← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 138

Sashe 109

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shuwwa ta dan yi tsam ta ce" Ya danganta, idan kamar a sutura ne haka kawai nake son saka color ash color, wasu kalolin kayan jikin Ash color ai sun hadu ne, aman kamar idan harkar cikin gida ne na fi son Golding, domin kalar ta fi jan ra'ayin mutun sosai da sosai, ash color na saurin sakawa ka tsani kwaliyar waje, ko kuma fari, fari kuwa yana sakani gajiya sosai"

Nahidt ta dago daga suyar kifin da take ta ce" Kan balaki, ni zaki saka na ji kunya? Gaskiya baki kyauta min ba Ibti, na dage nake cewa Ash color ta fi birgeki Fauzy ta ce min wai lalle idaj kuwa haka ne ta wannan fannin ban gama karantarki ba, ashe haka din ne"

IBTISAM ta dan tabe bakinta ta duka tana fadin" Na dandana? Wollah yawuna sai tsinkewa yake yi, yadda kika shafa masa jajagen percil din nan na san dandanon sai an tsinke harshe, sai dai ni ba zan taya ku aiki ba gaskiya, ke Fauzy wai me ake yi a falo?"

Nahidt ta yi murmushi ta ce" ki huta a gefe, domin Mama ta tafi da kanta yau kasuwar turaruka zata hado maki aikinki, na tabata sai kin yi juwa dan gajiya in sha Allahu, kuma gyaran gidanku ne ake yi, ni baban takaicina da ba zan yi casu ba, aman ba komai ai in sha Allahu idan bikina ya tashi da Malan dole ne mu kwaso shokiiii"

Fauzy ta dantse lebenta tana kyakyata dariya tana hanna kanta fada mata cewar a yau fa daurin aurenta bai fi saura kwana shida ba, itama Hamza ne ya fada mata ya kuma ce kar ta fada mata domin su Mama basu sanar mata ba tukunnan

A wannan ranar aka fara gyaran gidan SHUWWA, aman sai a washe gari aka gama shi domin gyra ne aka yi na mamaki , kaya ne aka zuba na yar gata

A ranar kwanan na uku biyun suka tashi da daurin kunshin da ta kwana da shi, a ranar ne kuma akai mata Alawa, aka kuma sake yi mata gyaran gashi, sannan ta wuni tana fama da shaye shayen abubuwan da iyayen ke bata, ga kuma yawan hawa saman turaren wuta da sauransu har sai da ta ji ta gaji sosai, aman kuma bata isa ta kusa ba

Zuwa yamma kunshin kafarta da na hannunta ya hudo sosai ya yi maroon sai dauakn ido yake , ya yi kyau sosai kamar ka dauke ka maido shi hannunka, ita da kanta a lokacin sai ya zamto takan yawan jin sha'awar kallon kunshin
Dare na yi kusan karfe takwas Maman Muhay da Mama sukai kiransu gaba dayansu watau ita da Nahidt

Nasiha ce sukai masu mai ratsa zuciya, har sai da suka fara tsarguwa da tsorata da nasihar domin idan Mama ta yi ta gama, sai maman Muhay ta dauka, gaba daya nasihar kuma a kan zamatakewar gidan miji ne, da yiwa miji biyaya, da dauka cewar shi aure ibada ne da sauransu a haka har suka gama kafin Maman Muhay a sanyaye ta ce" Nahidt, in sha Allahu yau saura kwana hudu a daura maki aure da malan Muhamad bisa hukuncin da iyayenki maza suka yanke, domin Dad dinku ya matso da auren y'aya matan da zai yi kwana kusa , hakan ya sa suka hade da naki "

Kai ta sada tana jin yadda gabanta ke ta dokawa daf daf daf da tarin jin abubuwa daban dake ziyartarta a wannan lokacin
Aurenta? Da Aban Shuwwa? Ya salam, idan ta kurma ihu a wajen nan me zai faru ne?

A hankali ta sake rufe bakinta dan kar ta kurma ihun, sai dai ina dariyar da ta ki boyuea ta tonata, hakan ya sa mamanta maka mata hararar da ta saka ta yi saurin gumtsewa tana mintsinin Shuwwa dake ta washe baki tana fadin" Wayo Allahna dadi zai kasheni"

Maman MUHAY ta yi yar dariya ta ce" Dadin nan kar ya kashe ki daughter, ya barmin ke da ranki"

Sai kuma ta yi kalar serius ta ce" IBTISAM, ban san yaya zan kwatanta maki ba, ban san ta inda zan fara ba, abinda na san zan iya roka a wajenki shine ki yi kokari ki gane wanene shi, IBTISAM kowa da gwaninsa a duniya, kuma ko wanene kai lalle akoy wace ke iya tankwasa lamarinka, sai dau idan baka hadu da ita ba, aman in dai ka hadu da ita to fa komai zai iya faruwa da kai, y'ata, so nake a matsayinki na matarsa ki yi kokari ki koyi zama da shi, ki iya tankwasashi, ki iya daidaita lamarinsa, ki cire tsoro ko shayinsa a ranki, ki jurewa halinsa ki kamanta zama da shi ta yadda zai ..............."
Ta dan sasauta ta dora da fadin" Ta yadda zai zama cikaken mutun, ta yadda zai zama mutun cikake Yarinyata, shi din bahagumen mutun ne wanda ni kaina nakan rasa inda ya saka gabansa, sai dai abu daya da na fahimta shine ko yaya yake yakan ja tunga a kan lamarinki, My daughter shin zaki iya yi min kokarin nan?"

Shuwwa ta kalli Mama a sanyaye, sai kuma ta kalli Mahaifiyarta

A hankali Mamanta ta.....🥺ALK'ALAMIN KADARATAH

Na

*Sajida*

Page

6️⃣2️⃣

A hankali mamanta ta dan gyada mata kai tana sake dubanta da kyau, hakan ya sa ta sada kanta tana sauke ajiyar Zuciyar da ta kwace mata,
Shin yaya suke so ta fahimtar da su cewar matse masa wajema na hadasa mata da bugawar zuciya da tunani? Yaya zata fada masu cewar shi din mutun ne mai karfin gusa tunaninta ya saka mata wasu abubuwa masu karfin gaske a cikin zuciyarta koda bata shiryawa hakan ba?

A hankali ta dan gyada masu kanta tana karra tunanin kawai sunna son sakata abinda zai hadasa mata ciwon kai ne, summa ya hadasa masu, domin a irin zaman da ta yi da mutumen nan ita kam ta cire tsamanin cewa wai zai iya daidaita lamarinsa a kanta, menene bara kamanta ba? Aman ko kallo bata ishe shi, dan wulalanci fa tafiya ce ya yi ko? Ko irin ya fada matan nan haka ya yi tafiyarsa,

Maman MUHAY ta yi murmushi tana sake kallonta da tunanin kunya ce ta sakata sada kan nan haka , dan haka ta furta" Allah ya maki albarka, Allah ya kama mana"

Da amen suka amsa, hakan ya sa ta mike tana fadin" Bara na baku waje Hajia"

Mama ta yi murmushi ta rakata da kallo har ta bar wajen kafin ta juyo ta fuskance su da kyau ta ce"Ta tafi, kina iya fadan na bakinki"

A tare suka kalli Maman, sai kuma suka kalli junna
Mama ta ce" Kin gane, ni na haife ki, na kuma san wannan sada kan ba wai na jin kunyar bane ba, sai dai abinda zan fada maki IBTISAM shine ki dauka wajibi ne a gareki gyaran aurenki, ki dauka idan kika ballo shi kika dawo da nice zaki zauna zama mai sunna zama, ki sani auren nan shine burinmu, zama a dakinki kuma shine kwonciyar hankalinki, darajarki, kimarki shine dakin aurenki kin fahimta?"

Kai ta gyada tana furzar da numfashi ta ce" Mama, bai fa damu da ni ba, du wani yi yake kamar an masa dole"

Mama ta tabe baki ta ce" Wannan shine dalilin da zaki masa dolen, shine dalilin da zaki mike ki jajirce ki masa dolen, dolen da zaki masa itace ta ya san kimarki, ya so ki, ya adanaki, babu wanda bai karanci yana kishinki ba, sai kuma ki bashi damar ya gane yana sonki, ban ce ki je masa da jiji da kai da wata takama ko wani abu makamancin haka ba, ina so ki je masa da taushi, da laushi, da tarin niimar da Allah ya maki ta kasancewa mace, ke macece kece duniyarsa, kece farin cikinsa, ke kadai kin isa idan kika yi niya ki saka ya birkice ko kuma ya shiga cikin nishadi.........a Yanzu ina so ki mayar da maganar bai damu da ke ba gefe, idan kika tabatar kun yi sabon da ya dace ki saka damuwar bai damu da ke ba a zuciyarki ma yi maganar, IBTISAM ki farauce shi, ki farauci dukan wani nutsuwarsa dan ku gudu tare , ku tsira tare"

Shuwwa ta hadiye yawu tana dan murmushin gefen baki tana ta tunanin abubuwa a cikin ranta

Mahaifiyarsu ta juya wajen Nahidt ta ce" Ke kuma daga yau ko kofar falo bana so kafarki ta fita, domin ko rakiyar kanwarki ba tare za'a je da ke in sha Allah, zan fara gyaraki!"

SHUWWA ta marairaice tana kallon mamansu ta ce" Mama, ina ina ce tare zamu je, ni kadai za'a kai gidan?"

Da mamaki baki bude mamanta ta kalleta, sannan ta kalli yayar tata
Kai ta girgiza ta saki zancen bata bata amsarta ba ta ci gaba da fadawa Nahidt cewa" daga nan har zuwa daurin aurenki kuma zaki yi hakuri da magana da shi Muhamad din, NAHIDt dole ki koyi abinda ake cewa jan aji koda baki sanshi ba, kin fahimta, dole ki iya bambance tsakaninki da wace bata san ciwon kanta ba, dan haka a yanzu ba zaku tare da kanwarki ba zan kilaceki na kula da ke ta yadda zaki je ana dokinki irin na kowace y'a mai daraja kin fahimta ko baki fahimta ba?"

Da sauri itama ta gyada kanta tana amsawa cewar ta fahimta

Mamansu ta sauke ajiyar zuciya ta sasauta muryarta sosai yanzun tama fuskantarsu da tunanin yaya zasu kwashe da wannan magana da mahaifinsu ya ce dole ita zata fada masu, wai wani itace koda sun so bata rai tana iya yi masu ihu su daidaita ta sani sarai shi sai dai su rikita shi, balle IBTISAM ba zai iya yi mata ihu ba gaskiya

Ta sake muzgutawa ta sanyayar da muryarta sosai ta shiga fadin"Yau kwana hudu kennan, da Mahaifinku ya yarda ya budi baki ya baku labarin wanene shi, asalinsa, danginsa sanadiyyar mijinki IBTISAM"

Gaba dayansu sun kamar zabura da jin wannan magana, sannan sun zaku da son jin karashen maganar, hakan ya sa ta sake aron jarumta ta sanar masu dukkan abinda ya faru , watau cewa su din jinnin sarauta me, y'aya suke ga sarkin garinsu
Chapter 109 · 0% Book details