← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 138

Sashe 6

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

A daidai lokacin da Abdul Mutalab ke begen SHUWAR da tunanin maimakun ya kai kararta saboda million goma sha ukun mahaifinsa gwara ya nufi kampanin sadarwa a bi layinta a sanar masa ina take wacece ita hankalinsa tashe ya dauki hanyar da ta dauka ba tare da ya san asalin nan din ta nufa ba
ita kuma a daidai lokacin Jar danja ce ta tsayar da ita a cikin motar hakan ya sa ta dauki lokaci mai ban mamaki bata saki ba
Gannin kamar Danjar ta ki ta saki sai ta saki karinta ta shiga neman ribom a cikin motar ko zata ci sa'a ta samu dan ta daure kanta da shi, a irin lokacin ta taki rashin sa'a domin wayarta dake cikin motar ce ta dauki kuka tana dubawa ta ga bakuwar number, har zata share sai kawai ta daga tana ajiyewa a gefenta tana ci gaba da neme nementa hankali kwonce duda irin yadda yanzu take gannin garin shallllll sai daidaikun mutanen dake tafiyarsu a gefe da gefen kwalta aman a tsakiyar titi duma wanda ya san ciwon kansa ya nemi waje ya ajiye brakarsa dan samun kwonciyar hankalinsa

"SHUWWAR a ina kike ne?" Ta ji muryar namiji na tambayarta da kama sunnanta kai tsaye hakan ya sa ta sake duba wayar dan gannin number daidai da ana kwonkwasa mata gilas din motarta

Dagowar da zata yi ta ci karro da abinda ake fadin kana samun faduwar gaba dake hadasa maka cikinka ya juya daga inda yake ya dawo kasa , a da bata san ana juyawar ciki ba sai yau,
Hannun mutumen ta fi kurawa ido wanda hannun ke jujuye irin a mumurden nan irin hannayen da ake nunowa a film din yan indiya wanda yawancin lokaci mukan yi daria mu ce ku ji wata karya wai hannu ne haka,
Kafin take sauke dubanta a kan fuskarsa da bakin gilas din dake saman fuskar sannan ta waigo da sauri wajen da aka sake buga mata da gagawa da dan karfi tana sauke numfashi da gagawa tamkar mai cutar athsma, domin har ga Allah sai ta ajiye hakan a matsayin ita kadai ta ga halitar nan

Da sauri ta nemi fitowa dan ta kula hakan yan jagaliyar sojojin ke so ta yi a lokacin da ta sake gannin sojoji ne zagaye da ita tamkar yar ta'ada
Lokaci daya magangannun Fauziya suka ringa dawo mata a kwakwaluwarta na irin tsaron da aka saka a kasar da hanni da akai kan fita kwata kwata

Tana budewa tambayar da aka fara yi mata ta sakata shiga inda inda gaba daya ta rasa me zata bada amsa

Babur din ya caka ya ajiye ya sauka yana matsar da sojan xake yi mata tambayoyin dan ya kula kamar ana sako taushi a lamarin, gefe ya maida shi da hannunsa ya karaso daf da ita sosai hakan ya sa ta rintse ido tana dahe rai tana son gane sunna ganninsa suma ?, Kai jama'a yau ta ga halita a gabanta

Tun daga kasa har sama ya kare mata kallo a yan sekwani kama daga shigarta, da gashin kanta dake barbaje kafin ya budi bakinsa a hade ya ce" Kin yi shaye shaye ne?"

Da sauri ta girgiza kanta tana fadin" Aa walahi "

"Ur name?" Ya fada a kausashe

SHUWAR ta ce" SHUWWAR , SHUWWAR ne sunnana Yalabai"

Gilas din idannuwansa ya cire yana fadin" Bamu takardar shedar yar kasa ce ke"

Da sauri ta juya daga wajen nan da take ta saka kanta cikin motar hakkan ya sa ta bado bayanta gabansa ta yadda duwawunta ya gogi kafarsa ta hagu da ta fi kusa da ita a lokacin da bai aune ba

Kansa ya sada dan ganin meye ya taba masa kafa a wajen da hakan ya faru ya dago da sauri daidai ta sake fitowa daga motar da jakarta ta ciro katinta ta miko masa hannayenta har dan rawa suke dan so take ta zauna ta fahimci wannan bawan Allahn mutun ne ko ba mutun ba?

Takardar ya amsa ya dan matsa yana dubawa ya dago yana tsatsareta da kakausan kallo ya ce" A nan an rubuta *IBTISAM*, kin ce sunnanki *SHUWWAR*, "

Hannayenta ta shiga hadawa tana son yin magana a kausashe ya ce" Saurara, ki tabatar abinda zaki fada gaskiyarki kennan domin tsagera na fito kamawa kuma na fara haduwa da ke, kin ga gaba dayanki kama kikai min da wada ta sha giya, sannan kikai min kama da barauniya, da kuma wace bata jin magana, so ki dan saukaka min kama ki mana? Idan kika wahalar da ni zan wahalar da ke ne"

SHUWWAR ta matse fuska sosai tana kikifta ido, a kasan zuciyarta a yau harta da bakon ashar ta hada ta laulayawa wannan gabjejen abin dake gabanta a tsaye, da ya san kudurinta a kan sojoji da bai tsayar da ita ba, wai yar shaye shaye, barauniya, marar jin magana, aka kai ikon kasar nan sata? Aka kaisu yin mankas? Bale wannan aba wai ita magana ai basu san inda aka rawaito jinta ba, shine shi zai tsaya mata a ka ya yi maganar nan?
Sai dai ta san a yanzu a nan da take tsakiyar kartin nan idan ta yi wasa sunnanta nama, babu abinda zai raba shi da ita kuma sai Allah
Iya gaskiyar lamari a kan maganar sunnanta ta budi baki tana sheda masa ta ce" Walahi sunnan IBTISAM shine asalin sunnan da iyayena suka saka min a garin Riyad, na cenza sunnan nan ne sakamakon sakina da mijina na biyu ya yi a lokacin da na tare a gidana yana sona ina sonsa aka raba auren, Yalabai ba zan manta ranar da Salisu ya mikon takardar nan fara ba mai bakin rubutuuuuuuu......" Sai kawai ta fashe da kuka tana fadin" Yalabai yana kiran IBTINA, ki yafe min, ina maimaita haba habiby kar ka sakeni ka tonan asiri yar bindin uwar babarsa ta saka ya yankan tikitin wahala nake yawo a titi ........Shin Yalabai tsakani da Allah wannan abin adalci ne??????"

A daidai likacin da MUHYIDEEN ke sake kallon wannan yarinyar sannan yana sake yarda da maganar da akai masa cewar garin nan gari ne na tsagera, yana jin sha'awar yarda da zama a garin na shiga zuciyarsa wata motar ta sake kawo kanta wajen wada ba shi ba da ya mutu da mamaki da rashin kunyar wannan mai shige da yan wiwi din ba, harta sauran sojojin da suka saki baki da hanci sunna mamakin wannan yarinya da ta budi baki take magana kanta sake hankalinta kwonce tana yiwa ogansu hira tana bashi labarin abinda ya faru da ita kamar bata san waye MUHYIDEEN ba? Suka juya sunna gannin fitowar Abdul Mutalab dake nuna takardar wuyansa yana gaishe su da girmamawa har ya samu kansa a inda take din da gaskata abinda aka fada masa na wajen da take ya ja da sauri gannin wanda ke tsaye a gaban SHUWWAR din

Wani dunkulelen yawu ya hadiye yana hado jarumta irin tasa ta d'a namiji yana hanna kafafuwansa yin rawa a gaban SIR LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN ya ja daga dan nesa jikinsa bai boye rawar da kafafuwansa ke yi ba ya ce" Allah ya kara maka lafia Sir wannan din matata ce, fushi ta yi na biyota dan na bata hakuri , dan Allah a yi hakuri a bani ita mu tafi gida ita batama san da dokar da aka dora na kar a yi yawo a cikin gari yau da gobe har sai an gama taron nan ba"

SHUWAR da zuciyarta ke dukan casa'in ta raba bayanta da jikin motar da dan sauri ta yi bayan MUHYIDEEN dake son fuskantar bayanan Abdul Mutalab tana zarro ido tana sake leko dan gidan Elhaj mai shinkafa da mugun mamakin irin gileliyar karyar da ya gila wace ko wuka za'a dora mata a wuyanta a yanzu zata iya fadin cewa babansa ne ya turo shi ya kasheta ya amshe kudin da ta karbo, Au ya kai masa ita
hakan ya sa daga bayan MUHYIDEEN take danna zuciyarta dake neman balowa ta fito ta bakinta ta kasheta dan tsoro da firgici

Bayan MUHYIDEEN ya karanta sunnan dake saman bage din Abdul Mutalab dake tabatar da shi din cikaken likita ne a asibitin gwamnatin kasar ya dago ya sake kallonsa da mamakin jin wai wannan matarsa ce,
Sai a lokacin ya fahimci yarinyar nan a bayansa ta labe hakan ya sa ya dan ja baya yana bata damar bayana a filin Allah ya ce" Meye shedar da zata tabatar min da iyalinka ce wannan?"

Da sauri Abdul Mutalab ya ce" Akoy shedar kudinta dake cikin bak'ar jakarta Million goma sha uku , Code din jakar kuwa shine 098526, ga kuma dan kwalinta dake hannunna da ta bara min ta fito, ka yi hakuri Sir zamu koma gida mu sasanta kanmu"

Da karfi ta ce" Da wa?, Ka koma gida da wa? Ka ga ba inda zan je yanzun, zan biyoka Daga baya ka je kawai ka fara tafiya kawai"

Tsitttt wajen ya dauka yan kwararin mutanen dake wajen masu kakin soja suke kallon kallo hakama Abdul Mutalab ya gama sarewa cewar idan har ta yi yadda aka fahimci tafiyarsu ba daya ba zata ja da farar rigar tasa ta likita MUHYIDEEN ya karkata masa kai, me yasa zata yi haka ne?

Motar MUHYIDEEN ya karasa ya saka hannunsa ya bude ya ciro jakar yana ajiyewa a saman motar ya shiga saka numbobin da ya fada ya bude jakar

Da mamaki ya kale shi yana fadin" Wani abu kuke yi a kasar nan da yake kawo maku kudi irin haka da har matarka zata malaki irin kudin nan ya kasance har tana yawo da su a sake cikin kasa?....." Ya maida dubansa kanta yana fadin" Menene sana'arki?"
Chapter 6 · 0% Book details