← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 138

Sashe 76

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tare a firgice suka kallota,
A zaunen da take yaren da ta yi da bakinta ba na dan koyo bane, yare ne dake zaune dam a harshenta , tun daga larabcin har buzancin

A hankali Shuwwa ta sada kanta hawayenta suka bale gaba daya a fuskarta
Mikewa ta yi tsam ta nufi dakinsu da gudu ta fada saman gado ta fashe da kuka

Nahidt gaba daya ta rikice, ta mike ta koma ta zauna tana kallon Mama zata yi magana Mama ta girgiza mata kai ta ce" Je ki kula da ita, ku yi adu'a kafin ku kwonta, zamu yi maganar da safe in sha Allah"

Wannan maganar ta hanna masu rintsawa gaba dayansu, hakan ya sa tunda Mama ta gama sallar asuba ta zo wajensu ta saka su a gaba kan maganar nan, domin idan su sun samu sun rintsama da kyau, ita ya kwana cikin tunani da mutuwar zuciya

A sanyaye Nahidt dake zaune rike da carbinta tana kallon Shuwwa da Mama ta riko hannunta tana hannata yin kuka ta shiga labartawa Mama rayuwarsu, abinda suka gani na rayuwa, irin tarbiya da soyayar da suka samu a wajen iyayensu, har zuwa ranar rabuwarsu ta karshe da su, da irin rayuwar da suka tsinci kansu a ciki daga baya, irin neman na kansu da ya zame masu dole ko dan su ci abinci......ta ajiye mata zancen a zuwansu kasar nan ba tare da ta fada mata bayan zancen ba

A hankali ya saki kofar dake bude ya juya ya fice a falon, domin dama ya yo safiya ne sakamakon kiran da akai masa cewar mutumen nan da ya kawo ga dukan alamu yana fama da tabin hankali ne, shi dai ihun da yake yi su tafi, su tafi da matarsa, yanzun sunma ki karra masa wata allurar barcin dan kar ta sake taba kwakwaluwarsa, sunna jiransa ya zo a mikashi likitar mahaukata, shine ya shigo ya gaishe da Mama kafin ya fita ya fada mata marar lafiya gare shi, sai ya tarda bata dakinta, kuma bata kicin, gashi basa zuwa bangaren Chief of army a irin wannan lokacin, sai hankalinsa ya ffara tashi da sauri har zai wuce ya ga dakin yarinyar nan a bude shine ya zo dan dubawa ya tsinci magangannun nan

A hankali yake tuki yana tunani a cikin zuciyarsa ya shiga ayanna'💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 4️⃣2️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Ya shiga ayanna abubuwa a ransa kamar haka' wani lokacin yannayin mutun na fasara irin rayuwar da yake ganni a duniya, Aman baban abun mamakin anya kuwa idan suka samu matsi sosai ba zasu saida hakurinsu da raina ba?, Idan suka gaza yin haka menene hujarsu ta kiyawa?, Idan kuma aka matsa masu har matsin ya kai da suka aikata anya ba'a shiga hakinsu ba? Yan Adam suke fa,...... MUHAY ka shiga a yannayi na sarkakiyar tunani....................'

A banagaren Mama kuwa sosai ta basu dama sukai kukansu son ransu kafin ta sake yi masu wata tambayar da ta saka su wannan karron kallon kallo tare da kasa furta mata koda A ne

Murmushi ta yi tana sake fuskantarsu a sanyaye ta ce" Ta yiwu ku ji tsoron idasa min labarinku, sai dai ban san dalilin da zai saka ku kasa idasa min shi ba, ta yiwu kunna tsoron kar na ji yaya kuka rayu bayan an cutar da ku an zo an fasa maku labarin cewa iyayenku sun rasu, iyayen nan naku da suka yi maku gata na rayuwa tsaftataciya, da dan mahaifinku za'a bi daga karatu sai barci, mahaifiyarku ke kokari da zarar ya gusa sai ta fitar da ku koyi aiki, ta dage ta koya maku dukan wata wahala da zaku iya jurewa, hakan ba yanna nufin bata tara maku ba, haka mahaifinku nemansa a kanku, an zo an kwashe komai da nufin za'a ajiye maku, sannan an nuna maku a yanzu fa ya zama wajibi ku fito ku garwaya da kowa, al'uma masu mabambantan halaya ku shiga gari gari ya ganku ku ga gari, ku saka kaffafuwanku wajen da baku taba zuwa ba, dan zalinci a rai biyun nan kacal wanda a yanzu da kuka warware kuka zama yan mata ana iya daukanki a ciyar da ki dan abincin lomomi kalilan ba da yawa ba, sai aka zabi cutarwar ta hanyar nuna maku dole ku biya hayar da kuke, ku kuma biya abincin da zaku ci, rayuwa kuma ai dole sai da cin tuwo koda babu muhali, Babu wani a kusa da zai kwaba ko ya yi fada dan a gyara, babu wata soyaya tsaftataciya da zata saka zuciya aminta harma ta samu laushin halaya, a sake ake a bakin titi babu wanda zai iya duba da soyaya irin ta musulunci ya taimaka?, To kuwa da kuke tare gar zuwa yanzu mo me kuka ganni na rayuwa ni sai dai na taya ku kukan hakan da kuma gyaran hakan, da kuke zaune a tare ni ba mahaukaciya bace ba kuma mai take ganninta bace, na tabata kun sha gwagwarmayar rayuwa a tsakanin mutanenmu masu son kansu da mugun nufinsu, masu rayuwa da son ransu da kidan ganga irin na shedan a zukatansu, daidaiku suke ganni su bari, an zo an rabu da mahaifinkama an karya masa kara a ido bale babu idannuwansa, babu na mama bale na yaya? Ina so ne tunda na fara na dire abin a ma'aunin da ya dace, menene karashen labarin da *ALK'ALAMIN KADARRARKU* ya zanna maku, IBTISAM me ya faru da ku bayan wannan?"

Shuwwa da a da take da karfin gwuiwar fadawa koma waye abinda ya faru da su da irin aure auren da suka yi a rayuwa sai a yanzu , a yanzu yanzu tsoron hakan ya darsu a cikin zuciyarta, ba komai ya hadasa maya haka ba kuwa sai gannin yau gata da ranta a gaban wata halita a duniya da ta saurareta, ta ji komai dala dala nata, harma ta yarfa da furucinta cewa bata yarda iyayenta sun rasu ba, sai take tsoron kar ta ji karashen labarin rayuwarsu da suka yi kafin haduwarsu da ita ya saka ta tsane su harma ta kore su, hakan ya sa take ta kallon bakin Nahidt da ta sake rike mata hannu ta ringa bayanawa matar nan irin gwagwarmayar da ta gani ta rayuwa, wace take dafe da ita , su fada ruwa su fada wuta su fito su kankami junna, su yi kuka su yi dariya , irin yadda maza sukai wasan kura da rayuwarsu rayuwa irin ta rabe rabe ko su ce dauki ajiye, aure aure da koke koke da wawurar auren da zarar ya gabato, fadanta da sojan da bata san wanenen shi ba haka shima, sakin da ta samu a ofishinsa har zuwa juyawar igiyar aurenta daga wuyan yayanta ya koma kansa, bayanuwar mutanen da aka ce wai dangi suke a gare su wa'inda kwata kwata suka kasa dauka da mahinmanci kai suka kasa saka soyayarsu a zukatansu harma suke neman yin nesa da su ido rufe domin su din baki ne a rayuwarsu kuma boyayun sirika ne a nasu sirikan har zuwa irin rayuwar da suke yi da SOJA GIDAN Baban gidan CHIEF OF ARMY, da zuwa shigowarsu jirgi da shi da saukarsu a garin nan

Idannuwanta cike da hawaye fuskarta shabe da shi tana kallon fuskar datijuwar dake hawaye tana kallonsu ta ce" Wannan shine labarinku, wannan shine takun salon rubutun *ALK'ALAMIN KADARMU* , mu namu ALK'ALAMIN kadarrar baya wasa Mamah, baya sasauci Mamah, ko kuma shi haka ne sasaucinsa a ganninsa a garemu? Gashi kuma mun sake bayanar da mikin dake rayuwarmu a nan Mamah, wa ya sani ko zaki kyamacemu? Allah dai shi muka rika, mu Marayu ne"

Da muryar kuka IBTISAM ta ce" Mu ba marayu bane Mamah, ta yaya za'a kyamacemu dan iyayenmu sun matsa?, Na kasa yarda da haka mama, ta yiwu ni kuma mahaukaciya ce Ba'a sani ba, dan Allah a fahimtar da ni cewa idan an mutu mutuwa batai bakin fentin da take kawo kanta da kanta ba mama, mutuwa fa ko a cikin rami ya rufta da kai da kanta take shelar kanta Mama, ita makociyarmu ita kadai ta jiyo labarin har ta fadawa kowa kuma kowa ya leka bai ga komai ba, karshema kudancewa ta yi ta tashi daga wajen da muke ta koma wata anguwar da take da mukami a cen.........shin menene a nanade a cikin kudin tarihinmu ne ?"

A hankali ta matso ta yadda zata iya kasancewa tsakaninsu haka

A hankali ta kamo hannayensu dake cikin na junna tana kallonsu sunna kallonta

Dan murmushi ta yi tana girgiza kanta ta ce" Alhmdulilah ala kulli hallin"

"Zaku iya maimaita kalmar godiya ga Allah subahanahi wata Allah kuwa?" Ta sake fada tana kallonsu

A hankali suke gyafa kawunnansu
A sanyaye ta sake furta" Alhmdulilah"

Summa da daidaya sai suke fada sunna kuma yin shiru da bakunnansu

A sanyaye ta ce" IBTISAM kin ga nima ban yarda cewar sun rasu ba"
Chapter 76 · 0% Book details