← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 138

Sashe 58

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta sake kura masa ido, watau an masa wani mahaukacin boyo ne da idan dai kai din kai a duhu ne ba zaka taba gane cewar akoyshi aa wajen ba, dan kuwa an saka wasu irin fitilun kwaliya ne a gefensa shi kuma an masa dabarar da ya dauki kalar fitilun suka laye da junna hakan ya sa da gagawa ba zaka fahimci cewar camera ce a wajen ba

Mikewa ta yi tana kallon camerar a hankali ta karasa wajen kujera ta janyo ta kawo kusa da camerar

Ajiyeta ta yi sannan ta dan duka ta saka hannunta ta cire pant din dake jikinta baki sannan ta haye kujerar ta daga pant din da kyau ta yadda za'a gane meye ta rufa a wajen sannan ta rufe camerar da shi da kyau ta yadda gannin camerar ya dawo duhu rudum domin a yanzun ba'a gannin abinda yake dakin ta sauka tana tsaki a bayane ta ce" Ku dora doka, kuma ku taketa da kanku, to babu wanda zai shiga secret life dina! Kamar yadda kuka dora dokar hanna saka camera a dakin barcin mutun ni babu wanda zai saka min!"

Ta koma bakin gadon ta zauna tana gyara zamanta domin ya rage mata oant daya tak kennan wanda ke rike da audugarta a jikinta ta sake kurawa hannayenta ido a kasa kasa ta shiga furta" Lalle zamu aiwatar da aikin ladan da zai hanna mu shiga wutar jahannama kafin mu saki hannun junna gaba dayanmu MUHAY, nai maoa alkawarin nuna maka menene aikace aikacen kiyaye fadawa wutar jahanama da mace ya dace ta yiwa mijinta in sha Allah......duk rintse sai na bayana maka kafin mu saki hannun junnan da ni da kai domin abinda baka sani ba koda ka ki ka sakeni ba zan rufe wata daya da kai ba sai ka sakeni ta laluma ko na maka ka a kotu!"

Da wannan kuncin ta kwonta barci, hakan ya sa ta yi barcin marar dadi, domin a takure take jikinta a hade yake waje daya tana ta juye juye dan ta samu ta daina mafarkin da batama san na menene take yi ba har garin Allah ya waye

Kusa da kiraye kirayen sallar subahi wayarta ta dauki kuka
Irin kukan wayarta kuwa wakar wata balarabiya ce mai kaudin murya ko a nesa kake kana iya jiyota bale kana barci, hakan ya sa ta farka a zabure tana waige waige da neman wayar, gabanta na yankewa ya fadi ta kai dubanta wajen wayar da kuma agogo tana tunanin mai kiranta a irin wannan lokacin ko waye ba lafia ke tafe da shi ba

A dan birkice ta wawuro wayar tana duba numbobin da zata iya rantsewa bata taba gannin numbobi masu bibiyar junna irinsu ba hakan ya sa ta ki ta daga har sai da wayar ta tsinke, aka sake bugowa

Daga kiran ta yi tana ajiyewa saman bed dinta ta saka a amsa kuwa sannan sannan ta zubawa wayar ido batai magana ba

"Na san kina jina, kuma na san kina cikin bacin rai, kar ki damu yadda ya wulakantaki haka yake wulakanta kowa, ki bani hadin kai mu nuna masa cewar shima ba kowa bane mu bashi abinda yake nema mu nuna masa shi din ashe kaskantace ne a cikin kaskantatu, zan sake kiranki na ji amsar ki a kan haka!"..........muryar da ta kasa fahimtar ta mace ce, ko ta namiji ce, tana ruwa ruwa alamu an saka wani abu a jiki dan kar a gane mai muryar aka fada mata magangannun nan da ta kasa gane inda suka dosa, da kuma tunanin ta yaya aka san ranta a bace da komaima suka sakata yin mutuwar zaune hadi da afkawa a duniyar tunanin da kiran sallah ya sakata zabura dan tsorata ta yi da jin kiran tamkar an matso masalacin yau cikin kunnayenta hakan ya sa ta yi baya da karfi ta hantsila ta..................................

Alkalamin KADARA..................................................................☺️☺️☺️☺️☺️☺️☺️ I'm back na gode da uzuri da akai min🥰🥰🥰🥰🥰🥰*ALKALAMIN KADARRATA*

NA SAJIDA

3️⃣1️⃣

Da karfi ta hantsila ta fado kasa daga saman gadon ta zabura ta mike tana zazaro idannuwanta a bayanne ta furta" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Innalilahi na shiga ukuna na lalace, ni kuma?"

Sai ta koma ta zauna gwarab saman tiles tana ta haki kamar wace ta yi gudu kafin ta dora hannunta a saman kirjin nata tana kallon waje daya a hankali ta ce" Shi yasa yake tafiyar da rayuwarsa wata iri? Wanene wannan mai tsaurin idon da ya samu number wayata? A ina ya samu number wayata? Yaya aka yi ya san ina cikin bacin rai? Ko me yake faruwa akoy ta hanyar da yake sani!"

A hankali ta karkata kanta wajen camerar da ta rufe da pant dinta dazun da safe, sai ta samu kanta da maido kanta da sauri tana zazaro idannuwanta

Cike da Tsoron haka ta mike da sanda ta fito ta shiga sauka da gudu gudu tana harhada matakalar tana sauka ta yi dakin yar uwarta da gudu ta bude ta fada ta mako kofar

A hankali ya lumshe idannuwansa a zaunen da yake a falo fitila a kashe da yar karamar wayar da ya gama sauraron komai a hannunsa har fitowarta da fadawarta dakin yar uwarta Duka kaf a kan kunnensa da idannuwansa

Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kansa a kasan zuciyarsa ya shiga ayana' An samu kutanen da kudi baya gabansuma bale ke?, Na san har sai kin yi farin ciki kafin ki taya mai son kasheni karni a doron kasa, na rasa me na yi da zafi haka, na rasa gagawar me yake yi, idan har mutuwar ce shin akoy wanda ya taba dorewa a doron kasa ne?........bawa ya cika neman fitina a duniya'

Daga haka ya mike ya saka wayar a aljihunsa ya fice a falon yana mai sake ayana' Aman zan yi asarar girki mai dadi, dan ba laifi abincinsu ya min dadi, na zata za'a bari na dan kwana biyu ina dan ci ko yayane.......'
(🤔)
Watau duk matar da ta amsa sunnan tasa koda ta wuni daya ce sai an masa tracng din numbarta ta yadda ko mesage, ko kira, ko whatsup komanta yana da damar samu da zarar ya bukaci hakan, ya samu wannan dama ne da kyar, domin abu ne da kudinka baya baka sai idan an yarda da abinda ya sa za'a iya yi maka shi da sauki, domin rayuwar mutun ta sirri tana da mahinmanci sosai a kasa ta yadda baka tashi kai tsaye ka yi haye a cikinta

Tunda ta fado dakin take koro mata bayanan nan bata ko tsayawa ta sauke numfashi har sai da ta gama sannan ta tsaya tana wiki wiki da idannuwanta wanda hakan ya saka itama cikinta juyawa tana kallonta ta ce" Kar dai a je wani soja ke son wajensa kin san fa ba karamin mutun bane a sojojin kasar nan gaba daya shine na biyu , kin ga Idan ya kashe mutun fa ba'a masa tambayar dalili an san mutumen ya cencenci kaura ne, mun shiga uku mun shigo tsakiya kar a hada da mu!"

Shuwwar ta kai zaune tana dafe gaban goshinta a sanyaye ta ce" Bama wannan ne damuwata ba, na tabata koma waye sai dai ya bi ta bayan fage ya saka da mu din idan ban masa biyayya ba, babar damuwata da yake na zo na hau kan sawun barawo ne inaa tafia, ina tsoron a kama ni a matsayin mai laifin da ban aikata ba, ina ji a jikina bana so na hau laifin da ba nawa ba Nahidt a kan lamarinsa, Domin camerar dake dakina ban yarda da ita ba sam, na fara kokonta a kan anya shi din nan da iliminsa zai sakawa iyalinsa camerar da ta kai har kuryar dakinsu na kwonciya barci dan yana tsoron kar a kashe shi? Anya kuwa ya san da zamaan camerar da ta wuce wancen ta falonsa a kafe? Nahidt anya ba yana zaune ba tare da ya san da ita bane ba kwata kwata?"

Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tana ji ana salame sallar asubahi a sanyaye ta ce" Kin gyara dakinsa kuwa?"

Shuwwar ta girgiza kanta

Nahidt ta ce" Ki tashi ki je ki kwatanta, ki yi kokari ki iya jurewa har ya bar gidan, sannan ki tambaye shi fita ku je wajen Abanki,, ni kam ina cike da tsoron lamarin nan Shuwwa"

Shuwwar ta gyada kanta a hankali ta juya ta fice a dakin da dan hanzari ta nufi dakinta

A nutse ta samu kanta da shiryawa bayan ta kai tufafinta cikin bayi da dukan abinda ta yi niyar yin anfani da shi a yau, domin a jiya bakinsa ne ya yanka wuyansa, ta yi niyar binsa tamkar bawa da uban gidansa , kamar yadda yace yana son kiyaye saka kansa a cikin wuta, zata bashi dama ta kuma nuna masa cewar a duniya gaskiya ba shi daya ke tsoron mutuwa ya koma ya tarda wutar ba, itama a kansa bata tunanin zata yi garagen da za'a tsomata a wuta

A cikin bayin ta gama komai ta fito da wanda zata shanya ta shanya su ta ajiye na ajiyewa sannan ta sake satar kallon wajen camerar nan kafin ta juya ta fice bayan ta sake daukan sansanyan turaran ruwanta ta murza a jikinta,

Tafe take tana dan motsa bakinta da tunanin yaya akai man leben da ta dan murza yake da danko a baki sosai?
Chapter 58 · 0% Book details