← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 138

Sashe 15

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A sanyyaye ta amsa salamar da ya yi mata sannan ta ce" Aba, Sudais din ne ya ce maganar turowar saura kwana uku na tuna maka , shine nace to zan tuna maka, Aba na masa maganar na fi so su zo da shirin yin komai harda daurin aure, bana son harkar bikin nan Aba domin idan na ce a yi biki ina iya janyowa kaina wata fitinar, shine ya ce Shima gidansu yan sunnah ne basa bidia, basa irin haka basa bukukuwan nan hakan ta fi gyara su"

Malan ya amsata a nutse yana adu'ar Allah ya sa alkhairi ne

Ta amsa da " Amen Aba alkhairin nema in sha Allah, Aba ka ga ya fara ankara da halayan aunty ko? Domin ya ce na yi mata maganar shigarta da yawan yawonta, Aba shin idan na kaita wajen yan Hizba ba zasu nutsar da ita ta daina wannan halaya ba?"

Da sauri NAHIDT ta juyo tana kallon SHUWWAR tare da zarro Idannuwanta, Fauziya kam ta mike tsagal ta yi ciki dan ta san ba za'a wanye lafiya ba

A sanyaye ya mike daga falonsa ya nufi hanyar waje
Ba dan yana jin tsoron iyalinsa ba, aa, sai dan kauce bacin ransu a irin wannan lokacin da suke karatu baki dayansu a falon nasa, duba da sun kulafurci alakarsa da yan matan, fitowa ne basa yi su zuba masa rashin da'a dan alfarmar lazumin dake bakinsa dake sakawa kowama shayinsa

A sanyaye yake sauraron muryar NAHIDT din dake fadin" Da kike hadani da shi kin ga na shiga harkarsa ne ko kawai ki sa ya tardoni nan ya min abinda ba shi ba? Da kika fada masa har ya yanke lokacin aurenki ubankine shi? to bari ki ji ban yarda ba, babu mai daura maki aure nan da kwana uku sai kace marar gata marar galihu, sai an yi biki irin na kowace y'a, ba wani yan sunna yan izala ne su masu tsirfa , to kaniyarsa shi da sirfarshi, dama ni sam bai wani yi min ba, sai na yi biki! Kuma so kike ki hadani da yan Hizba? To dan Allah ki kaini idan sunna so su bani sana'a mana, yau na ga jaraba daga ke har masu daure maki an je an yin!"

Murmushi ya yi yana girgiza kansa sannan ya daga idannuwansa yana kallon sararin samaniya

A hankali ya ce" Allah ya shirye ki, in Sha Allah sai na daura mata aure jibi, ki kaini kotu idan baki yarda ba, kinga ta nan sai mu samu mu mikaki hannun yan hizban idan ya so sai mu ga fitsara shin zaki kalle su ki tata masu ne ko zaki yi laushi? NAHIDT ALLAH ya shirye ki"

Wayar ta warta a hannun SHUWWAR dake girgiza kafafuwanta tana ingoying da fadan su domin idan sunna yi abin haka kawai yake sakata a shauki ta maka mata harara sannan tana hararar wayar ta ce" Malan, na ce SHUWWAR din nan kanwarka ce ko tawa? Ina ce kanwata ce, uwarmu daya ubanmu daya da ita, wace aya kake tofa mata da take jin maganarka sama da tawa? Na ce ba zaka daura mata aure ba ka ji?"

Muryarta cikin fada take yi masa magana, sannan da take yi masa maganar sama sama abinta, aman kalkala irin ta wanda larabci yake yarensa, wadda ta tashi a cikin larabawa na yiwa harshen nata linzami, haka kuma da take yin ihun tana hadawa da larabcin ne har idannuwanta na rufewa, hakan sai ya saka shi sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" NAHIDT ?"

Kin yin shiru ta yi da farko ta ci gaba da maganarta har sai da ya sake furta sunnanta a sanyayen sannan ta ringa inda inda kafin ta ce" MeMeMeye?"

Idannuwansa ya bude yana fadin" Ki yi magana kasa kasa ta yadda muryarki zata yi kasa da tawa kin ji?"

Haushi ne ya kamata ta kankance idannuwanta, sai dai a rashin sanninta muryar tata fa ta yi kasan ta ce" Kana nufin ga abinda nake yi maka magana a kai cewar ba zaka daurawa kanwata aure ba shine a gabanka ba ta matsalar da kai ka gabu cewar muryata na sama da taka shine ka dakatar da furucina ne ya fi mahinmanci a kan maganar nan? Malan fa.....Malan fa?"

Har ga Allah yar dariya ya yi na karashen maganarta da ta ce Malan fa, irin idan kana yiwa d'anka fadan nan da zaka ce wane fa din nan?

A sanyayensa ya ce" Eh haka na ce jibi zan daura mata aure kuma bana son ki yi taro kin ji?"

Ido ta kifta tana kallon yadda Shuwwar ke sake daura kafa daya kan daya a saman kujera ta ce" Idan na ki me zaka yi?"

Lebensa ya cije yana jin irin balakin dake kunnun masa a kan lamarin yayar SHUWWAR , yakan fadawa Allah cewar shi kam ba zai iya ba, a sanyayensa ya ce" Ko na zo sai mu ga abinda zai iya faruwa ne NAHIDT ?"

Gabanta sai da ya kwonci kwonci ya fadi, haka kuma hannunta ya fara dan rawa tana kallon wayar tana kallon SHUWWAR da ta kureta da kallo

SHUWWAR ta kanne mata ido daya ta ce" Ki bashi amsa ya zo ku yi maganar a fili ne ba ta waya ba?"

Yatsa NAHIDT ta nuna mata tana wurga mata wayarta a jikinta ta ce" Bari ki ji, babu wanda zai daura maki aure ko waye, shi kuma da yake nemana da fada ba zan kula shi ba, dan ya san darmin ginda gareshi a anguwa idan na kula shi a ce na masa rashin kunya a hayaceni, ba zan kula shi ba aman ke, ke, na isa da ke walahi!"

Daga haka ta nufi dakinta da sauri tana karrra kallon hannunta tana jimke shi tana bude shi dan rawar da yake yi mata

Murmushi Shuwwar ta yi a bayane a sanyaye ta ce" Aba ka yi hakuri da abinda ta ce ka ji?"

Murmushi Malan ya yi a bayane yana girgiza kansa ya ce" Ki ci gaba da neman zabin Allah , in sha Allah zan daura maki auren ranar da zasu zo, zan samu mahaifin nasa da kaina kafin ranar ta zo mu gama maganar komai in sha Allah domin ya zo masalaci bai sameni bane, zan je da kaina"

Kai take gyadawa sannan suka datse kiran ta yi kwonciyarta a falo tana mai cike da adu'ar Allah ya rufa mata asiri aurenta ya tabata, sannan ta ringa adu'ar Allah ya shiryi yayarta, gashi dai kudi ta kawo gidan ta nemi da ta fara sana'a ta nuna ba sana'ar da zata yi kayan daki zata karra mata bayan tana da komai Alhmdulilah, sannan ta zuba mata a banki da sunnanta ta boye katin bankin cewar itama ba sana'ar da zata yi , ita kam takan cire rai da shiryuwar yayarta, takan fashewa da kuka idan irin tunanin nan ya sakota a gaba

__________________________________

Karan cokulan ne ya fara hawa kanta sama sama wanda ta tabata harda gayya aunty ke cokala cokulan sunna bada kwal kwal kwal a cikin plate din dake dauke da soyayun zabi

Dagowa ta yi tana kallonta ta ce" Ki bari mana dan Allah"

Maimakun ta barin sai karra kukan bugawar da take ta yi har Fauziya ta shigo da salama tana fada masu Malan ne

Bugawar da take yi ta ci gaba da yi da karfi tana kallon Fauziyar da ta dan kura mata ido sannan ta juya ta koma waje dan ta sanar masa yana iya shigowa

Da salama ya shigo falon a daidai lokacin da SHUWWAR ta mike daga saman table din ta karaso tana amsa salamar hadi da gaishe shi bayan ta rage tsayinta sosai
Amsawa yake a mutunce sannan ya maida dubansa wajen da kukan cokalin nan ke tashi sama sama

Dan kura mata ido ya yi sannan ya cire da gagawa duda a yau shiga ce ta mutunci a jikinta aman hijab din irin lafafen nan ne a jiki , ya lafe mata sosai a jikinta

Dan gyaran murya ya yi yana furta" NAHIDT Bismillah ina son yin magana da ke"

Sai da ta bubuga sosai sannan ta wurgar da cokalin ta mike ta karaso tana zama hadi da hararen gefe da gefe

Zama ya yi shima a kujerar kusa da kofar sannan a nutse ya tabatar masu da an daura aure , iyayensa zasu zo daukan amarya zuwa dare, ya dora da fadin" Ga sadakin SHUWWAR dubu dari uku da hamsin, akwatunnanta iyayensa sun fada da kansu cewar idan ta tare zata tarda abinta a dakinta domin basa irin al'adun kawo akwatunna gidan su amarya, sai kuma maganar tarewar, ina so yanzu mu je cen gidana da ku baki daya, idan sun zo sun dauki amaryarsu sun tafi sai ku dawo nan din"

Dama sama sama kirjinta yake yi dan a shake take, hakan ya sa ta ce" A kan me ba zasu dauketa a nan ba?, A kan me ba zasu kawo mata akwatunnanta ba kafin ta tare ? Me yasa sai gidanka zasu je su dauketa ne?"

Da dan sauri SHUWWAR ta ce" Aunty"

NAHIDT ta ce" Na'am SHUWWAR, zan yiwa abanki fitsara ko?"

SHUWWAR ta gyada kai hankali kwonce ta ce" Kin ga ba haka nake nufi ba, aman ai baba shi aban, ai ya girme ki ko?"

NAHIDT ta bala mata harara da hannunta ta ce" In ba zan balla maki mari ba ki ce min shegiya, kakana ne ba ya girme ni ba, wannan aure na hudu kennan da ya daura maki, Idan kika je aka sako ki sai ki kuma dawowa nan tamkar zaki mutu, yaushema wancen auren ya mutu da zai daura maki wani? Sai na yi magana a nuna nice fitsarariya ko? To bari ki ji ni ba zan saurarawa kowa ba, du wanda zai ce zai daga maki hankali zan daga masa ne nima!"

Murmushi ya yi yana mikewa tsaye cikin shigarsa ta kamala ya saba babar rigarsa wada ya wakilci daurin auren da ita yana kallon NAHIDT ya ce" Kun ga , ku dauki abubuwan bukatarku ku fita gatanan fitowa"
Chapter 15 · 0% Book details