← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 138

Sashe 77

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri NAHIDT ta kalleta a raunace ta ce" Mama haba Mama"

Mama ta yi gagawar cewa" Haba Nahidt, to ai ba sabo bane, ba laifi bane, ba haramun bane, abinda nake ji ne na fada , kuma ina mai tabatar maki tun daga cen kasan zuciyata nake jin cewa basu rasu ba"

Tsatsareta suka sake yi da ido har Shuwwa ta ji idannuwanta na zafi a hankali ta ce" Mama kema baki yarda ba ko?"

Mama ta gyada kanta tana sakin hannunta ta dafe gaban goshinta tana fadin" Kin ga, su sun rayu da ku ba tare da sun fada maku garinsu ba, Menene dalili? Kasata mai dadin riko a zuciyya?, Ko daga rami ka fito watau aka ce cen ne asalinka zaka ga ko ka tare a karshen kasashen duniya lokaci zuwa lokaci kana sako maganar garin haihuwarka kana begenta harma ka ringa fadin abubuwan da kuke da shi masu daraja a garinku, aman ace iyayenku basu da shaukin zanta haka a tare da ku kadai da Allah ya basu? Wannan shine tabatuwar labarin mahaifiyarku , na yarda cewa Hamza yyayanku ne kuma danginku ne suka wakilci daurin auren IBTISAM, sai dai labarin mahaifinku ne na kasa kamo zaren maganar, shi kuma wanene shi?, Shin shine mahaifin Hamza ko kuma shi din wani ne daban mai tatare da boyayan Al'amari?, Abinda na sani shine zuciyata ta kasa aminta cewar sun rasu, ban sansu ba, ban taba ganninsu ba, ban san me ke tafe da rayuwarsu ba, aman ina ji ban yarda da sun bar duniya ba........."

Ajiyar zuciya take ta saukewa ta dora da fadin" Ni dai mutun ce kamar kowa, ban isa na iya cire maku damuwarku ba, aman kun san me? Zamu tashi tare mu je saudiya da ku, zamu je wajen da kuka zauna da iyayenku shekaru masu yawa baya, zamu sake bincikawa sannan mu sake bibiyar hakan,
Daga nan zamu amshi dama wajen ikon kasar mu je mu duba kaburburan su, zamu roki Allah idan sunne ya saka mana salama da dangana a zukatanmu, zamu yi iya yinmu, idan har amsar ta zo daya ce cewar babu su, zamu zo mu zauna mu fahimci junna, domin a rayuwarku komai ya yi min banda al'amuranku na furucin bakinku, da wasu abubuwan, a matsayina na wace zan rikeku tamkar uwa a wajenku zan fada maku gaskiya cewar dole zamu kasance masu laushi, matan da suka amsa sunnayensu mata, a farawa daga yau, daga yanzu yanzu yanzu zan fara da baku kadan daga cikin sirikana, ba gudu ba ja da baya kuma sai kun yi domin ni mamanku ce!"

Gaba dayansu har wani tsigar jikinsu ke tashi, dama bayan Malan akoy wasu mutanen da suke rike da dabi'un mutane masu daraja na gidan duniya?,
Basu kara yarda da lamarin na gaskiya bane sai da ta gama barawa masu aikinta salahun dukan abubuwan da take so su kular mata yau sannan ta aiki Lami zuwa bakin hanya ta siyo mata manyan Po na hawa biyu, sannan ta ja su makeken dakinta mai dauke da falo da dakunna biyu a cikinsa bayan falonta ta shige daka da su ta fara ciro kayayakin da gaba dayansu sai da mamaki ya fara kashe su kafin su maida hankalinsu kanta domin wani zama da Shuwwa ta yi a kasa ta baje kafafuwa ta sakata mikewa ta sakata ssake zamanta ta halin nuna mata cewar mace yarinya ko baba, ya dace ta kiyaye zama irin na wara kafafuwa, ta iya zama na hade kafafuwanta ko a ina zata zauna, wannan din zai hanna mata saurin kamuwa da iskar gaba

Kayayakin da ta fara fitarwa sunne SASAKEN BAURE, Kananfari, Cristaux de menth, ta raba masu aiki kan daya ta dora dahuwar sasaken bauren nan, daya kuma ta zo ta daka kananfari, sannan ta ciro abin cire akaifa da kayan gyara ta baje masu a nan kafin ta koma falo dan amso Po din ( bayanin yadda ake anfani da su a page na gaba in sha Allah)

___________________________________

Daga wajen da suke tsaitsaye sunna kallon kokowar da ake dima tsakanin Lieutenant Ganaral da wannan bakon marar lafiyar abin na daga masu hankali, sunna so su shiga aman umarnin da ya bada cewar a barsu ya saka kowa ke tsaye jinninsa a akaifa yanna kallon abinda yake faruwa

Matarsa dake tsaye hannayenta rungume a kirjinta muryarta a sanyaye ta ce" Ta yaya za'a ce mijina mahaukaci ne, haukan yaushe ya same shi ne?, A da mijina ba mahaukaci bane, shi dai burinsa mu bar kasar nan, dan Allah ku cewa wancen bawan Allahn a salamemu mu bar kasar nan, mun tuba bama son zaman garin dan Allah"

Likitar da ta gama sauraronta ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Idan kuka fitan ina zaku je?, Me yasa yake maimaita kalmar a barshi ya tafi? Ya tafi ina? Ina danginku ne?, Ko baku da kowa ne?"

Zata kuma yin magana gaba dayansu suka juya a firgice jin datijon nan ya fashe da kuka, domin abu yake dauka yana makawa Ganaral dan ya barshi ya fita aman mirsisi mutumen sai ya ki koda kwakwaran motsi ne, kuka yake yi kansa da kafarsa a haukace ya ce" Wayo Allahna baka gannin abinda nake gani ne?, Bina ake yi da wuka ana huro min wuta, kasheni ake son yi, kuma shekara yau daya bayan daya shekara goma sha biyu rabona da y'ayana, sun dauko mu mun zo da mu nan dan su halaka mu? Na ce na bara masu koma me suke so , ni burina na rayu da iyalina cikin kwonciyar hankali da nutsuwar zuciya, ko na tambayi da yawa ne?, Ku barni na je ga IB.................. "

😩😭 I'm sorry I'm seek walahi 👏👏👏👏💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 43

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

"Ku barni na je wajen *IBTISAM* , ku barni na je na gani koda kabarinsu ne a nuna min nai masu adu'a, ku barni na tafi dan Allah, idan kuma sun gane inda nake ne su kasheni mana su gaji duniyar?, Dan Allah ku sasauta min haka mana??????" Ya idasa yanna dago kansa yana kallon MUHAY fa ya zuba masa ido yake ta kallonsa da son gane surutun magana marar ma'ana ne irin na wanda bashi da hankali yake yi, ko kuma wannan bawab Allahn na cikin wani yannayi ne na son a gane yarensa?

A hankali ya nemi da ya kama hannun mutumen, sai dai ya ga ya dan ja baya kadan da yannayi na ya tsorata

Dan gyaran murya ya yi yana kallonsa ya ce" Idan da hali, ka dan fada min wanenen kai mana?"

Mutumen ya ringa kallonsa da son fasare kalamansa da kuma son gane a kan wani dalili yake son hakan?

Dan gyaran muryar ya sake yi zai yi magana sai ya ga mutumen ya rike hannunsa ya rage muryarsa sosai ya ce" Kai din Soja ne ko? Ba su kake yiwa aiki ba?, Kai din mai adalci ne?"

MUHAY ya bi hannun nasa da kallo, sai ya sake kallonsa ya gyada kansa a hankali yana kallonsa ya ce" To ka taimakeni ka daukeni ni da matata ka fitar da mu daga kasar nan, a kafarmuma zamu je kasar da nake da Nutsuwa, zan yi aiki har a kaini kasar, domin a cen kadai nake da Nutsuwa, kuma a cen na baro y'ayana, ka ga masu nemana masu fada a ji ne, idan suka sameni zasu kasheni ne ni da iyalina, kar ka basu dama dan Allah, .......". Ya yi magana cikin nutsuwa sai kuma ya shiha kallon sama ya fara dan Neman fita da gudu sannan ya fara ihun irin na dazu yana ambaton ana fa son kama shi, ana binsa fa, ana tsorata shi........

Sai da ya ja numfashi kafin ya sake tare mutumen da karfi ya ringa tafia irin ta baya baya har ya karasa kusa da gadon nan ya ce" Ka kwonta a nan na je na dauko matarka sai na fida ku inda kake cewa din"

Kai ya ringa girgizawa yana fadin" Ka je da ni, gaba Daya wajen nan ya zama ramuka da duhu, ka tafi da ni ka ji?"

Ido ya sake kura masa, a hankali ya ringa kallonsa kafin ya samu kansa da fadin" Kana adu'a kuwa?"

Likitocin dake kallonsu dukansu mamaki ne ya kama su, ta yaya Ganaral zai dubi mutun a irin wannan yannayin ya masa tambaya irin wannan? Wani irin adu'a kuma? Anya mutumen nan dake haukace ya sanma meye hakan? Gashinnan karara hauka ne yake yi ba ji ba gani? Su kam ya yi ya barshi ya fito ya basu dama su mika shi wajen likitocin mahaukata a je cen a gagarkama masa allurori na mahaukata a saka shi a dogon barci a huta, wannan ai ya tafi sai hakuri kawai, aman abin mamaki sai wani sauraronsa Ganaral yake yi yana wani kokarin yi masa magana
Chapter 77 · 0% Book details