Sashe 26
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daga wannan ranar suka fara shinfida Rayuwa mai tafe da daraja da mutunci
Rayuwa ce da basa fita yawo dan neman na cin abincinsu, rayuwa ce da suke zaune a daki iya tsayin yawonsu falonsu ne sai ko idan zasu rufe gidan
Hakan ya sa suka ringa taya SHUWWAR daukan azumin da take yi wanda daga bakin lokacin da ta fara yinsa ta fara fuskantar wata irin nutsuwar zuciyarta
Lafiyar jikinta ta karru fiye da da, uwa uba da zarar ta sha ruwa ta yi salolinta sai ta kawo kayan gyaran jikinsu ra hada ta hau Dukhane hankali kwonce ta dauki lokaci mai tsayi a sama tana shan hayaki har sai fatarta ta yi jajajir sannan ta sauka ta dora da damamen kurkum da madarar kauri a jikinta ta murje sosai har sai ya kamata sosai sannan ta sha kadadar madara mai sanyi karara ta haye gadonta ta luluba da bargonta , garin Allah na wayewa kuwa take dora zaman turaran wuta, wannan kuwa sabonsu ne su dukansu ukun kowace da kujerarta da turaran tsugunonsu da na jiki
Watau sabon da suka yi tun a saudiya na gyaran jiki da iyayensu ke yiwa larabawa da yan matansu na cen idan aure ne ko biki ne , kai kulun dai cikin gyara ya kasance suma abin baya basu wahala, ba zai yiwu su yi sati basu dora gyara ba, jikinsu har tambayarsu yake yi
Sai suka karra samun sirikan gyaran na mamaki wanda ke karra fitar da darajar fatarsu
A Yanzu kuma da suke zaman gida ba dare ba rana, abin sai ya zama shine kadai abinda ke debe masu kewa bayan TV
Gefe daya kuwa Hamza ba wai kwata kwata bane basu da labarinsa
Ta cikin waya ya zame masu karfen kafa
Ita da kanta Shuwwar dake mamakin sun yi saurin sabo da shi sai gata ta saba da shi din
A waya suke bata lokaci mai tsayin gaske sunna hira, kuma hirar kowa da kowa ne
Ta wayar ya nemi sannin su din su wanene?
A lokacin da NAHIDT ta shiga bashi labari a lojacin nan Shuwwar ta mike ta nufi ta kwonta
A hankali ta lumshe idannuwanta tana jin yadda zuciyarta ke dan bugawa
Labarinsu?
Labarinsu ai takaitace ne, domin su da kansu basu san menene asalin labarin iyayensu ba, basu san su din yan wata kada bace, su dai sun samu yaren hausa a bakinsu sai larabci sai ko turanci da suke ji
An haifi su a Riyad ne su dukansu , daga baya iyayensu suka dawo maka da zama
Abinda suka sani da rayuwarsu shine mahaifiyarsu dai farar mace ce kamar zabaya, akan kireta da buzuwa sunna ne na kiranye da abokanan aikinta ke kiranta da shi, sai mahaifinsu shi kam ba fari bane ko kadan, aman mutun ne mai kyan gaske domin a kamani ita SHUWWAR ta dauko kamanin mahaifinta ne, ita kuma NAHIDT ta dauko na mahaifiyarsu, aman gaba dayansu farin mamansu ne suka dauka da gashinta da kirarta
Labarinsu bashi da tsayin da zasu ce ga asalinsu har iyayensu suka barsu da sunnan sun tafi arfa a cen aka dawo masu da maganar sun rasu
Basu ga gawarwakinsu ba, basu ga kabarinsu ba, a haka suka dangana daa son ganninsu domin sun je sun kuma zuwa basu samu gannin mamatan ba bale su ga gawarwakin iyayensu, gashi a lokacin sunna cike da tsoron kar a kama su a kaisu wata kasar daban
A haka suka ci gaba da nema da aikatau dan su ci da bakin su, har ranar da la'ananen nan ya kama auntynta aka kaisu gidan da ake dawo da jama'a kasashe daban daban aka diro su hausa
Ajiyar zuciya ta sauke dan ta san shikenan ko mai yannayin rayuwa irin ta Hamza me zai ci da mai irin rayuwarsu?, Ita kam yanzu a irgenta satinta uku kafarta bata leka waje ba, da zarar ta samu ta idasa sakewa sosai zata fara fita ne dan ta samu aikin yi ko yayane ta ringa yi , zai kore mata kewa
____________________________________
Sati shida kennan da rabuwar auren Shuwwar
A tausashe ya dora da fadin" Ban sani ba, malan ban san ko matsalar halin da ya fada maka kai tsaye bane ya saka ka yi masa iyaka da yarinyar wajenka?, Ka ga wannan da kake ganni yaya yake a wajen mahaifiyarsa , yakan zo lokaci zuwa lokaci, shima a yanzun wani ne a kasar nan, aman Hamza ya ki ya dube shi ya ki ya yafe masa, a yanzu da ya zo na ce bari na janyo shi mu zo mu sameka tare domin zan fi jin kwarin gwuiwa, kuma mai yiwuwa idan muka zo taren koda ka yi niyar hanna mana ne kana iya bamu, Hamza yarona ne, aman ka ga yayan mahaifiyarsa nan, bamu da labarin mahaifiyar tasa dai , an yi neman an hakura an barawa Allah komai"
Malan ya sake kurawa fuskar Datijon dake zaune cikin shiga ta alfarma ido
Da sauri ya cire idannuwansa yana mamakin kamanin nan, datijo ne, ga shekaru ga komai, aman cikin ikon Allah kamanin a bayanr suke ba a boye ba
Wata ajiyar zuciyar ya sauke yana fadin" Elhaji, ko daya, ba wannan dalilin ya saka na dakatar da shi ba, ina so ne mu bi komai a hankali, bana so abinda ya ringa faruwa ya sake faruwa da yarinyar nan duda ban isa na hanna kadararta wadda Allah ya kadaro mata ba, aman ina iya yina, so nake ko yayane abin ya zo mana da dalili, ba wai ace a musulman duniya an rasa wanda zai iya yin jihadi ba, wannan shine kawai dalilina, yanzu kuma da ka zo da kanka na yarda cewa da gaske yake, harma zan iya bashi aurenta in sha Allah"
Farin ciko ne karara ya bayana a fuskokinsu, datijon nan ya budi bakinsa da hausarsa mai hade da yare irin na buzun usul ya ce" Allah ya saka da alkhairi Malan, mun gode mun gode sosai, dan Allah a fada masa ya yafe mana, a lokacin da muka kyamaci mahaifiyarsa har muka koreta a gida dan abin ne ya zo mana a birkice, sai muka guji kunyar duniya muka yafawa kanmu ta lahira domin mafanar da nake yi maka mahaifinku shine sarkin garin Tanus, a yanzu haka yayanmu ne ke sarauta a garin, mun tafka kuskure, mu dukanmu muna dana sani, sai dai dama an ce dana sani keya ce, gashi yanzun sai shi kadai muka sani bamu san ina uwar take ba, bamu san tana raye ba ko a mace ba, saudiyar du shigarmu sai mun sake kokarin nemanta a tashihin da yan kasar nan ke rayuwa, aman kulun amsar daya ce basu san *TINANA* ba, Malan idan har ba takura dan Allah a taimaka mana daurin auren nan a yi shi kwana kusa, kar a ja mana malan, shi ba yaro bane karami, itama ba aurenta bane na farko, kar a ce mana ba'a shirya ba domin mu dama bama auren mace ta kuma tare da mana da komai, ko karan tsintsiya bama yarda mace ta zo mana da shi, namiji shi ya dace ya yiwa mace komai ko a adinace, ba adini bane ya zo mana cewar a yiwa mace gado da sauransu, zamu yi komanmu, mu dai macen muke so dan mun san darajarta zamu amsheta da hannu bibiyu in sha Allah"
Wani irin farin ciki ke ziyartar zuciyar Malan, hamdallah yake yi a cen kasan zuciyarsa yana hasaso irin farin cikin da zasu yi su dukansu idan suka ji wannan dadadan labarin
Tabas NAHIDT ta yi gaskiya a kaf manema auren Shuwwar babu wa'inda suka zo da niyar taa alkhairi irin wa'innan ba
Hakan ya sa shima ya ari bakin yan matan ya ci masu albasa a nutse ya ce" To ai shikenan Elhaj, kamar wani lokaci kuke so? Wata daya ya isa?"
Aban Hamza ya sake Nutsuwa yana murmushi ya ce" Ai shi baban nasa ne yake da tafia malan, bama gagawa aman da mun samu nan da sati biyu, da mun ce Alhmdulilah, ka ga babansa ba yau ba yake shirye shiryen auren dan nan nasa na tabata kofar gidanka sai ta yi kamar zata fashe dan jama'a"
Farin ciki ya sake lulube zuciyar Malan, a sanyaye ya ce" Alhmdulilah, in sha Allah ya yi, zamu fara shiri tun daga yau bi izinillah".............
Da wannan suma rabu da junna, malan kam bai wani yi dogon zama ba ya samu ya je gidansu da karfinsa da kuma rigima daidai da du wanda zai zo masa da tangarda a kan maganar
Sosai ya sake samun Nutsuwa da urin halin da ya same su, kunshi suke yi, wace ke yanyara masu kunshin kuwa Shuwwar ce, Shuwwar ta yi kyau har ta gaji abinta , ga kunshinta dan dasss a kafafuwanta
A nutse ya sanar masu abinda ya yanke da Shuwwar ya dora da fadin" na fi so ku yi taron bikin a gidana, idan har hakan ba takura bane a gareku"
Zuciyarta tsintsinkewa take yi tana kallonsa, a hankali ta ce" Aba"
Kansa ya dago domin du bayanin da yake yi ba wai kallonsu yake yi, dan kwaurin Nahidt a fili kuma ba abinda ya dameta
A hankali SHUWWAR ta ce" yadda kake kokari a kanmu, Aba yadda kake nuna mana kauna, yadda bakaa kyamatarmu ABA, Allah ya rufa maka asiri duniya da kiyama......" A hankali ta dora kanta a gefen kafadar Nahidt tana hadiye hawayenta
Fauziya da gaba daya jikinta ya mace mata sosai kanta aa kasa itama adu'a take yi tun karfinta tana korar abinda ke a cikin zuciyarta
A sanyaye ya yi Murmushi yana fadin" In sha Allah, da zarar ranar ta gabato zaku koma ku yi bikin a cen, zan koma masalaci"
Daga haka ya mike ya juya da niyar tafia ya ji muryar NAHIDT a sanyaye ta furta" Malan "
Dakatawa ya yi yana ayana' Na san ai sai mun raba hali '
Yaja juyowa ya ga hawaye ne shar shar shar a kan kumatunta tana kallonsa