← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 138

Sashe 81

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muryarta na rawa ta ce" Kana kallo bata motsi Yalabai, dan Allah ka rufa mana asiri ta tashi, koda bata da hankali koda me ta zama muna sonta a haka......ka ga a rashinta babu irin abinda bamu gani ba,, ashe dai da gaske da nake cewa bata mutu ba haka ne? A ina ka sameta? Ina papyna ?"

Hannunsa ya sa a hankali ya baambareta daga jikinsa yana kallonta yadda du ta rikice take son komawa jikin nasa

Kansa ya maida wajen Mama a dan hankalce ya ce" Ku shigo wata motar mu kaisu asibitin kudi,, na so na kilace shi a bashi kulawa irin abubuwan karya sihiri, aman mu je asibitin kawai"

Mama ta amsa shi da kai, shi kuma ya karasa ya saka hannunsa ya dage Nahidt daga zubun matan da ya yi ta mayar da ita gefe sannan ya sake dan rage tsayinsa ya makawa Nahidt din wani kakausan kallo gannin zata sake zubun mata ya saka hannayensa ya dauketa ya nufi motar da ita, inda su kuma suka kasance kamar idan kana son kaza ta biyoka idan ka dauki y'ayantan nan

Sosai ya kwontar da kujerar gaban ya dorata ya saka belt ya daureta kafin ya juyo wajen da suke jira ya basu waje su shiga

Fuskarsa ya hade sosai yana kallonsu kafin ya masu nuni da Mama da ta fito da ky da kanta , masu tsaronta na biye da ita ta dakatar da su ta karaso tana dubaa number dake jikin abin ky din har ta gane ko ta wace mota ce ta dauko dan haka ta zagaya da kanta ta yi Bismillah ta bude ta shiga da tunanin yaushe rabonta da yin tuki

A nutse ta fitar da motar daga layin ajiyeta ta dawo kan hanya, hakan ya sa ya masu nuni da cen zasu shiga

SHUWWA da muryarta ta disashe tana kallon fuskarsa kanta a dage a sanyaye ta ce" Aman me zai hanna ni na shigo nan din yalabai?"

Sai da ya dan rintse idannuwansa kafin ya bude a kan lebenta shima ya furta" Haka na yi ra'ayi !"

Da sauri NAHIDT ta ja hannunta suka koma motar da Mama take suka shiga kowace na dan dagowa tana hangen tasa, har ya gama waya da baban datijon Malamin da yake masa taimako kafin ya koma gaba ya shiga ya tayar yana sauke ajiyar zuciya ya dauki hanya

Sunna isa babar asibitin aka amshe su
Likitocin da ya samu mutane ne da suka sanshi suka kuma bashi daraja ba ta karfi da tsoronsa ba, sai ta cencentarsa a matsayinsa na nagartacen mutun mai boyenyen kyakyawan halaya, sun saba amsar marar lafiya daga hannunsa, sun kuma saba bashi kulawa

Sau dukansu sun zauna ne sun yi jigum jigum, uwa uba irin kukan da suka rikice da shi su biyun du sun rikita masa uwa baiwar Allah sai janyo su take yi a jikinta tana faman rarashi da faman bada baki a lokacin da suka ga ashe harda mahaifinsu a cikin motar nan, kuma mahaifinsu dogon mutun mai cikar halita da kwarjini ne ya dawo haka sai gaba daya suka sake rikicewa da wani koke koken wanda yake hahauda ciwon kansa

Gwuiwoyinta a kasa suke, kanta a saman cinyoyin Mama, hannayenta a zagaye da kaffafuwan Maman tana kukanta ba ji ba gani, hakan ya sa jikinta ke rawa, kuma hijabin ya sake dame mata jikin sosai, dama irin mai bin jikin nan ne

Doctern ne ya zo ya dan tsaya a gefensa yana mai yi masa bayani a kan dukkan abubuwan da suka dora su a kai, ya sake yi masa bayani a kan ciwukansu zasu samu sauki idan har sun samu kulawar da ta dace, ya dora da fadin cewa baban abinda ya fi yi masu ila itace yinwa, ya karashe da dora tambayar mamaki yana kallon MUHYIDEEN dake sauraronsa yana kuma amsar dukan takardun da yake miko masa kamar haka" Sir ama da mamaki, bayin Allahn nan a wani daji kuka samo su haka? Kuma na ga yar budurwar nan na kuka kamar ta hada jinni da su, sorry yar kyakyawa zasu samu sauki ai cuta ba mutuwa bace, dama cutar ke samuwa da gagawa lafiya kuma yar a hankali ce in sha Allah.................."

Yar budurwar da ya fada ya nuna ya karashe maganarsa a kanta ya juya ya kai dubansa kanta, hakama Mama dake ta rarashin su ta dago tana kallon Likitan da MUHAY dake tsaye yana sauraron bayaninsa

A hankali ta rage muryarta sosai tana ta ce" Ku yi hakuri da kukan nan haka, kun ji fa likita ya ce zasu samu lafiya kau? Ku mu yi masu adu'a shine zai sa su samu lafiya ba kuka ba............."

Takardar ta karshe ya amsa a hannun likitan ya juya ya fita bai ce komai ba

Likitan ya yi dan murmushi shima ya sake komawa dakin hutun da aka ajiye mutanen kowane da dakinsa, dakunna ne masu tsadar gaske , asibiti ce tamkar a turai, komai abin kallo ne abin ba'a cewa komai, ya sake duduba komai ya gamsu da komai da irin karrin ruwan da aka jona masu mai dauke da vitamine din da zai saka su cin abinci da sauransu sannam ya juyo ya dawo ya wuce office dinsa dan ci gaba da duba mararsa lafiya

An dan dauki lokaci ya dawo da waya a hannunsa ya mikawa Nahidht ita sannan ya kalli Mama ya ce" Ta koma Gida"

Mama ta kalle shi tana ayanna' Zama ka kawo kanka ne' ta dan gimshe tana fadin" Ban fahimta ba"

MUhay ya ce" Ta koma gida ta yi kukan a cen"

Mama ta dan tabe baki tana fadin" Ba zai yiwu ba ai Ka ga ba zata iya nutsuwa a gida ba bayan iyayenta a nan a kwonce"

Dan juyawa ya yi yana kallon yadda yayar tata ke kuka tana ta gyada kai ga dukan alamu rarashinta ne Aban na Shuwwa ke yi domin ya ce yana ta kiranta baya samu hankalinsa a tashe, shine ya bashi ita, kuma ta bude baki sai zayane masa komai take yi hankali kwonce kuma gashi sai ajiyar zuciya take yi ga dukkan alamu rarashinta yake yi, ya cire kansa ya dawo wajen Mama ya budi bakinsa da kyar ya ce" Za, zamu, zamu koma ta cenza kayanta mu dawo Mahmanah........."
Irin yadda ya karashe Mamanah din ya saka Mama dan murmusawa a hankali ta dan ringa shafa kan Shuwwa ta ce" Daughter, tashi ku je gida ki yi wanka ki dauko mana abinci da abin bukata, idan kuka dawo sai Nahidtma ta je ta kimtsa ta dawo kin ji?"

Kanta ta dago hakan ya sa ya zubawa fuskarta da ta yi jajajir ido da lebenta da har suka dan tasa dan tsabar kukan da ta ci da ranta

Yar ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya koma bakin hanya yana kallon wucewar mutane har suka gama magana da Mama da kuma Nahidt da ta bata Abanta sukai magana wanda a sanyaye ya ce" Kina ji yar gidan Aba, ba kuka ya dace ku yi ba mana, farin ciki ya dace ku yi, sannan ku godewa Allah, in sha Allah jirgin gobe da ni zai taso zamu zo mu yi ta fadawa Allah, in sha Allah ko menene zai zo da sauki kin ji?"

Kanta take gyadawa tana dan hawayen ta ce " Abahnahhhhh, ba ka ga yadda Abunah ya dawo ba"

Irin muryar nan mai hade da kuka da shagwaba ce ta yi anfani da ita hakan ya sa ya dan sake juyowa yana kallon wayar dake hannunta da kuma kunnenta

Juyar da kansa ya yi har suka gama ta taho tana tafe tana rangaji ga ciwon kai, ga tashin hankali gaba daya sai take wani rangaji tamkar zata kifa haka take ji da kyar ta iya fitowa har ta samu ta bi bayansa dan Mama ta ce shi zai mayar da ita gidan ta cenza kayanta, gaba daya tamkar ba Shuwwa yar rigima da fitina da kaudin tsiya ba, wannan lamari ya sa gaba daya jikinta ya mutu bata da wani karfin aiwatar da komai sai ido

Tunda ya fara tukin bai tsaya ya kalleta ba har suka karaso gida ta bude ta fice ta nufi bangaren Mama

Motar ya rufe Shima ya fito ya nufi bangaren na Mama

Yana shiga masu aikin suka ringa gaishe shi

Sai da ya gama kare masu kallo kafin ya salamesu ya nufi dakinta

Bai tsaya neman izini ba ya tura kofar ya shiga, a lokacin tana daure da tawul a kirjinta

Sosai gabanta ya fadi, harma ta so zabura ta rufe suturar jikinta , sai dai irin yadda sukai ido cikin ido ga rashin karfin jiki ga dacin zuciya sai ta kasa kwakwaran motsi bale har ta aiwatar da abinda ta yi niyya

A nutse yake takowa yana sake saka idannuwansa cikin nata har ya matse mata wahe sosai yana kallon fuskar tata ya ce" Shi din danginku ne?"

Kasancewar bata gane ko wa yake nufi ba sai ta samu kanta da kurawa bakinsa ido tana ta son gane wane?

Huci ya furzar yana kallonta a dan kausashe ya ce" Shi din ta ina ya zama Abanki?!"

Da dan sauri ta kalli fuskarsa, sai kuma ta sada kanta , ta sake dagowa zata yi magana ya daka mata tsawar da ta saka kanta mugun sarawa harma ta saki Tawul din da take rike da shi da hannayenta dan kar ya fadi, sai dai sarawar da kanta ya yi ita kanta bata san a lokacin da ta sake shi ba ta kai hannunta dan ta rufe idannuwanta da shi, hakanma ta ga kamar rufeta zai yi da duka, hakan ya sa ta karaso da sauri a haka din da take ta sake rukunkume shi da karfi ta saka kuka tana goga fuskarta a jikin rigarsa tana mai karra shigewa jikinsa
Chapter 81 · 0% Book details