← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 138

Sashe 2

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wace aka yi kira da SHUWAR din ce ta dan miko hannunta idannuwanta a rintse muryarta na rawa ta ce" NAHIDT, kunshin nan ki goge min shi kin ji? Na tsane shi. Bana son ganninsa a hannuna........"

Da sauri ta zauna tana birkito kanwar tata jikinta ta ce" To yanzu kuwa, SHUWAR yanzu kuwa, Fauzy je ciki hado min abubuwan da zan mata anfani da su na wanke mata kunshin kin ji?"

Da sauri Fauzyn ta yi ciki dan daukowar ita kuma SHUWAR din kanta a saman kirjinta muryarta cen ciki ta sake bude bakinta ta ce" Sunna da gaskiya da suka ce ba zan ce kadara ce ta saka ki haka ba, NAHIDT son rai ya shiga cikin lamarin, aman mazan kansu kin san sun zama yan iska ko? Me na yi zasu ringa sako ni bayan kafin su samu soyayata sai sun yi kamar zasu yi hauka?"

Nahidt a sanyaye ta ce" SHUWAR dukankima shekarunki nawa? Just 22 fa, SHUWAR sai kina cewa mace tsufa take ke aure kike so, SHUWAR na san aure kike so aman kina da damar jan ko dan uban wanene a kasa yadda kike so, SHUWAR ki bari mai mutuncin da ya san mutunci dan mutuci mai daraja ya bayanar maki a lokacin da ya dace, ki daina gagawar nan, SHUWAR ke matar sarki ce ko gwamna, SHUWAR ki daina kukan haka a kan d'a namiji , ya jima bai sake ki ba wani zai kama ki ya so ki ai!"

Kanta ta dago tana kallon kyakyawar fuskar yayar tata mai shekara talatin da daya a duniya , aman kula da kai ya saka freshhh take da ita, sai dai duda wannan kamaninta ba nutsatsen kamar mai Nutsuwa bane sakamakon kauce hanyar da ta dauka sana'a

A hankali ta ce" Kina nufin na ci gaba da cin haram?, Na ci gaba da gannin kin shigo a talatainin dare kin shiga kin wanke najasa kin zo kin kwonta a kusa da ni? Kina nufin haka zamu ci gaba da rayuwa da wanda ya isa da wanda bai isa ba ya dubeni ya zagar min ke dan kin wulakantar da kanki? Wai Kinma san me Elhaj mai shinkafa ya ce da ke ne? Dalilin zagin da ya maki na rantse da Allah gobe sai na gigita rayuwarsa fiye da tunaninsa, haka kike so kina amso ni a police station kamar barauniya? ......"
Dubanta ta maida kan Fauziya da ta gama zuba Dop a cikin ruwan dumin da ta tafasa ta ce" Fauziya, kin san da sai na halaka farin cikin Mai shinkafa?, mai shinkafa ya taka wuta bai sani ba, da ace hakurin da na bashi kar ya yanka min tikitin zawarci a karro na uku ya saurareni ne da na sasauta masa, aman walahi a yanzun ko sai kun yi belina, ina ji a jikina zan janyo maku magana ne"

Hankali a tashe Fauziya ta ce" Kin ga ki rufa mana asiri, baki ji ba za'a yi taron nan na shugaban kasa? Kin san waye ya sauka a garin nan? Ki bari bayan taron nan sai mu je mu samu mai shinkafa mu koya masa hankali, aman a yanzu ki rufa mana asiri da bawan Allahn nan, cewa aka yi mahaukaci ne, kurmane, makaho ne a gaban wanda bashi da gaskiya, ki yi hakuri kar ki dago *ALKALAMIN KADARARSA TA BI TA SAMAN KANKI* sannan ta biyo ta kanmu SHUWAR!"

SHUWAR ta lumshe idannuwanta masu shige da na mashayiya luuuuuuuuuuuuu tana saka kafafuwanta da hannayenta a cikin ruwan yayarta na anfani da lemun tsami ta fara darje mata kunshin ta ce" Baki sani bane, kin ga tun daga ranar da wannan basamuden ya damki kugun auntyna ya riketa dam ya jamu ya maka mu a gidan da aka kwaso mu ba ko sisi aka zubo mu kasar nan? Na tsani du wani halitar da zai amsa kiran mai anfani da kaki, bana jin tsoron mai rigar soja, bana jin shayin kai masa wargi, ko uban waye shi ni SHUWAR zan iya dubansa ido cikin ido na ce da shi Jaki , idan shi dan iska ne dan Allah ya yi gigin taba ni, ni kuma sai na karar da jikokinsa a wahala sai dai idan kasa ta lulube idannuwana kafin mu kai lokacin!"

"Ikon Allah" Fauziya ta fada a hankali ta ci gaba itama da wanke mata hannun a kasan zuciyarta tana ayana 'Allah ka kashe rigimar nan tata da wuri ya Allah domin idan ranta ya bace ashar kam sai dai idan babu shi a duniya ne'

Itama yayarta faman goge mata take yi duda ta san abu ne mai wahala kunshin nan ya fita tasss duba da irin yadda suka bata lokaci da kayan aiki dan yinsa , su biyu ne sukai mata shi hadin kunshin da ake yiwa larabawa ne wanda suka koyo suka iya abinsu tun a cen, shine suke yiwa kansu bale wannan rana baba ta kanwar tasu sai sukai mata na gani na fada, gashi ta ce a wanke

Cen kamar kamun hauka ta sake barkewa da kukan da sai da NAHIDT ta zabura tana kallonta
💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Lebenta ta cije tana ayana' Sai na wulakanta farin cikinka mai shinkafa, Kukan nan da ka sakata sai na saka ka shi da idannuwanka!' ta idasa ayannawar tana kallon SHUWWAR dake kukanta kashirban

Da kyar suka iya rarrage duhun kunshin, sai dai hakan da sukai masa sai ya kasance kunshin ya fi da kyau, domin a yanzu ne kunshin ya sake daukan kalar fatarta ya wani irin haskawa
A haka dai suka lalabata ta shige dakinta ta nufi bayi dan yin wanka sannan suka koma falo sunna maida numfashi hadi da tatare kayayyakin da suka yi anfani da su

Sunna jiyo motsinta, har ta daina daga bisani kuma sai suka jiyo muryarta cen wajen minti talatin bayan shigarta ta saka karatu da karfinta wanda ya saka yayarta sauke ajiyar zuciya tana mikewa da wayarta ta nufi dakinta ta rufo itama ta nemi salayarta dan ta gabatar da sallar isha'i domin bata yi ba sakamakon rikicin da suka kwasa da kanwar tata

Fauziya kadai aka bari a falon wace ta jima zaune tana sauraron zazakar muryar Shuwwar dake fitowa da kukan dake cikin zuciyarta har ta yi kasa kasa kafin take yin diffff alamun barci ya dauketa hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta je ta rurufo kofofin gidan ta dawo falon saman kujera ta kwonta dan ta san yau dai ba damar zuwa harkoki domin idan suka yarda suka fita yau zasu siyawa kansu balaki ne a wajen ita kanwar tasu

_______________________________

Wayar da ya sake bugawa a karro na uku ya dan saurara dan yana saka ran ko yaya ne yanzun zai daga wayar domin yanzu karfe tara na safe kennan duda ya san waye shi , me ya je yi, wanda ya tabata a irin wannan lokacin da wahala matuka ya kula harkar waya

Har ya fida rai da samun amsarsa sai ya ji an daga wayar sannan shiru ya biyo baya sai alamun shasheka dake dan tashi a cikin wayar wada ke nuni da alamun yana gudu ne ko kuma yana dakin Gyms ne

A nutse ya yi salama da nasa kalar ikon shima sannan ya saurara

Sai da ya yi yar gyaran murya kafin ya amsa salamar da murya mai shige da ta zaki, domin amon muryar ba laushi ba tausasawa a hade kuma take kamar yadda mai ita fuskarsa ke hade

A nutse ya ce" Why zaka salami yarinyar nan ne? Me hakan yake nufi ne Lieutenant Ganaral?!"
Chapter 2 · 0% Book details