Sashe 95
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kai jama'a alkur'ani gaba daya ji take kamar ta kwala ihu, sai dai ganewar da ta yi a waje ne suke da ba'a son ihu ko sunna yara sai ta ringa rike abinta, ko ba komai da basu sha duka bama ai an taki sa'a, mamansu fa tana duka fa, wollah tana duka , tsaf zata zartar da abinda ya dace a daidai lokacin da ya dace sai dai a kwarari gaba a kuma yafe mata
Dan haka da sauri ta ringa gyada kanta tana kallon mahaifinta ta ce" Papah dama sai da Abana ya ce Sunna na ya fi ma'ana, to dai shi baya kin min abinda nake so shi yasa ya min"
Dan murmushi ya yi yana kallon dan bakin cakwaikwaiwar ya kalli NAHIDT da du take takure
Itama ya kamo hannunta yana kallonta ya ce" Istgfari bata yawa Yarinyata, duda baki da huja ta aikata haka, duba da sana'a ta cika duniya, aman kika zabi wannan kika kuma yi, na godewa Allah da ba sai da kika dawo baki da anfani ba na same ki, na godewa Allah da ya takaita abin, na kuma gode masa da ya hada ku da jajirtatu mutanen kirki, kama daga Aban IBTISAM, da mijinta, da mamanku da kuma mijin mamanku, mutanen nan ba zan taba mantawa da su ba har duniya ta tashi, zan kuma yi ta nema masu gafara a wajen ubangijinsu, domin sun rike sun kuma daidaita, ina so ki fuskanceni da kyau........a jinninki babu wulakanci, tabas jinninki na tafe ne da hau da baki da jarabawa kala daban daban, aman kuma jinninki bashi da wulakanci a ciki, shin zaki karra damkar astagfari sannan ki yi min biyaya ko yayane ?"
Itama da sauri take gyada kan nata tana jin wani irin kaunar mahaifin nata a cikin zuciyarta
Abansu ya yi murmushi ya ce" To ku je ku kwonta "
Da sauri IBTISAM ta ce" Aba ni a nan zan kwana a wajenku"
Mamanta dake mikewa ta dan balla mata harrara tana fadin" A ina? Kin ga rashin ta idon tamu bata kai cen ba, tashi ki tafi inda kike da"
Nahidt ta yi gagawar fadin" Mama yau ai a bangaren Dad maman take, ku barmu mu kwana a nan kun ji?"
Mamansu kanta tana matukar son ta kwana tare da y'ayanta, tana kuma son nuna masu kauna karara, sai dai ta rike komai a zuciyarta ta kuma bari har ta idasa nuna masu laifinsu a ilimance ta yadda gobe zasu kama kansu, ba wai dan ta riki abun a rai bane, ko daya, aman dole ne ta koyawa y'ayan nata bambance fari da baki, kadarar rayuwa kuwa ta same su babu yadda suka iya, ita da ta haifama ta yar ta tafi fa? Tana cike da tsoron haduwarta da yaronta na farko, bata san yaya zasu kaya ba, tana kuma cike da zumudin son gannin ahalinta, wai da gaske sun nemeta?
Sandar da aka ba mijinta ta kawo masa sannan ta taimaka masa ya tashi
Tare suka taimaka masa gefe da gefe suka nufi dakin da Maman Muhay ta ce cenne na barcinsu suka shiga da shi
Mama ta yaba sosai hakama shima ya yi murmushi da karamcin mutanen sannan suka fito bisa umarnin Mama suka dawo falo
Sunna Zama Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tanaa kallon IBTISAM ta ce" mutuniyar banza , da kice bakya son sunnan mana dazu?"
IBTISAM ta kalleta tana harararta ta ce" Ke da kice ba zaki yi biyaya ba mana, malama kar fa ki tsokaneni kuma ki janyo mana duka kinga dai Mama bata huce ba fa?"
Dan murmushi ta yi ta gyara ta kwonta a saman cafet din sannan ta mikawa IBTISAM hannunta
Itama karasawa ta yi ta kwonta aa kusa da ita sosai sannan suka rike hannun junna
Daga nan babu wace ta yiwa yar uwarta magana sai barci ne da ya kwashe su
Sai kusan karfe daya Mama ta fito domin sai da ta kula da mijinta yadda ya dace har sai da ya kwonta barci sannan ta fito da abin rufa tana tunanin ko sun yi tafiyarsu ne wajen Mamansu ?
Sai da ta ji hawaye ya cika mata Ido da ta ga irin kwonciyar da suka yi sunna barci
Dan murmushi ta yi a hankali ta rufa masu abin rufar sannan ta dafa kawunnansu ta yi masu adu'a ta mike ta koma ciki
Ita kam ba kwonci ta yi ba, Domin bata jin barcinma sam, zama ta yi saman salaya ta yi ta jan carbinta bayan ta yi nafila tana sake rokar Allah kariyarsa, yafiyarsa, farin ciki daga gareshi wa dukkan ahalinta
Da sasafe tana fitowa ta tarda su sunna aiki, hakan ya sa ta shiga yi tare da su, wanda hakan ya saka su cikin farin ciki
Kusan karfe goma wayar Shuwwa ta yi kuka
Da sauri ta nufi wayar dan a zatonta ko yau ya ga dama ya ga message din da ta saka kanta yi masa ba dare ba rana na gaisuwa da fatan alkhairi harma ya yi kiranta ne?
Sai dai tana zuwa ta ga number yayansu ne Hamza, ta daga suka yi hirarsu yadda suka saba, har sai da ya kusan kashewa yake fadin" Kennan da haka zamu ci gaba da yin magana da ku ba zaku fada min cewa kun gansu ba?"
IBTISAM ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri yayanmu, ko Fauzy da muka fada mata a tare muka yanke hukuncin kyaleka ka ganta da kyakyawar kama ba a irin halin da muka sameta ba, muna so ka yi mata gannin da zaka ji farin ciki ba wanda zai kona zuciyarka ba, ka yi hakuri"
Hamza ya yi dan Murmushi yana girgiza kansa ya ce" Kin manta ni banma san yaya kamanin nata suke ba? Kuma ganninta a kowani hali ba zai saka na kasa farin cikin ganninta ba, duda ita watsar da ni ta yi ?"
Mamansu da hankalinta ke kan Shuwwa tunda ta furta yaya Hamza ne tana sauraro, kasancewar dakin shiru ne sosai domin ko panka ba'a kunne ba AC ne ke kunne kuma basa hayaniya dan mahaifinsu yana dawowa daga masalaci ya koma ya kwonta ya sa ana iya jin maganar dake faruwa sama sama , dan haka a samu kanta da amsar wayar ta karra a kunnenta har ya dire maganarsa
A hankali ta sauke ajiyar zuciya , muryarta na rawa kadan ta e" Hamza.....?"
Tsai ya yi da dan cin abincin da yake yi zuciyarsa ta bada wani irin bugu mai karfin gaske
A hankali ya lumshe idannuwansa kafin ya katse kiran yana lumshe idannuwansa tare da jin yadda gummi ke neman karyo masa sakamakon jin muryar mahaifiyarsa a duniya
A dole ya mike daga cin abincin ya nufi hanyar ficewa dan ya tarda babansa ya sanar masa cewar yau har ya yi magana da mahaifiyarsa, ya ji muryar mahaifiyarsa shi Hamza
___________________________________
Washe gari
Dukan yadda maman MuHay ta kai da tunanin lamarin maman su Shuwwa abin nata ya wuce haka
Ko a yanzu aiki suke yi a baban filin girkin gidan, gaba dayansu ne suka hade suke girke girken sakamakon sanar masu da Dad ya yi cewar su Muhay zasu taso tare da Malan, da Hamza
Du irin yadda Maman Muhay ta so ta yi zamanta duba da akoy gajiya a tare da ita a ganninta, sai Maman su Shuwwa din ta nuna mata cewa ai ita ai zama a waje dayan nan ne gajiyarta walahi, dan Allah ta barta ta kama masu aikin
Ai kuwa tana kallon girke girke, girke girken irin na larabawa, kayan sarafawa ne wasun babu su aman da wa'inda ta samu ta yi anfani
Cen kusan karfe biyar na yamma ta kai dubanta wajen Mama a hankali ta ce" Mamansu inace da mijin Ebtisemmmmmmmm ne za'a zo yau din?"
Mama ta waiga itama ta kalli Shuwwa, harga Allah tun dazu take ta son ta ce ta tashi ta je ta shirya tarbansa ko yayane, itafa so take su tare dan har yanzun mamakinsa take yi, sam bata ga alamun ya taba kusantar iyalinsa ba, wannan abin ke daga mata hankali walahi, har yanzu fa tana cikin tunanin abu biyu, to wai ko bashi da lafiya ne? Ko kuma baya ra'ayin mata ne..? Subahannalah sosai abin nan ke damunta bata san yaya zata cire a ranta ba, kuma tana kallo fa yarinyar nan fa na iya bakin kokarinta, gaba daya shi dinne ke saka mutane a wani tunanin daban
A nutse ta gyada kanta tana fadin" Eh maman IBTISAM, da shi za'a zo"
Mama ta sake waigawa wajen shuwwa da mamaki a saman fuskarta ta ce" Ke , me kike yi har yanzu a zaune ne?"
Shuwwa da Nahidt suka dago a tare sunna kallonta
Da wani mamakin ta ce" Ba yau mijinki ke dawowa bane?"
Sake kallon Nahidht ta yi domin abin ya mata banbarakwai, sai dai da sauri ta sake juyowa kan mahaifiyar tata a lokacin da ta ce" Ya ina magana kina waiwayarta ne?"
Da inda inda ta ce" Eh, Eh haka Mama tace yau zai dawo"
Da wani mamakin ta sake kallonta jin wai haka Mama tace, me kennan? Yaya zaman auren y'artata yake ne yanzunma? Ko dai daurawar kawai aka yi sunki yarda su gyara zaman nasu?
Miyar Agushin da take yi ta bude ta daidaita dandanonta sannan ta rufe ta sake juyowa da haushi haushi ta cire ludayin cikin miyar ta nufo Shuwwa dake kikifta ido ita bata san me maman nata ke nufi ba💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 5️⃣6️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*