← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 138

Sashe 107

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Father ya lumshe idannuwansa yana jin kaunar yaron a zuciyarsa da na mahaifiyarsa
A hankali ya rungume shi a jikinsa yana furta" Haka mahaifinka ya kasance mai matukar hakuri a rayuwarsa, yana iya yafe abu mafi munin da dan Adam ba zai taba tunanin ana iya hakurinsa ba.......... Son Allah ya maka albarka ya karra kiyayemin kai"

Kansa ya sada yana amsawa da kan nasa , ya kalli Mama dake murmushi ta dora hannunta saman nasa a hankali ta dan dadaba kafin ta lumshe idannuwanta tana share hawayenta itama

Murmushi ya yi bayan Dad ya sake shi yana jin zuciyarsa na samun wani gurbi na farin ciki a cikinta

A hankali ya ce" Ya dace ku shirya ku fita ku huta Dad, ya dace ku fita ku yi hutun ajiye aiki Abanah"

Dad ya ringa yar dariya yana kallonsa ya ce" Ban ki ba, aman kafin nan gaskiya sai ka tare a gidanka da iyalinka, ka ga daurin auren yayarta saura sati daya yau, ina so kafin nan ka tare a gidanka da matarka gararambar ya isheni haka"

Kansa ya sada kasa yana sake sauke ajiyar zuciya na jin abinda Dad ya fada, balema da ya ji gaba daya ana dafa maganar ta Dad wace ba yau ba yake so ya ce a yi haka din aman kuma baya fada dan kar su ce ya yi wani hali daban

Kansa a sade yana tunanin lamarin yarinyar a ransa ya ji kamilaliyar muryar Sultan dake murmushi yana kallonsa yana fadin" *TUN DAGA TAUSHE KA SAN CEWA NINE SULTAN UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB?* "

DAM DAM DAM DARAM DADARAM, DARAM DAM🥰🥰🥰🥰🥰

Kun san halina idan kuka wankeni da commentma ana iya karowa na wknd din gaskiya, 😂😂😂😂😂 da yawa fa ba wai an tsugul ba🥺🥺🥺💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 6️⃣1️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A Wajen Maman MUHAY da matarsa ne suka samu kansu da zuba masa ido da ayar tambaya a kansa

MUHYIDEEN ya yi dan murmushi yana sake sada kansa kasa sosai a nutse ya furta" Bincike na yi da magangannun Mama na sake yarda da hakan ne kuma da na bi tsohon tarihin dake birne"

A hankali Tinana ta sake kallon MUHAY, ta juya wajen Maman MUHAY mamakin wani abin kuma , kai gaba daya sai ta fara tunanin wannan rana wace irin rana ce haka mai dauke da abubuwan mamaki ne?, Wai ana so ace da su Wannan shine sarkin........?

Da sauri ta sake fuskantar mijinta da ya yi dan murmushi yana girgiza kansa a sanyaye ya ce" Allah mai iko........., Me ka fahimta a binciken naka ne ?"

Matarsa ta sake kafeshi da ido, aman gaba daya sai ya ki yarda su yi ido hudun da ita domin ya sani sarai in dai hakan ta faru to fa zai bude bakinsa ne ya yi ta bayani ba ji ba gani, yar budurwar tasa ta iya saka shi doguwar magana koda bai shirya ba

Dad ya sauke ajiyar zuciya yana fuskantar Aba ya ce" Allah ya taimakeka, aman baka gane ni ba ko?"

Aba ya yi murmushi yana kallonsa ya ce" Tunda na ganka a cikin hayacina nake son sannin ina na taba sannin mutun mai kama da kai? Aman abin ya shige min"

Yar dariya Aba ya yi ya ce" Dole ya shige maka, ga yannayin girma ya kamani, ga cenjin yannayi, aman nine fa........................"
Nan Dad ya bashi sani, ai kam ya sha mamaki matuka har ya kasa boye farin cikinsa ya juyar da kansa ya ce" Allah sarki, ka yi zama na shekara biyu zuwa uku a tare da mu kafin Aba ke shaida mana zaka tafi makarantar sojoji, na ji wahalar rabuwa da kai sosai fa, kawai dai gimbiya ce bata yarda cewar a wahalce nake da rabuwa da kai ba har take cewa wai anya ina son kani kuwa? Bayan nima burina na ga inada yan kanai a gidanmu ba wai ni daya jal uwa rai ba, du inda na motsa idannuwansu a kaina dan an ce abu daya da tsoron bari"

Yar dariya shima Dad din ya yi a sanyaye ya ce" ALLAH ya karra maka lafiya, shin me ya faru da kai ne?, Me ya faru da kai haka? Na samu kaina a cikin hali na tashin hankali da mamakin yadda du muka manta da kai da lamarinka, shin me ya faru da kai ne?"

Sai a yanzu ne ya sauke dubansa a saman fuskar matarsa
Irin yadda ya karanci abinda ke cikin zuciyarta saura kiris ya saka dariyar dake cikin zuciyarsa, watau ita dai bata kama da IBTISAM dinsa aman dabi'unsu daya, tai wata kala da ita kamar wata yar 22 yrs

A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Kamar yadda ka sani a zamantakewarka da mu a cikin baban gida shine ni daya Allah ya ba Mahaifina a duniya , watau sarki ABDULAHI dan MUTALAB, a sanina suma a wajen nasu iyayen y'aya hudu suka zo duniya, uku sunna uwa daya uba daya da mahaifina, dayan yana dan uwansu aman wanda suka hada uba daya da junna, a cikinsu daya ya koma ga mahalicinsa, saura kwara uku wa'inda biyu ke bima mahaifina , hakan ya sa a lokacin da mahaifinsa ya zo tsufa ya nada mahaifina a masarautar garinmu........"
Sasautawa ya yi yana kallonsu ya ce" na zo a tsakankannin soyaya da soyaya ne, du inda na waiga nine dai, a bayana mahaifina ya sake aure aure ko za'a dace? Amaj cikin ikon Allah ba'a samu ba, harma aka fara tunanin anya mahaifin nan nawa yana haihuwa kuwa? A wani dare da kanninsa wanda suke uwa daya uba daya ya jefe shi da wannan maganar cewa anya kuwa ni din nan nasa ne? Hankalin kowa ya tashi domin dai lamarin da mamaki sosai ga jahili mai karamin tunani, ai kam aka fatsama yin gwaje gwaje duba da ci gaba da yake samuwa na rayuwa, aka kuma tabatar cewa ni din kwonsa ne jinninsa ne........"
Ya sake fuskantarsu yana fadin" ku gane, ni ban taba gannin kiyaya daga wajen uncles dina biyu ba, hasalima rige rigen nunan soyaya ake yi a tsakaninsu , hakama matayensu da y'ayansu muna da kyakyawar fahimta a tsakaninmu, sai dai da yawancin lokuta nakan tsinci koke irin na jaje da nuni a kan wani dalili mahaifinsu ya fi son mahaifina a kansu? Sukan nuna abin bama dan yana d'ansa na farko bane, kiri kiri ya fi sonsa da su ne, sukan nuna hakan baya yi masu dadi sam, harma baban limamin masalacin masarautar ya taba yin zama da su da Sarkin garinsu watau yayansu, da mahaifansu ya yi masu nasiha mai ratsa jiki da zuciya, bayan sun bar wajen ya fuskanci iyayensu ni kuma ina zaune a saman cinyar mahaifiyar dan uwan mahaifina domin a duniya matar na shagwabani na nunan soyaya tamkar itace kakata ya yi masu nuni da tabas maganar y'ayansu gaskiya ce, a yanzu sun kai gabar tsufa ya dace tun sunna iya dajatar da abin su dakatar su kuma daidaita tsakanin, su boye soyayar yaronsu na farko a gaban sauran yayansu ko dan su sama masu zaman lafiya da jituwa a tsakaninsu, sai dai kashhhhhh , lamarin samun cenji bai samu ba, domin da tsufa ya sake kama su harma suka zamto tamkar yara ko abinci basa yarda su ci in ba shine ya basu da kansa ba, dama dama sukan yarda da uncle dina wanda suke uba daya da mahaifina wani sa'in, a haka rasuwarsu ta zo a jejere domin kuwa maman Uncle Ibrahim ta fara rasuwa, sai maman su mahaifina ta rasu, sai kuma mahaifinsu ya bi matansa............"
Ya hadiyi yawu yana kallonsu ya ce" Daga nan girman da komai ya sake hawa kan Takawa, gashi mutun mai son mutane domin ba lokaci Takawa yana amsar baki, ba bambancin kai na kasarsa ne ko bako yakan karama kowa ne shi, haka Allah ya yoshi mutun mai son mutane,............"
Chapter 107 · 0% Book details