← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 138

Sashe 55

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nahidt ta ringa sauke ajiyar zuciya tana kallon yadda kiran ke ta karra shigowa, tana so ta je da gudu ta daga ko dan ta ji muryarsa sai dai ba zata daga din ba, ba zata daga ba ko daya zata yi hakurin kamar yadda Shuwwa ta ce, itama ta jure a ja abanta bale ita?

Wayar tafi da gidanka dake kuka ya saka Shuwwar mikewa da mamakin wa ke kira dakin NAHIDT ?

Dagawa taa yi ta yi shiru bata ce komai ba

Sai da ya ja numfashi kadan cen kasa ya ce" wa zai yi servg dina?"

SHUWWA ta zarro ido tana ciro abin a kunnenta, sai kuma ta maida da sauri jin kamar ya sake daukan wata maganar
A hade ya kuma fadin" Nd Nahidht ta fito fr eat"

Daga haka ya katse kiran da ya sa Shuwwa yin mutuwar tsaye

Kai ta girgiza ta ce" Na rantse tarko ne, kai, walahi tarko ne babu inda zamu tafi"

Nahidt ta tsatsareta da ido tanai maya kallon tuhuma ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣9️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

*Alhmdulilah mun watse taro lafiya, na gode sosai da adu'o'inku*

Da kallon tuhuma ta ce" Me kikai masa ne Shuwwa?"

Ido ta dan zarro ta ce" Me kuwa zan yi masa aunty?, Kin ga ni babu abinda na yi masa kawai dai na san shi din mugu ne kuma na san idan muka fita falon cen babu abinda ba zai faru da mu ba"

Dan tsai ta yi tana tunani da yannayin SHUWWA kafin ta tabe baki ta ce" Mu je Kawai, tawakaltu Allalah, SHUWWA ke din cema yar iska, babu yadda zan maki magana ki dauka tashi tsaye, kin gama raina min wayau, ki Duba ki ga uwar rigar da kika saka a cikin gidanki da kananun shekarunki, a aurenki da wannan tsabgegen zauraryin da kin wan mata babu kalar da bata kawo masa wawa, maimakun ki yi anfani da damarki ki ringa matsewa cikin kannanun kaya kina juya mutanen da Allah ne ya baki ba uban wani ba, ki kwato shi a lokacin da shi din kansa bai sani ba, aa ke ga alamiya dan ubanki kina yawo da riga uwa zaki je tsome, kin luluba dan kwali ke ga ustaziya, bari ki ji a barkar kwato sarautar miji idan kikai lako lako ba rantse maki tsaf zaki jawa kanki asara da tashin hankali dan kuwa kina ji kina gani wata zata iya bada kaya sai dai ki ji ana tarihinki! "

SHUWWA ta tafa hannayenta tana kallon Nahidht ta ce" Yanzu wannan shigar tawa menene laifinta?, Wai ke a tunaninki wancen mutumen wani shigar kananun kaya zasu kaishi ne?"

Nahidt ta ce" Dan ubanki waliyi ne shi da zai ga haja ya ki rayawa?"

SHUWWA ta tabe bakinta a kasan zuciyarta tana ayana' dadin abin ba so nake ya taya dinba ai, wannan ai bama saana bane sam!'
A bayane kuwa ta girgiza kanta tana neman zama saman kujera hakan ya sa Nahidht ta damko hannunta tana fadin" ke dadina da ke wawuya ce ke, miji zaki ce zaki ki zuwa bayan ya yi kiranki? Ai zuwa ake komai ta fanjama fanjam,"

Shuwwar ta ce" Nahidt ki dakata, ki fa ankare da lamarin mutumen nan fa, ki fa kiyaye fa Nahidt du inda kike tunani ya zarce nan fa"

Nahidt ta dan juyo tana kallonta ta ce" To ko dai tsoronsa kike ji ne?"

Da sauri ta girgiza kanta tana fadin" Allah kiyaye na ji tsoronsa kawai bana son wulakanci irin na sojoji ne!"

Nahidt ta ki ta tsaya ta jata suka fice gaba dayansu suka nufo falon tana ayana' Shuwwa baki da mutunci, tunda aka kamo mu aka watsomu nan kika tsani soja, bayan ba sojaa bane ya kamo mu kin hade dukan mai iko kin masa fenti, dan an kamo ki baki ga kabarin su Mama ba? Sun rasu Shuwwa ya dace ki yi hakuri'

Kasancewar a zaune yake ya ba bangaren dakin na Nahidt baya hakan ya sa bai ga fitowarsu ba, domin keyarsa ke kallonsu sai bakon dake zaune ne sukai ido hudu da junna

Ido SHUWWAR ta zarro kasa kasa ta ce" Hamza?"

Nahidt ta ce" Kai, to me ya zo yi? Yaya aka yi aka barshi shigowa warhaka?"

Shuwwa ta ce" Na fada maki tarko ne zai ci ubanmu ne a gaban yayanmu"

Nahidt ta dan sakarwa hamza murmushin yake itama kasa kasa sosai ta ce"Na ce me kikai masa kin ce ke ba komai ba, to mu je mu gani yadda Allah ya yi da mu"

Hamza ya yi dan murmushi yana kallonsu a sanyaye ya ce" Ku karaso mana"

Sake kallon junna suka yi sannan suka shiga karasowar kowace na saka abinda take sakawa a cen kasan zuciyarta

Zama sukai suka saka shi a tsakiya har ya zamto kafafuwansa na gogar nasu domin a saman kujera daya ne suka zauna gaba dayansu

Gaishe da MUHYIDEEN Nahidt ta fara yi sannan ta juya itama wajen Hamza tana gaishe shi kamar yadda Shuwwa ke gaishe shi bataiwa MUHAY magana ba

Dan murmushi ya yi a sanyaye bai amsa gaisuwar tasu ba sai ya shiga tambayarsu da damuwar dake saman fuskarsa ya ce" Shin baku yi farin cikin samuna a matsayin yayanku da muka fito ciki daya bane ko ba zaku yi zumunci da shege bane?"

Da dan karfi Nahidt ta ce" Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam mun shiga uku"

SHUWWAR ta kalle shi a sanyaye ta ce" AA Hamza me yasa zaka ce haka dan Allah, wata irin magana ce zaka ke fadi kai tsaye a gaban kowama dan Allah, me yasa kake son neman wulakantar da mu baki daya ne Hamza ?"

Hamsa ya yi dan murmushi yana kallonta ya ce" Na fa kula da ku fa Shuwwa, asalima irin farin cikin da na yi jin nima ashe ina da kanai ashe soyayar da na ji farat daya inai maku dan ku din jinina ne ku du ban ganta a saman fuskokinku ba, Sannan tunda muka tafi gida da NAHIDT gatanan bata da sakewa da ni irin na da, a da takan zauna mu yi ta hira muna ta shan ihunmu da dariyarmu aman a yanzu ban san me yasa du ta cenza ta fi kaunar zama a daki, karshema ta yi tafiyarta ta bar mana gidan wanda hakan ba iya ni ba, Fauziya kanta sai kuka take yi na hakan ta damu ta kuma shiga cikin tsoron dalilin da ya sa kuka aikata haka?, Dan Allah bakwa jin dadi da farin cikin samun dan uwa a kusa da ku kin ga fa ko sunnana gatsal kuke kamawa dan Allah bakwa sona ne ku?"

MUHYIDEEN Bakinsa ya tabe yana zaunen dai yana sauraronsu aman kuma ba kallonsu yake yi ba

Wayar da Dad dinsa ya kiresa a kanta ya shaida masa yayan matarsa na waje dan Allah a sanyo shi hankalinsa ne ya tashi bai ga Nahidt ba yana son ganninta a kan dole ya sauko ya bada dama aka sanyo shi ce ta dauki tsuwa hakan ya sa suka kai dubansu gaba dayansu kan wayar ciki harda shi,

Hannunsa ya saka ya dauka ya daga kiran yana karawa a kunnensa hakan ya ba SHUWWA damar rage sautin muryarta sosai tana ruruko idannuwanta domin so take su dauki maganarta da mahinmanci kasa kasa sosai ta ce" Yayanmu, kar ka yi maganar ahalinmu a gaban bako mana, gaba daya fa ba abinda kake tunani bane ba, ita dama tana son zuwa wajena shine ta zo"

Hamzan shima ya rage muryarsa sosai ya ce" Mijin naki ne bakon?, Kuma tana son zuwa ba zata bari mu shirya mu zo tare ba shine zata zo gidanki da kayanta na sakawa? Ni fa aikin me nake yi ne da ba zan rike kanwata daya kwal ta gabana ba?"

NAHIDT ta ce" Du fa ba inda ka nufa ba na nufa big brother, kai ka san muna cikin farin cikin gannin ashe muna da kai a duniya bayan mun fitar da ran cewa muna da wasu a duniya harma muka ga danginmu, abin ne ya zo mana a baibai shi yasa muke ta shawarar yadda zamu dauke shi idan ka yi la'akari da mun taso ne mu mu biyu,, daga baya muka hadu da Fauziya sai baban Shuwwa shikenan ne, ka ga dole komai zai zo mana a baibai"

SHUWWA ta dan dago daga kallon Hamza da take ta sauke a kan fuskar MUHYIDEEN a kasan zuciyarta tana cike da mamakinsu da zasu saki baki sunna son tona asirinsu a gaban wannan mutumen mai yannayi irin na wulakanci salon gobe ya wulakantasu a banza a wofi
Idannuwansu da suka sarke da junna ne ya sakata sake kallon fuskarsa sakamakon abu biyu
Na farko fahimtar da ta yi magana ne yake yi a wayar ashe? Sai na biyu ankara da ta yi kamar ya harareta
Chapter 55 · 0% Book details