Sashe 126
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda ta furta wannan kalmar Nahidht ta rintse Idannuwanta ta kuma sada kanta kasa, ta fa san ba kowa zai zamto ya iya yi mata adalci ba, bayan wannan ai bata nemi a yi mata adalci ba, sai dai bata san mijin tace ta aura ba sai yanzu, tun dazu yarinyar nan ke zuba rashin kunya aman yana zaune yana kallonta bai iya ce mata komai ba, wai dama yadda yake sanyi sanyin nan a komaima haka yake ne? Ta tabata ido zai zubawa yarinyar ta wulakantata dan ga dukkan alamu tsorontama yake, sai dia bata tunanin zata hadiye zagi daga kowace y'a a duniyarnan, tunda laifin ba ita ta yiwa ba ubangijinta ta yiwa, kuma a lokacin da take aikata laifin bata miko mata hannu da tatausan magana da nasiha dan ta kubutar da ita daga fadawa halaka ba, lalalalaalalala saima sake zaginta da take yi a kwararo kwararo, idan a da ita din ba tsarar yinta bace duba da babu abinda ya hada su tana gannin a yanzu tsarar yinta ce, dan haka ta sake damke idannuwanta dan bata so ta yadda hali daga zuwanta gidan a yau yau
Sshi kuwa tunda ta furta kalmar a hangame take din nan sai ya samu kansa da jin zufa na Neman karyo masa du kuwa da irin sanyin ACn falon
A hankali ya lalubo hannun uwar gidansa ya rike gam da mugun karfin da ya sakata zuba masa ido cike da tausayawa
Takan auna abin a zuciyarta ne, yanzu ace irin matsanancin son da take masa ta tsinci ya yi taraya da wata a titi wace ba halalinsa ba? Lalle bata san ke zata iya aikatawa ba, domin tana tsoron idan ta shanye na halalinsa ta kasa shanye na wace ba halalinsa ba, ita kuma shaida ce so halita ne Allah ya darsa na wannan baiwar Allah a zuciyar uban gidanta
Furera bata mike a wajen ba sai da ta idasa rufe maganarta ta hanyar fadin" Nadaden nadin da ya sameta a yau ba shi ne zai saka min tsoronta ba, Malan dama ace yarinya danya sharat ka dauko sai mu saka rai da gani yan dagwai dagwai mai yiwu kafin mu mace, aman tsabar ka kauce sai ka kwaso wace ta zubar da kwayakwayen a titi, menene ya rudeka ne haka? Inaga kangarewar ce da kuma jar fatar....., Sai a yi mu gani idan tusa zata hura wuta!"
Da kallo Malama ta rakata kafin ta juyo hankalinta tashe ta shiga fadin" Dan Allah ka yi hakuri, Dan Allah ki yi hakuri kema, kar hakan ya hadasa maku da bacin rai komai kankantarsa, ku yi mata uzuri kun san kowani bawa da irin yadda yake kore bacin ransa, aman dan Allah ina rokar sasauci a fahimtarku wa kalamanta......."
A nutse Nahidt ta sake dago idannuwanta ta zuba su a saman fuskarta, a hankali ta sake karantar wannan mata mai dumbin abin mamaki, a tsanake ta tsintsinci halaya cikin nata na alkhairi a lokacin da ta fahimci wannan mata ba son mijinta bane bata yi, ba kuma rashin sannin ciwon kai bane, haka Kuma ba aiki irin na kissa bane, tashin hankakinta tashin hankakin mijinta, nutsuwarta kuwa dariyarsa
A yanzu a gabanta da yake lamari irin na murmushi ta fi kowa farin ciki, a yanzu kuma da wani al'amari mai kama da bacin rai ya shinfidu a saman fuskarsa sai ta ga nata tashin hankalin ya fi nashi bayannuwa, har sai da ya sakar mata Murmushin yake sannan ta iya mikewa ta yi masu salama da fatan alkhairi ta fice a falon
Shiru ne wajen ya dauka na lokaci kamar minti goma a kalla, domin har sia da ta cire ran ko zai dago ya dubeta, sai kuma gashi ya dago ya zuba idannuwansa a cikin nata
Da sauri ta cire dubanta a nasa tana harhade girarta hadi da sake tunanin ya aurota be dama dan da zarar an fadi magana kwatankwacin wannan ya birkice? Aman ai ya san me ya dauko ko?
Gannin zaman yana neman zama na wulakanci sai kawai ta mike tana gyaraa alkyabarta da tunanin kar dai ta Shuwwa ce zata kasance da ita? Kai da ta shiga ukunta a duniyar nan baki daya
Wajen da yake ta dan matso kadan tana kallonsa ta mika hannunta tana fadin" A fahimtata nan bangarenka ne Aban Shuwwa, bani ky din nawa bangaren na je na huta bakina ya fara tsami!"
Hannun da ta miko mai dauke da kunshi ya zubawa ido, kafin ya sake lumshe idoo yana son ta sake bude baki ta kuma yi masa magana dan ya sake jin maganar da muryar tarrr ba tare da korar shedan da yiwa kansa iyaka da fadin cewa ya fa kula ba muharamarsa bace
Baki ta kuma turowa ta kama tsatsonta tana fadin" Ga dukkan alamu zan fara fuskantar cenzawar namijin tun yanzu? Aban SHUWWA magana nake mak.........Wayo Abanahhhhhhhhhh" ta fada da dan karfi sanadiyar hannunta da ya damka ya wartota ta fado saman jikinsa
A tsorace ta dago ta zubawa fuskarsa ido da idannuwansa, shima hakan ya yi yana kallonta yana ayanna abubuwa kamar yaka......' zan so na zarce duk wani marar azancin da ya so birge ki, zan so a yau na yi dan ina ra'ayin hakan, zan so idan Allah ya bani ikon yin ki amshe ni ki kuma bani dama, zan so na kasance mai saka fuskar nan farin ciki ba mai sakata bacin rai ba, ni na ji na gani na kuma dauka da farko na so yi dan na ceceki ne na rabaki da rayuwar bariki, a yanzun kuma zan iya cewa kece bugun zuciyatahhhhhhhhhhhhhhhh'
Ita kuma a yau da ta kasance a haka a jikinsa sai ta ji jikinta ya karra mutuwa, gannin ya kira mata ido bai ce komai ba ya sakata mayar da kan nata saman jikin nasa a hankali ta barke da kukan da ya saka shi dawowa hayacinsa a rikice yana dagota gaba dayanta
Har muryarsa na rawa ya ce" Nahidh kuka? Kuka kuma? Ya salam menene?"
Da muryar kuka ta mike tana janye jikinta ta dube shi da dan harare sannan ta harare shin gaba daya tana fadin" Aban shuwwa har ka shiga halin dana sani da ka aureni ko? Ka shiga halin dana sani ko? To ai sai ka sauni tunda ni dai ba zan zauna na ga wulakanci daga gareka ba walahi, ka sauni ai ba laifi bane malamaima sukan zama azalumai ehe!"
Ido ya kikifta kafin ya saki murmushi yana girgiza kansa a sanyaye ya ce" Shin kina da alwallah?"
Dan kure shi ta yi da ido kafin ta girgiza kanta tana cirw kai hadi ta turo baki
Wani murmushin ya sake yi ya ce" Kin ga mu je ciki ki yi alwallah mana mu yi nafila ta godiyar Allah sau mu yi barci mu hutar da gajiyar nan da muke tare da ita, kin san gajiya bata da dadi sam ko?"
Kasa kasa aka sake kallonsa kafin ta yi wajen da ya nuna matan
Da ta shiga bayi dan yin alwallah hadi da wanka sai da ta kunna ruwa ya shiga dukan jikinta ta fashe da kuka tana rike kanta sosai, kukan wannan lokacin da ta san zai zo mata, kukan takaicin kanta da kanta, kukan ta cuci rayuwarta sannan ta kuma maimaitawa kanta maganar da mahaifiyarta ta fada mata cewa aikin gama ya gama, idan har da gaske Muhamad din ya yi domin Allah zai kamanta adalci a gareta, itama ta yiwa kanta adalci kar ta tsangwami kanta, dan haka ta wanke fuskarta ta yi wanka hadi da saka doguwar rigar da ta cire a yar akwatin da aka zo mata da su bangaren nasa da hijab dinta ta saka tun a bayin
Tana fitowa a tsaye ta gansa saman darduma, dan haka ta karasa ta fesa turare sosai sannan ta dawo tana ta sada kai dan kar ya kula da fuskarta da yake ta son kallo
Murmushi ya yi ya juya ya tada ikama sannan suka gabatar da sallar
Bayan sun gama dukan wasu tambayayoyi da ya dace ya mata ya yi nata ta kuma bashi gamsashiyar amsa, dan haka sai ya gabatar mata da kazar amarcin da ta yi mamakin yadda aka bata kaza bayan ba a rufe take ba, aman sai ta kore ta ki ci kwata kwata dan cikinta ya riga ya kulle bata jin dadadon abincin a bakinta, ta nuna masa da safe zata ci
Da ido ya rakata har ta haye saman gadon sannan ya yi wani murmushin ya mike ya nufi bayi shima