago da kalar nasa fahimtar da ya fara yi masa yana kallonsa da hakan
Amininsa ne ya riko hannunsa yana fadin" Father Lieutenant, ka kuwa fahimci rigimar cen da ta kacame? Ana nufin uwar da ta haifi Hamzana ita ta haifi yan matan cen, ta ina kake so a daura aure kuma? "
Chapter 33 · 0% Book details