← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 138

Sashe 108

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fuskancesu ya ce" Mahaifina nada cutar zuciya, wace iya mu ne muka san da wannan rashin lafiya, rashin lafiyar dake hanna mahaifiyata nutsuwar zuciya domin shi ke dauke da cutarsa aman ita ke nisa rashin lafiyarsa, har abin yai mata ilar da babu maganar waiwaye sai dai hakuri da daukan danganaa na rashinta a ranar juma'a da sanyin safiya inda ciwonsa ya tashi sosai ita kuma ta yanke jiki ta fadi, daga wannan lokacin na fara maraicin uwa,............ Sannu a hankali na saba da rashin ganninta na kuma dauki dangana domin ko a lokacin shekaruna sun kai na nema na ciyar da kaina, dan dai na tashi a gida na sarauta ne ya zamto a boye nake , a kilace nake tamkar kwai, bale da kowa ya san cewa nine zan mulki kasata, harma an rigai an min sunna SULTAN tun ban kai ko'ina ba, hakan ya sa ake kakau da ni , balema dan uwan mahaifina Uncle Ibrahim wanda bawan Allahn ke koya min dukan wasu abubuwa da ya dace ace na iya na gidan sarauta ba tare da na fuskanci komai na tsana a tare da shi ba, shi kuma uncle Khamis damaa mutun ne mai matukar iza da sarauta a jikinsa, domin bana tunanin idan har sarkin dake saman sarautar kasata a yanzu ko da matansa yana hira bale y'ayansa harma a zo kaina, shi yasa ni dinma idan da halin mu zanta muke zantawa idan kuma ba halin hakan bana takurawa........"

Ya dafe gaban goshinsa ya ce" Mahaifina ya rasu ne a sanadiyar tashin ciwonsa a daren litinin wayewar talata, wanda muka tashi da gawarsa a gabanmu ana ta yi masa shinfidar kabari........"
Ya jimke hannunsa yana kallonsu ya ce" kamar yadda yake kaida haka aka bi da ni, ana dawowa daga suturar sarkina a cen cikin makabartar dake cikin gidanmu aka nadani a sarautar kasata da kannanun shekaruna ko auren fari ban yi ba, sannan aka saka ranar da za'a daura min aure da wace za'a binciko a ga ta dace da ni............."
" Na rikice, na dimauce na rasa ina zan dosa na nuna tsantsar tashin hankalina a kan ranar da na wayi gari ake kirana sarki maimakun sarkin garina kuma mahaifina, wace zan je na yiwa kukan ta rigashi kaura, hakan ya sa na kwana cir a saman salaya ina kuka ina fadawa mai duniyar da kiyama cewar zabinsa nake so, karfin gwuiwa nake so daga gareshi,na sake dora kaina na yi kuka na fada masa cewar ba zan iya ba, bani da karfin hakan, aman idan hakan ne zanen rubutun ALK'ALAMIN KADARATAH ya bani ikon cinye jarabawar cikin sauki..............., Ni dai zan iya cewa daga wannan ranar sai samun kaina na yi a garin Manzo, shin ta yaya na zo? Ni na biya ko biya min aka yi?, Ni dai na samu kaina a garin da nake jin nutsuwa a jikina, ta yiwu rabon na hadu da gimbiyar da zan dora kaina a jikinta nai mata kuka ne? Ni dai zan iya cewa babu abinda ya fi daga min hankali irin maganar waye ni, ko kuma a kai ga maganar kasata, harma a san waye asalin ni din, sai kuma ta yarda, ta amince bayan ta fada min abinda ya cirota daga gidansu itama na ji kuma na amince da hakan sai mukai aure muke zaune da junna "

Ya lumshe idannuwansa ya ci gaba da fadin" Shin wanene a cikinsu?, Me yasa ya min haka? Ina cen dinma a labe ya bini ya sake dawo da ni ya rufeni a dakin duhu ya ci gaba da azabtar da ni , ya rabani da y'ayana mata biyu masu kananun shekaru, ya kuma wulakantar min da iyalina .....ya kalleni a hali na hauka , ya ki ya kasheni da wuri wuri ya ci gaba da kallona, ko duk dan Allah ya yi da sauran shan ruwana a doron kasa ne?.............ni dai gani a zaune ina tunanin ina Uncle dina Ibrahim da yake gaba da uncle din Khamis ?, , Yaya aka yi uncle Khamis yake saman karagar mulki bayan Babu wanda ya ji mutuwar IBRAHIM?, shin me yake faruwa a Baban gidanmu?"...........ya idasa yana sake kallon su Dad da Muhay da kowa ya shige a hali na rashin dadin zuciya

A sanyaye Dad ya ce" Ai uncle dinka IBRAHIM yana rufe a gidan mahaukata, zan iya cewa a kadan ya dauki shekara ashirin da bakwai a ciki, domin wayar gari aka yi yana hauka jajir, maganar da nake maka d'ansa daya kawai ke cikin gidan sarautar a yanzu , matansama sun yi wani aurensu sauran y'ayansa mata kuma du basa kasar sai dansa dayan nan , ai yanzu inaga shima ya tara iyali kam"

Sultan ya dan girgiza kansa yana ta ambaton sunnan Allah, sai kuma ya dube shi da dan sauri ya ce" Ko dai Muhsin ne d'an nasa?"

Da sauri Dad ya amsa shi cewar kwarai kuwaa Muhsin sunnansa

Sultan ya fuskanci Tinana da ta yi mutuwar zaune ya ce" An maya, kina tune da wanda ya kawo mana sutura ya bude mana hanya cewa ya yi sunnansa Muhsin? Ko dai shine?"

Tinana ta sauke gwauron numfashi tana sake kallonsa da mamakin wai dama mijinta sarki ne? Sarkinma mai daraja? Ta gyada kanta a sanyaye ta ce" Eh haka yace"

MUHAY ya ce" Koma menene in sha Allah zai fito, a gobe da sasafe zamu juya da LIEUTENANT GANARAL MUJAHEED, option ta gaba da ya gabatar mana shine za'a dauki hoton ABA da rawani sannan a babu rawani , tuni ya sayi baban kampanin jarida ya kuma gana da mai kampanin a boye ya bashi sirrin maganar, daga goben in sha Allah zasu fara yadawa , dama komai dare a yau muka yi niyar fuskantarka da maganar ,sai gashi komai ya zo da sauki in sha Allah....... Zamu fara gannin yaya al'umar kasarka sunna tune da sarkinsu da suka nada ba wanda ya nada kansa ba?, Zamu tsintsinto abubuwan da zasu gabatar na reaction sanann mu watsa a gidajen TV da redio, koma waye a karkashin wannan lamari zai fito fili.....Allah ya bamu sa'a"

Da wannan suka ci gaba da tataunawa har daren ya yi sosai kafin ya shirya cikin dakakiyar shada fara, aka dora masa rawanin da ya saka Tinana fashewa da kuka tana kallonsa, Domin gaba daya ramar ta boye a cikin suturar da ya sha, danma ramar a yanzu gaskiya sai dai ace dan abinda ba za'a rasa ba, da kyar ya iya rarashinta yana binta da kallo akai masa hotunnan yadda ya kamata suka yi kyau sosai, sanann ya cire ya kafa hula nanma aka dauka harda wajen da ya yi murmushi mai kayatarwa duka aka dauka, ana gamawa MUHAY ya masu salama bayan ya furta kalamai kamar haka" Al'umar kasar ce zata sauke shi, sannan ta nadaka, koma wanene boye a bayan lamarin zai fito da kansa ne ko zaman kasar ta gagareshi kamar yadda ya fitar da kai, in sha Allah zai gane tadawar ALK'ALAMIN Kadarra baya goguwa, idan ta zanna ba tsumi ba dabara......"

Hakan ne, a wannan rana SULTAN ya jima rike da matarsa a jikinsa bayan ya samu nutsuwar da rabonsa da irinta har ya manta, harma ya cirewa ransa cewa zai kuma moruwa ta wannan fannin, sai gashi a daren yau sun kule a daka sun kuma yiwa junna tambaya da amsa daidai gwargwado kafin su afka a duniya ta manya, ta yara, watau dai ta masoya.......zai iya cewa ko a haka aka tashi shi kam alhmdulilah😌

Bangaren Muhay kuwa sai da dare ya tsala har kusan karfe biyun dare ya dawo, a lokacin da ya shigo ya sameta ta jima da yin barci kamar jiya a saman cafet ta dukunkune jikinta a cikin hijab dinta
Bayan ya gama kimtsa jikinsa ya dauko lalausan bargo ya dawo falon ya rufa mata kafin ya dora yar yatsarsa daya wajen kuncinta a hankali ya dan shafa sannan ya mike ya barta a kwonce ya shige ciki

Washe gari da ta farka ta gama shiryawa bayan ta gama gyaran falon, jin shiru shoru ya saka kawai ta shige ciki dan gannin yana ina ne?
Tana shiga ta samu baya nan, aman kuma kanshin turaren dakin ya gama game dakin gaba daya

A hankali ta shiga kokarin gyaran dakin, a saman bed din ta ga takarda da rubutu a jiki
Da farko kasa dauka ta yi, domin tsoron abinda rubutun ya kunsa ya kamata, sai dai gannin tana ta tsaye da kyar ta janyo hannunta na rawa rawa ta bude ta zauna tana dubawa

Rubutu ne kamar haka
*Ki rufe jikinki koda dakin Mamah zaki je, ta yiwu na yi kwana biyu ko uku....... EBTISEMMMMMMMM, ki kula da kanki*

Shiru ta yi da takardar a hannunta tana tunanin kwana biyu ko uku? Ina ya je ne? Me hakan yake nufi ne?

A hankali ta zauna saman bed din tana dauke gajeran wandon da ya cire na yau, sai ta samu kanta fa lumshe idannuwanta tana jin wani abu a kasan zuciyarta ga tarin tambayoyinta na damun kwakwaluwarta

Sai dai rashin samun amsar ya sakata dunkule takardar ta yar a nan da bacin ran yaya zai dawo har ya yi tafia bai tasheta ya fada mata ba? ta fita ta yi bangaren iyayenta
Tana zuwa bata samu mamanta ba, dan haka ta koma bangaren Maman MUHYIDEEN din, domin mahaifintama baya nan

A nan dinma ta tarar ana ta shagulgulan da suka dan daure mata kai
Da kulawa Mama ke amsa gaisuwarta sannan ta ci gaba da yiwa mutanen dake zaune bayanu, abinda ta tsinta Maman na fadi cewar aa bata so a yi gyara na fari kadai, su fa kula fa idan gadajen da aka zuba basu yiwa MUHAY ba sun sani sarai na zai yarda ba, gaba daya a yadda ta kula ana cikin shagulgula ne na gyaran gidan CHIEF OF ARMY, dan haka ta silale ta yi bangaren da take jiyo maganar su Nahidht

Tana shiga Fauzy ta ce" Shuwwa, wai dan Allah da color golding da ash color wanne ya fi birge ki?"
Chapter 108 · 0% Book details