← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 138

Sashe 118

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bayane kuma sai ta kiya ta ja tebar tana sake kallon kazar a hankali ta saka cokali hadi da yin Bismillah ta dan diba ta fara kaiwa bakinta
Ai kam ta sha hadi yadda take sonta hakan ya sa ta sake kaiwa bakinta still tana hankalce da lamari na leda mai dauke da kaza, shi kuma yana kallonta kamar ya samu wata TV har sai da ta masa alamu na abin jika makoshi kafin ya mike a sanyaye ya dauko ya sake ajiye mata ya kuma zuba mata ido yana kallon dukkan motsinta har wayarta ta kuma daukan vibration din da ta yi ta yi a dazu aman bata sani ba

Shine ya dauki wayar da sauri, hakan ya sa ta zuna masa ido a lokacin da ya daga kiran ya saka a handsfree bai ce komai ba

"Wayo Allahna kanwata, fada min fada min Shuwwan Abanta shafa min an yi ko? Shikenan Shuwwan Abantama ta san abin? Fada min sumanki nawa"
Zuuuuu haka Nahidt ke maganarta tana kyakyata dariya, a lokacin da suka yi ido hudu ita da shi suka kumakin cire dubansu wajunnansu

A hankali ta fashe da kukan tabarar da ya saka shi lumshe idannuwansa ya dauki wayar ya karra a kunnensa a hankali ya ce" Bana tunanin zaki iya biyan kukanta gaskiya, sai dai ko mijin ki!" Yana gamawa ya katse kiran ya janyo matarsa jikinsa ya shiga dan rarashinta yana aukin maimaita Nahidt ce ko? Ta yi shiru zai yi tafiya mai digi tata ta kanta ya bata abinda ta nema! A haka ta lafe a jikinsa ta idasa zuba tabararta tamkar ba ita ba, tana zile zile ana tarota tamkar wata yar goye.................................

Ita kam Nahidt wayar ta cila da ihu ta ringa kwaso shokiiii tana aukin fadin ta aurar da y'arta ta kai daki, y'arta ta kai dakinta............ (🥺😔), Sai kuma ta idasa da silalewa tana zama bakin gadon a lokacin da ta tuna jibi i war haka fa ta yiwu har an daura nata auren itama da nata mijin, shin me ta tamadar masa wanda zai saka shi nishadi harma ya gasata? Ita fa tausaya masama take yi, anya malan zai iya wani katabus kuwa??????takan ji tausayinsa a zuciyarta sosai, yana cen ya kasa zaune ya kasa tsaye sai shiri yake abin har mamaki yake bata, sai dai kuma idan ta tuna Allahu gafurun rahim ne sai ta sake rike carbinta ta kuma sake kadaice kanta wa bauta masa da fatan ya sanyaya kaurin rubutun ALK'ALAMIN KADARARTA

A wannan rana Shuwwa ta ga tatali irin na soja, bama a wannan rana kadai ba har dare ya shigo idan ya matsa to fa dan ya leka masalaci ne, a nan a tare da ita ko kiransa aka yi yake amsawa, a nan a tare da ita ya baje ya ringa sakata magana da yawan nuna mata kular da ta sakata sake baje kolin tabararta, baci take yi da shagwaba son ranta kai da za'a bartama sai tace a sabata a baya Tunda dai Allah ne ya yi abinshi ta samu mai tarota ai sai yi............

_____________________________________

A gidan Malam

Karfe shida na yama

Dago kansa ya yi yace..................ALK'ALAMIN KADARATAH

Na

*Sajida*

Page

6️⃣8️⃣

Dago kansa ya yi daga ware hular da zai hadawa dinkin shadar da aka watsa masa fari kalll wanda ya sha zubi gari da yar ciki ya zunawa rigar da ta ajiye ido yana kallo sannan ya sake maida kansa dan cire abin balawa a hannun rigar da kuma safar da Matarsa uwar gidansa watau Malama ta ce ita ta fi dacewa da hawa dinkin ba tare da ya furta mata ci kanki ba

A harzuke ta sake kaiwa saman kujerar tana zama ta ce" Ka rasa wace zaka kawo ka jera ni kishi da ita Malan sai warce ba'a san asalinta ba? Y'ar ina ce ita su waye iyayenta?, Malan du irin yadda nake zuba maka karya tabaya a abincinka kana ci dan kar munafukar nan ta cin maka sai da ta cin maka ashe? Du tarin azhkar dinka da adu'o'in neman kariyar da kake yi ba dare ba rana sai da har dandi ta cin maka? Malan yau kaine kake murnar zaka je daurin aurenka da yar barikin da ta tare a gidan kanwarta har ka yi mana dinkunnan shada ka ce sai mun je? Da ni za'a tafi daurin auren yar iskar y'ar ? Malan ai ya dace ka yi min adalci ko dan zaune da nake da kai a hali na rashin jin kukan yan jarirai da yawon yan dagwai dagwai a gefena, Malan haka zaka wulakantani a anguwa a ce du abina ka kare da auren karu........"

Hular da ya dauko ce ta kubce a hannunsa ta fadi lokaci daya kuma ya sake zuba mata ido da idannuwansa da suka fara daukan launin ja dan bacin rai

A cen kasan zuciyarsa ya ringa astgfari da hailala dan samun sasaucin bacin ran dake tuko shi

A sanyaye ya karasa wajen da take zaune yana kallonta ya ce" Furera, ai ke kin san cewa an auna kwayoyin haihuwata an kuma aunawa likita dai bai ga matsalar da ta hanna ni baki ciki ba, kuma ke kin san wanene ni a saman shinfidarki wanda koda baki zauna da ni dan komai ba na gabata dan hakin da nake ba gaban jikinki kamar yadda na karanta a koyarwar adinina kadai na isa ki zauna da ni, bale ban san abinda Allah ya boye a hanna min haihuwa ba, Furera a kulun kece mai tino min cewa ban ajiye ba kuma hakan damuwa ce a tare da rayuwata, kin ga na hakura na kuma barawa Allah shi yasa nake burin ajiye wace zuciyataa ta yabama, Allah fa ya halata min shikenan ke sai ki fitineni?, Ki sani idan takamarki baki haihu ba y'arki ba zata kasance cikin jarabtar furucinki ba ki kiyaye lamarin ubangiji a kan hannin da ya yi, domin bawa baya tinkaho da halitarsa da yannayin tukin rayuwarsa har sai ya jishi a kabari, hakan na nufin ke din nan hakita ce da Alllah ke iya juyawa lokacin da ya so, kar ki manta sai idan ya so zaki shiryu idan ya ki ba zaki taba shiryuwa ba, in ba abinki ba meye riba a cikin zubar da mutunci ne? Ba zaki yi koyi da yar uwarki bane? Nan fa aka kawo mata ke ta kuma amsa ta yi min biyaya, kina tunanin akoy matar da zan yi ta tureta a kima d adaraja a cikin zuciyata ne? Furera Zuciya na son mai kyautata mata, ba kuma zan karra aure dan na tsane ku ko kun gaza min bane, zan karro ne dan halin hakan ya kama, shin ke bakya tsoron Allah ne? Kuma da kike magana a kan wai rashin asali ki wanke idannuwanki ki kuma nemi majinginin bayanki, domin ina tsoron ki tsinci keyarki a kasa a lokacin da kika ji cewar kadara ce ta rigayi fata har kika sameta a bagas kike son wulakantata, ki sani ba'a wulakanta dan Adam ko waanene domin yanzunta na iya kasancewa gabanki, ita kuma yanzunki ya dawo nata, ko a yanzu gaskiya du wanda bai yiwa NAHIDT dina adalci ya yabeta ba bana jin zamu shirya, tunda ai ta yi kokari ta zubar da komai ba tare da an saka mata wuka a wuyanta ba, sai dan mai shiryawar ya shiryeta ne, sauran kuwa zan tayata da daga hannuna na hada da kama kafa da fiyayen halita kan aya kar ta kasance a kanta , kunya da soyayar maaiki ta sa Allah ya karra yafe mata sannan ya saka Matar malan a gidan aljannah, zuwa kuwa da ki dauki shadar nan ki saka ki je da ita, ko kar ki saka ki saka wace ta maki dama so na yi mu yi ankon farin kaya tunda murna muke, ni dai na san sai kin halarci daurin aurena tare da yar uwarki, idan kuwa ba haka ba......Furera idan kuwa ba haka ba ina tsoton kanki ya kasa rike asalin wanene ni!"
Yana dasa aya ya juya ya fice a falon nasa yana ta karra tausar kansa da magangannun cewa wannan ba ranar bacin ransa bane, dan haka ya nufi bangaren da aka gama gyara komai da irin dukiyar da aka zuba mata wadda daga MUHAY ne ya bada wannan mamakin , kaya fa an zuba ko yar waye kaya kuma sun yi ko a gaban waye, shi da kansa sai da wajen ya ringa bashi sha'awa

Murmushi ya yi yana girgiza kansa da tunanin wai da gaske Shima goben nan zai kilaceta kamar yadda ya jima yana fata?, Tabas bawa kar ya cire rai da rahamar ubangijinsa duk rintsi, komai nisan dare gari zai waye ne, mai hakuri kuwa shi ke dafa dutse.

Tunda ya fice ta mike da gudu ta yi bangarenta, tana zuwa ta dauki wayarta ta kile bangaren nata ta shiga dokawa

Ta jima tana ringin ba'a daga ba hakan ya sa ta yi wurgi da wayar ta fashe da wani kukan mai tsananin gaske a bayane tana fadin" Walahi walahi walahi ba zai yiwu ba, ina ji ima gani na san kana sonta na yarda ka aurota ka kawota gidana ta yada zata idasa janye min kai daga duniyata? Malam idan taa rabani da kai na shiga ina da raina? Walahi ba zan yarda ba , uwar gidanka ai dole zuciyarta ta mace ita din kanta shekararta hamsin ne ta girmeka da shekaru bila adadin, me ya raage mata? Tama ce zata yi kishin mana ai da ta kwashi abin kunya, ni dai nice daidai da kai ba wata karuwa ba walahi, wayo Allahna ba zan iya yarda wata ta zo ta kwacen mijina da mutanen anguwata ba!"
Chapter 118 · 0% Book details