← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 138

Sashe 117

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har sai da ya cenza mata ruwan nan kusan sau uku sannan ya ciko mata tsaftataciyar buta ya ajiye yana neman kamata dan ta gabatar da wankan tsarki, a nan ne ta samu da kyar ta nemi da ya barta zata iya
Hakan ba dan ya so ba ya bata dama ya fita a bayin bayan ya yi nasa wankan ya je ya shiga kimtsa gadon duda ba wani iyawa ya yi ba, aman a yau da kansa ya kwatanta gyara gadon dan kuwa ya san hajia mai shinfida ko wuta yake hadiya ba zata yi ba!

Ta jima a ciki, domin bayan ya fitan bata fito na wani ruwan ta kuma tarawa mai zafin gaske ta sake zaunawa da kyar tana matse hawaye hadi da girgiza kanta tana hasaso azabar nan da ta ji yau idan haihuwa ta fita azaba ai ta shiga ukunta!

Sai da ta ji ta kara jin dama dama kadan sannan ta kama da kyar ta fito tana wara kafa ta samu ta tsaftace jikinta, ta janyo tawul dinsa ta raba da kyar tana jin gaba daya jikinta fayau wani irin ba karfi da kwari a jikinta ta dadafa ta fito daga bayin tana sake rintse Idannuwanta ta yi turus tanai masa kallon kallo

Dan jan hancinsa ya yi da pain killer din da yakr sha lokaci zuwa lokaci dan magance dan ciwon jiki haka da kofin ruwa ya karasa kusa da ita a tsayen ya nuna mata da ta bude bakinta
Ba yadda ta iya haka ta bude bakin shi kuma ya saka mata hadi da kafa mata ruwan
Tana gama sha ua sakar mata murmushin da ya sakata sake kafe shi da ido

A hankali ya ce" Wai me ya cinye bakin, ki min magana mana"

Ita dai ta dawo daga rakiyar kililin kasau macijin kumbarsa, sani ne bai yi ta gama gane cewa shi din nan idan ya samu makararen waje zai karta ne kawai, dan haka zata fuskance shi su fuskanci junna , dama ta jima da sannin ba kaunarta yake yi ba, ya jima burinsa ya saketa, yanzun kam ta dangana da auren, ta hakura haka, ta yarda aure ya fi karfinta ita ke masa shishigi, ta hakura duniya da kiyama ta kamanta ai sosai ta kamanta

Bed din da yake nuna mata ta bi da kallo, ta sake kallonsa kafin ta girgiza kanta a hankali tana sake matse idannuwanta

A sanyaye ya ce" Oh sorru Ebti, kin san dai nima ba zan karra ba bayan na ga kin ji ciwo ko, saima da safe na kaiki wajen su Mama su fada mana me zaki sha ki warke, plz zo na kwontar da ke ki huta kin ji?"

Bakinta ta bude muryarta a shake ta ce" Ni dakina zan je, ni ni ba zan iya ba, ba sai mun je tare wajen su maman ba, daga nanma ka bani takardata sai na je da kaina wayo Allahna zafi nake ji da ina magana wayo nan dina....."
Ta idasa da nuna Wajen tana neman durkushewa

Du irin yadda maganar ya bata takardarta ta soke shi gannin zata kai kasa a durfafe ya durfafeta ya kuma dauketa a hankali ya kaita saman gadon ya shinfidata kafin ya haye ya sakata a kirjinsa a hankali ya ringa dan shafa bayanta ta yadda du irin yadda ta kai fa kokowar ya barta har ta yu laushi ta yi shiru tana sauraron yadda zuciyarsa ke dokawa, kafin a hankali idannuwanta su ringa yi mata nauyin gaske har maganin nan ya ci karfinta barcin ya yi awon gaba da ita

Sai da numfashinta ya tabatar masa ta yi barci mai karfi sannan ya cireta a jikinsa a hankali ya zubawa fuskarta ido

Dan murmushi ya yi a hankali ya manawa lebenta kiss a kasan zuciyarsa yana ayana' Na dauki maganar na sake ki a matsayin zafin ciwo da kika samu a tare da ke, domin an ce dukan macen da bata tabaa sannin da namiji ba ko yar karamar yatsa aka zo da niyar saka mata a jiki sai ta ji zafin haka balatana jikin namiji ginane, tabas nan din gonata ce, ke din kuma Allah ne ya bani, ko ba komai ai da kunya yarana su ji matar da suka aura min da gumin aljihunsu na saka itama?, IBTISAM kece sirrina, kuma yadda Allah ya tsaftace min ke, ya karre min ke du irin gwagwarmayar da kika ganni ta rayuwa na yarda cewa Allah ne ya ajiye min uwar y'ayana a kilace da irin kilacewarsa, Allah ya yi maki albarka ya karre min ke My Princess'

Da wannan ya sake komawa ya tofeta da adu'a shima ya yi ya shafa sannan ya kwonta ya sakata a jikinsa ya shiga neman barci

_____________________________________

Abinda ke sake yi mata yawo a jiki har ya haye ya nufo kunnenta ta saka hannunta ta kuma dokewa tana korewa sannan ta yi mika kadan da niyar kuyawa hadi da jan bargon da take lulube da shi tun bayan sallar asubahi da ta yi ta koma ta nade tanama tunanin du inda al'adarta take a wunin yau ko wayewar gobe zata ganta ta kuma shan maganin ciwon nan da ya bata domin sarai ta ji dadinsa hakama da ta sake shiga ruwan dumin sosai ta ji dama dama a kan abinda take ji, dan kuwa barta dadewar da wajen ya yi ya mutu murus in ba motsawa ta yi da karfi ba bata jin zafin, hakan ya sa ta smau wani lafiyayen barcin da yinwa bata samu damar tashinta ba

Dan murmushi ya yi ya sake anfani da gashin dawisun da ya zagaya ya dauko a wajen da aka zuba masa su dan kiwonsu da yake sha'awa bayan fitarsa ya jibgo mata gasasun kajin harma da wasu abubuwan na marmari,, ya kuma je gida wajen mahaifiyarsa ya bukaci a fada masa abinda ta fi so a rayuwa, irin annurin dake fita a fuskarsa ya saka mahaifiyarsa gagawar dago maganar dake dankare a zuciyarta, harma ta yi gagawar saka Nahidt hada mata abinda take so ta hada masa taa yi masa rakiya har wajen mota tana ta so a kan dole sai ta yi tambayar da zai fito mata fili, aman dukan tambayoyin da take masa sai dai ya saki lalausan murmushin dake sakata a mamaki ya bata takaitaciyar amsa har ya tada ya tafi gidan da fatan Allah ya sa bata farka ba

Ko da ya dawo kuwa tana barcin shine ya saka komai yadda ya dace ya rage karfin ACn sannan ya je ya dauko gashin nan ya dawo ya cire rigar dake sama ya bar ta ciki mai dogwayen hannu fara mai botira sannan ya dan bale sama saman kwaya ukun ya bar sauran

Kuma dokewa ta yi da fada fada ta ce" Nahidt in ban hannaki fira da ubana ba ki ce min ni ba yar babana bace!"

Dan murmushi ya sake yi a karro na hudu ya sake Kai abin wajen wuyanta dake ta sheki ya sake shafa shi

Raf ta yi da shi tana wartsakewa hadi da sakin kukan shagwaba, sai kuma ta yi tsittt tana wawara ido da tino cewa bafa a gida take tare da yayarta ba, hakan ya sa ta zabura da dan karfi ta mike zaune, sai dai zafin ya sakata saurin rintse ido tana furta" aushhhhh wayo Allahna nan dina......."

Da sauri ya yarda abin dawisun ya idasa hayewa saman gadon gaba daya yana fadin" Oh sorry, I'm sorry an mata , in ga wajen in ga nan din naki.......?"

Matse kafar ta yi tana zarro ido tana kallonsa hadi da turo bakinta ta sake matse kafafuwan tana fadin" Me zaka gani? Allah sawaka"

Wani murmushin ya yi yana duba agogon hannunsa ya ce" Kin ga, karfe goma ce ta gota kina ta barci, bayan na ji tsare tsarem dake gabanki na aurar da babar yaya, me zai hanna a matsayinki na matar soja ki murje ki ba marada kunya ki ci kazarki gatanan tana kallonki sannan mu shiga rubuta abinda ya dace mu yi a bikin nan? Nine fa baban amarya......" Ya karashe yana kanne mata ido daya

Hannunta ta dora a saman bakinta da mamaki ta ce" Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam, a ina aka taba yi kai mijin kanwarta kuma ka zama baban amarya? Hana dai "

Idasa zama ya yi gannin ta fara sakewa da magana ya sake rike damar ya ce" kin ga, ko dai ranki ya kiya ne da Allah ya daukaka ni? Nine baban amarya baki ga Abanki a bayana yake buya bane?"

Ai kam tino ranar da abanta ya yi wuf ya boye a bayansa ya sakata kyalkyalewa da dariyar da bata shirya bashi a kwana kusa ba, har tana dan dafe cikinta da ya tuna mata yinwa take ji matsananciyar gaske kuwa sannan ta dan girgiza yatsarta a hankali ta ce" Nahidt bata da kirki, a bainar nasi ki saka ubana gudu kuma ki ce ke ba haka kika zo yi ba?, Allah shirya min ita......."

Ita na dariyar Nahidt ne, shi kuma yama kallon fuskarta da yadda take yi din, har ta dire ayar maganarta sannan ya saki lalausan murmushi ya juya ya dauko kwanon wajen mama da kuma ledar kazar ya sake dawowa yana bubudewa a hankali yana ajiyewa a gabanta

Tukakiyar tebar da ta sha miyar markadadiyar gyada ta zubawa ido yawunta na tsinkewa, sai kuma ga kaza wace tana yin ido hudu da ita jiya ne ya fado mata a rai
Cike da kula da yannayinta da dan sigar tsokana ya ce" Kumama ai akoy ta frij ta jiya ko ita zamu ci mu adana wannan?"

Da sauri ta kalle shi tana zarro ido a zuciyarta kuwa ta shiga ayana' waye babana, ai daya ake yi da Allah in ji kuturu, ni na ci kazarka kai kuma ka kasheni? Ka je ka ci abinka Allah zai bani nima'
Chapter 117 · 0% Book details