← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 138

Sashe 1

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

"Wayyo, wayyo Allahna, wayyo na mutu na lalace Innalilahi wa inna ilaihi raj'une wayyo wayyo zuciyata wayyo ku taimakeni zuciyata"...................... A duken da take a kusa da famfo take wannan kururuwar tana dafe da gaban kirjinta dake yi mata zogi tamkar zata mutu, dagowa ta yi tana doke hannun yayarta da ta miko da niyar riketa tana fadin" Walahi kika yi gigin tabani ke kuma sai na lallata maki fata, sai na jaki a wajen nan mun mutu ta yada zamu ba duniya lafia kowama ya huta"

Ta sake dafe kanta tana kurma wani ihun kukan tana fadin " wayyo Allahna Wayyo duniya"

"Dan ubanki ko maimaicin rasuwar iyayenki ne ya faru a yanzu kya yi wannan kukkan ina ce sai dai ki yi adu'a ko kuma ke din kin isa ki hanna abinda Allah ya kadarta maki? Meye a ciki? A kanki aka fara? Ko a kanki za'a kare ne? A me kika dauki kanki ne? Ki tashi mu shige ciki tun kafin jikinki ya fada maki dan kin fara isata na fada maki!!" Yayar tata ta fada da ihun da ya saka itama mikewa tana sake warce hannunta ta ja tunga wannan karron tana kukan mai karfi ta ce" To wannan jaraba da me ta yi kama, Aure uku? Dai dai dai sau uku aman Ko daya ban kwantashi ba bale a yi tunanin na samu d'an da zai min adu'a idan na mutu dan kawai ina karkashin ikon ki, ke kuma kina aikata laifinki? Du a tunaninsu uwata ce keh, dan Allah ki rakani na cewa Elhaj ke yayata ce iyayenmu suka mutu suka barni daga ni sai ke, ki zo mu je ya maida aurenmu da shi dan girman Allah na gaji da yawon zawarcin, wayo Allahna ni aure nake so, me yasa kika aikata kwartanci da mijinki aunty?"

Dau ta dauke fuskarta da wani wawan mari sannan ta saka hannunta ta hankadata cikin gidan da mugun karfi tana dane zafin da maganar kanwar tata ke yi mata a zuciyarta idan tana furucin nan a gareta

Tana turata tana tirjewa har sai da ta samu da kyar ta idasa sakata cikin gidan da kyau sannan ta mako kofar ta saka sakata ta juya da gudu ta warto wani ice ta yi kan kanwar tata tana fadin" Amshi ki kashe ni, na ce amshi ki kashe ni! Banza wawuya da baki san ciwon kanki ba, ni abin barkata ne da ya sakeki domin ba namijin kirki bane shi dan ubansa, sai me dan ya sau ki? Na ji ni abinda na aikata kennan shi shegu nawa ne da shi a waje? Ki kasheni na ce sai ki yi zamanki ke daya kwalin kwal a cikin duniya, sau nawa zan ce maki ki yi hakuri ki daina gagawa naki mijin na zuwa inda kike? Bari ki ji du katon da ya kama ki da laifin wani ba naki ba dama jiranki yake, ke kina manta *ALKALAMIN KADARAH NE?* ke kin isa ki daidaita taki kadarar ne?, Dan ubansa Elhaji mai shinkafar nice zai ce na haife ki? Ki zauna babu inda zaki je aurenki kuma ya mutu shi kuma walahi walahi zai ga aiki da cikawa, zan iya jure komai banda wannan, ni karuwancina a bayane yake, shi boyayen nasa zan bayanar, haka kuma yadda ya zagar min ke da sunnan karuwanci walahi sai na tona masa asiri!" Ta karashe tana jefawa kanwar tata icen da yake hannunta da burga dan ta san ba zara rotsa mata icen nan ba ai

Ai kam bata ankara ba ta ga ta wawuri icen
Ido ta zarro tana kallonta hakama Fauziya gannin ta dauki icen sai ta sake tsorata tana karra share hawayen fuskarta tana basu hakuri aman ina, a yau gaba daya agolancin ya motsa, sai sun yiwa kansu rauni ko zasu saurari wani

A haukace ta nufi yayar tata tana fadin" Bas, lah ba'as, na gwamace na soka maki wannan icen uban kowama ya huta!, Shekararmu nawa a hausa? Dalilinki an lalata mana takardar shiga saudiya!, An min hanyar zuwa ni dan na yi sana'a kin bi kin toshe, a nan din sana'arki bayananiya ce, ina son zaman aure aman ya gagara, sai na yi aure a watsar a sakoni kamar ni na fi kowa abin fade a kuguna, kin ga gwara mu mutu kowama ya huta, *NAHIDT* gwara na soka maki na san na kashe ki na je na yi kasonki tunda a hausa kaso ake yi ba gile kai ba!"

Ihu NAHIDT ta saka da gudu ta yi bayan Fauzy tana fadin" Fauziya kin ga duniya ko? Kanwata zata kasheni dan an saketa a aure? Yau na ga jaraba da kike cewa na bar kula Hajoji da me zan biya wuta, ruwa, da hayar gidan nan da muke ciki? Kin fini kyau da komai aman na haramta maki yi, ni zan yi na cida ke na shayar da ke na tufatar da ke, yaya kike so na yi ne? Bamu da dangi, iyayenmu sun je cen sun hadu sun yi aure sun zubo mu uwa tumakai sun je sun mace a wajen arfa yanzu kuma ni ce mamanki nice babanki, ni kadai na ragee maki shine zaki kashe ni? Lalle ke yar agula ce *SHUWWAR!*"

Gajiya ta yi da zagayen ta yar da icen ta yi ciki da gudu tana gurnanin kukanta ,balema da ta yi arba da akwatunnan lefenta da komai da komai sai kawai ta zube a gabansu tana rusa wani kukan tana dora kanta a saman daya daga cikin akwatunnan ta ce" Haka salisu ya sakeni saboda yayata bata jin magana, Aka zo kan Mus'ab yana kuka ina kuka aka rabani da shi dan kawai yayata budurwar mijin mamansa ce, yanzun kuma Elhaj ya sake ni dan matarsa ta ce masa mamana karuwa ce? Yayata ce ma fa Elhaj ba mahaifiyata bace, wayyo *ALKALAMIN KADARATA MAI CIKE DA RUWAN TAWADA NE, ZANNA NI YAKE YI A GIGICE, TSARANI YAKE YI A HAUTSINE, RUBUTANI YAKE YI A KARKACE, GAMU A KASAR DA BAMU SAN AINAHIN ITACE TA IYAYENMU BA, GAMU A ZAUNE MUNA RAYUWA TAMKAR TUMAKI.......SHIN WANENE WANNAN WANDA TAKE CEWA ZAI ZAUNA DA NI BA RUWANSA DA WANDA YAKE RIKONA? SAI DAI IDAN DAN BARIKIN NE SHIMA, SAI DAI IDAN BASHI DA MAFADA A DUNIYA NE*....." Ta idasa maganar kasa kasa sosai ta yadda zaka gane daga kasan zuciyarta take jin ciwon abinda yake damunta, a nan tana kwoncen nan hawaye wani na korar wani ta sauke dara daran idannuwanta a saman kunshin da akai mata mai ruwan maroon wanda ya wani irin daukan kalar fatarta ya haskata tamkar kwai

Da karfi ta budi bakinta tana ambatar sunnan yayarta wace ke tsaye a kofa sun yi cirko cirko ita da Fauziya

A tare suka kalli Junna ta daga kafarta zata shiga Fauziya ta yi saurin rikota tana fadin" Kar ki je NAHIDT, kin fa san idan ranta ya bace komai yi take yi"

Nahidt din ta share kwalar da bata so kowa ya gani tana fadin" Yaya kike so na yi Fauziya? Zuwa zan yi, ba zata iya ilatani ba, ranta ne a bace zata sauko in sha Allah, ko yanzun da ta kama sunnana na san ta fara saukowa ne kin fa santa sarai"

Fauziyar dai na bayanta a hankali har suka idasa shiga dakin

A yadda suka sameta sai da su dukansu suka kamu da tausayinta mai matukar yawan gaske

A hankali yayar tata take dan matsawa tana fadin" Na'am?"

Shiru ta yi mata bata amsata ba, hakan ya sa ta sake matsawa sosai muryarta a sanyaye matuka ta ce" *SHUWAR* gani na zo, ji na yi kamar kin kirayeni"
Chapter 1 · 0% Book details