← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 138

Sashe 37

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

NAHIDT ce ta gyara mata kwonciya Fauziya ta kawo abin rufa suka rufa mata sannan suka lalayu a jikin kujerar daga Fauziyar, har Nahidt din, dama shi Hamza a sama yake yana cikin damuwar yannayin jikin yar uwar tasa wace zai iya rantsewa aa yanzu da ya sansu a kansu babu abinda ba zai iya yi ba

A hankali Fauziya ta dan dago ta dube shi daidai sun yi ido hudu, har zata cire idannuwanta da sauri sai ta ga ya sakar mata murmushi, hakan ya sa ta ji wani irin sanyi da tarin tsoron dake daskare a kirjinta na barinta, a hankali ta sada kanta tana rike hannun NAHIDT dake kusa da ita

A hankali NAHIDT din itama ta rike nata hannun tana dan murzawa idannuwanta kyam a kan SHUWWA

Dan kwalinta dake yashe da hijab din Shuwwa Malan ya dauko ya dawo yana ajiyewa gefenta ba tare da ya ce komai ba sannan ya yiwa su CHIEF OF ARMY Bismillah kan su karasa cen nesa da su kadan saman kujerun arabian su zauna su tatauna

A nutse bayan sun zauna kowane da yannayin damuwa a kan fuskarsa ya dan sauke ajiyar zuciya yana fadin" Mu yiwa Annabi sallati sallalahu alaihi wa salam"

Gaba dayansu suka amsa suka shiga yi a nutse har suka gama, Makan ya dauki ADU'A a sanyaye ya nemi dukan alkhairin zamantakewar sannan ya nemi tsari da shedan da dukan sharin dake tare da zaman, harma ya nemi alkhairin abinda suka aikata sannan ya dora da fadin" Alhmdulilah, ELHAJI DA ELHAJI, DA BABAN HAMZA, DA ABANSU dan Allah ku yi hakuri da irin abubuwan da kuka gani, ina mai karra fahimtar da ku cewa abin ne ya zo mata a ba zata, ga yannayin.......",
Ya dan yi shiru dan jin nauyin maganar a bakinsa ya furzar da wata iskar yana fadin" Zai zamto zaku dan fuskanci bambancin dabi'u da irin namu, a hakan ina matukar girmama dabi'unsu domin sunne malaman kansu, sunne iyayen kansu, sunne komai nasu..............., A gaskiya zan iya rokar Alfarmar a taimaka masu........idan na ce a taimaka masu shine a ringa sako uzuri a dukan abinda zasu aikata, a ringa basu dama sannan ana yi masu nasiha.......in sha Allah idan ta farka daga barcin nan da likita ta yi mata allurarsa zan fuskanceta a nutse kuma na san zata saurareni domin tana jin maganata sosai"

Ya dan sake yin shiru ko wani zai furta wani abin a cikinsu?

A nutse Baban Hamza ya ce" Ya Allah, rayuwa abin tsoro ce, sai nake gannin sun saba kokowa da dukan abinda zai nufo su da niyar cutarwa, tsabar sun rayu a kadaice da kannanun shekarunsu"

CHIEF OF ARMY ya ce"😭💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣9️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

CHIEF OF ARMY ya sauke ajiyar zuciya yana duba agogon hannunsa yana lalubar wayarsa a dan yana son yin call ya ce" Hakkun, hakan ba shi zai sa muma mu yi watsi da su ba, in sha Allah Allah zai daidaita lamuransa da kansa, ka ga barama na ji wajen da dan rigimar ya shige, domin so nake a yau a mika masa iyalinsa, su je cen su karata, idan har aka dauki wani lokacin ina tsoron rigimarsu su dukansu"

Malan kam farin ciki ne ya kama zuciyarsa, kamar sun san abinda yake cikin zuciyarsa kennan
A daidai lokacin da CHIEF OF ARMY ya shiga tura kira a lokacin Matar malan uwar gidan ta yi salama ta tsaya a kofa tana neman izinin shigowa domin an amsa mata aman ba'a ce da ita ta shigo ba, ita kumaa ba zata shiga kai tsaye ba

Malan ne ya mike yana sake gyara hular saman kansa mai shegen tsada wace ta amshe shi ta fito da kyansa sai sheki yake uwa shine angon ya karasa ya dagaa labulen yana amsata

Kayan abincin da ya ga ta zo da su ya saka shi sakin murmushi yana kallonta kasa kasa sosai yaa furta" Barakalahu fihk Ya Maryama"

Murmushi ta yi masa kasa kasan itama ta ce" Ya Imam, ya dace a kula da cikin bakinmu, uwa uba na amarenmu, ga abincin nan na baka ka mika?"

Kansa ya dan girgiza yana bata hanya aman ya umarci masu aikin da suka rakota kan su ajiye a nan su juya

A nutse ta ringa kaiwa tana ajiyewa a tsakiyar falon bayan ta yi salama ta gaishe da mutane
Ba tare da ta tsaya kale kale ko tsegumin komai ba ta gama ajiyewa ta juya ta fita abinta da zuciya daya bayan Malan ya sake rakata yana mai shi mata albarka da kyakyawan murmushi a saman fuskarsa wanda hakan ya sauka a fuskar Nahidt dake kallon matar tunda ta shigo har ta gama ta juya

Bakinta ta tabe tana ayana 'Kinibabiya kawai, shi kuma katon banza!'
Chapter 37 · 0% Book details