← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 138

Sashe 114

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya girgiza mata kai yana cire kansa a kanta har ta karaso ta zauna din
Idannuwansa ya lumshe saboda kanshin turaren da ya dake shi a lokacin da zata zauna da ta dan yarfe hijab din nata ta zauna ( yar uwa, ki kula, kin ga hijab ko zani yakan baza kanshi ko warin dake tare da shi a dukan lokacin da kika gita ta gefen mutun, wani sa'in zaki ji ke da kanki wani doyi doyi bayan ke kin yi wanka, to fa ki kiyayeni ki ringa kamanta anfani da turare a jikin gyauton nan namu😌, ki dan shashafa masa sannan ki daura zani, kin ga ki turarawa kayan turare hakan zai sa ko wucewa kika yi sai dai ki bar kanshi ba dai hamami ba wollah😌, bale dan iya yi da dan kissa a gaban miji ai sai ana watsa hijab ana kwashe shi dan ya ringa dan hango mutanen zam a jiki🥺)

Sai da ya dan yi gyaran murya sannan ya ce" IBTISAM farilan sallah guda nawa ne? Kuma ke kuma sallar kwaya nawa kike yi a wuni?"

Da mamaki ta dan dakatar da muimui din da take da baki tana jan carbi ta kalle shi, kasa hanna kanta ta yi cewa" To yalabai ban gane ba kuma wata sabuwa, so ake ace bana sallah ne?"

Dan hade girar sama da ta kasa ya yi a dan kausashe ya ce" Ba wannan maganar nake so ba, zan so ki maida shiririta gefe mu yi magana ta fahimta, kin san hakinki ne a kaina daga bakin lokacin da kika baro gabam iyayenki kikaa dawo hannuna kula da tarbiyarki? Idan na ce tarbiyarki ina jam'i ne da adininki, ko ba wannan abin kunya ne ace kai katon gardi ka auri mace ka zubar ba ruwanka da bin didigin adininta, wani namijin abinda ya fi kwarewa a shi shine neman nan, yana neman har sai an danna keyarsa a cikin kabari an rufa kasa mala'iku sun zo sun tashe shi zaune ne zai gane duniya ba matabata bace, wanin zai kai macen ya zuba mata kayan more rayuwa ta yadda ita da kanta zata watsar da tunanin neman ilimi da rike adinninta, gaba dayansu ba zasu gane aun tafkawa kansu aikin dana sani ba sai sun haifa sun kumaa horar ba tarbiyar islama tun a nan gidan duniya y'ayan sun watsar da su kafin a je kiyama su tsaya a gaban Allah abin kunya da aikin dana sani ya yiwa kansu girman da zasu kasa dauka, so zan so ki fuskanceni ki bani amsoshin kadan din da nake son sani kafin na san da wa nake zaune kin fahimta?"

Kashhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh, yana bambanmin nan ne Shuwwa ta auka a duniyar mamakin da ta ayana a ranta kamar haka' Lahaula wala kuwata ila bilah, dama soja yana da adinni? Kai wannan gayen kasheni yake son yi walahi, ga girma, ga girman murya, ga yayan banki, ga iyaa tsotsat lebe uwa uba ga adinni.............. Wo katona.......'

Sai da ya sake dubanta ya yi wata gyaran muryar gannin ta yi kimmm tana kallonsa kuma tana jan carbin nan ya kai hannunsa ya janye carbin a yatsarta yana fadin" Da kuma irin jan carbin nan na munafurci, ka ce ka ja adadin wanda ya nuna maka bayan ba'a haliceka da irin wannan iyawar ba, ba'a gudu da sosa duwawu ki bani amsoshina , shin zaki iya"

Yawun ta hadiye ta sakar masa murmushin kauna, ita fa ta sani ne soyayarsa wajibi ce ga yan mata sai dai wadda Allah ya kare kawai
Kai ta gyada masa har kamar sau hudu har sai da ya dan karra kureta da kallo sai kuma ya basar ya ce" *FARILAN SALLAH GUDA NAWA NE?* "

Kallonshi tayi da fari sai kuma ta sauke dubanta k'asa tace" Niyyar sallah, kabbarar harama, tsayuwa a kanta, karanta fatiha da kuma tsayawa a cikinta, ruku'i da d'agowa ma farilla ne na sallah, yin sujada akan goshi da d'agowa daga sujadar, da jeranta farillan, zaman tahiya da yin sallama, a wajen maza wasu abubuwan kan k'aru saboda su suna bin jam'i ne a masallaci ma'ana suna biyar limami..."

Sosai ya yi mamakin amsar da ta bashi, hakan ya sa ya dora da yi mata yan tambayoyin dake kusa, ba dan komai ba sai dan ya gamsu da yannayin ibadarta, ya ce" *FARILAN ALWALLAH GUDA NAWA NE ?* "

Ba alamar wasa a tare da ita ta shiga motsa bakinta a hankali tace" Farillan alwala Guda bakwai ne niyya, wanke fuska, wanke hannaye zuwa gwiwar hannu, shafar kai da kuma wanke k'afafu zuwa ijiyar sau, sannan da cud'awa da kuma gaggautawa."

Ya sauke ajiyar zuciya ya dora da fadin " *YAYA KIKE YIN TSARKI NE?, DOMIN AI KIN SAN CEWA BABU ABINDA KE SAKA BAWA A UKU IRIN TSARKI, ZAI YI TA YIN IBADA NE SAI YA JE YA TARDA BA LODI, TSARKI IDAN BAI YI BA BABU SALLAH* "

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike ta nemi kwaye hijab din nata tana kokarin dukawa

Da sauri ya zarro idannuwansa yama fadin" Ebtisemmmmmmmm me, me zaki yi?"

Kwabe fuska ta yi ta ce" To ba kace yaya nake yin tsarki ba?, Shine zan nuna maka yadda nake yi"

Kansa ya girgiza yana fadin" Ba zai fadu bane sai kin nuna min?"

San tsai ta yi ta koma tana fadin" Har na ji wani iri nima, to shi dai tsarki yadda nake yinsa shi ne na kan tanadi ruwa mai tsarki da tsarkakewa, zan fara d'aura niyyar wankan tsarki sannan na fara kama ruwa, ba wai kama ruwa kamar kowane ba, zan dinga zuwa ruwa ne a gabana daga cibiya har zuwa bakin gwowoyina, zan tabbatar na wanke da kyau sannan na wanke hannayena da sabulu ko kuma k'asa, idan na wanke da kyau sai na fara d'aura alwala kamar yanda nake alwala ta sallah, zan yi hakane har sai na zo shafar kai a nan saina zuba ruwa sos1i a kai na na wanke yanda kowane silin gashina zai samu ruwa, idan na kammala saina k'walk'wale kunnuwa sannan zuba ruwa a b'aren jikina na dama na wanke da kyau sannan na wanke b'aren hagu daga sama har k'asa, idan na kammala sai na wanke k'afafu daga bakin ijiyar sahu, da haka wankana ya kammala, wannan shine cikakken wanka wanda aka koya daga wajen annabi, amma kuma akwai wani wankan wanda shi ma malamai sun ce idan ka yi shi yayi saidai ba kamilallen wanka bane, domin kuwa waccen d'in mai alwala idan ka fito daga yin shi zaka iya kabarta sallah idan lokacinta yayi shi kuma waccen baya da alwala dan haka ba za ka iya sallah da shi ba har sai ka yi alwala.

Kansa yake dan jinjinawa na gamsuwa da amsoshinta ya ce" Yaya kike yin wankan HAILA?"

Wani kallo ta masa wanda shi a ya sadda kanshi ya had'e fuska da tunanin ba za ta gane ba, dan kuwa ai wankan tsarkin da ta fad'a masa duk d'aya ne da na *haikar, gawa, wankan shiga musulunci, da kuma na saduwa da ma wankan jego*, niyya ce kawai ta bambamta, dan haka ta d'an juya bakinta tace "Duk d'aya ne, niyya ce ta bambamta."

Wani kallo ya aika mata yana k'ank'ance idonsa kamar mai tsoron fito da abinda ke bakinsa yace "Haka kike yin wanka JANABA?"

fisabililahi ba wai tambayyar ce ta zo mata a rashin sanni ba, yadda ya yi mata tambayar ne ta ji wani iri, kamar wace ta saba yin wankan janabar kulun?, Sai dai bata da yadda zata yi, a hankali ta ce" E, haka na ke yi..."

Dukan amshohin da take bashi babu wace ta koja masa rai irin wannan, yadda take yin wankan janaba, irin ita gata mai yin wankan janaba? Me yasa yarinyar nan ke wukakantashi ne? Me yasa take yi masa abinda ba daidai ba?

Ruwaan dake ajiye gefe ya dauka ya kuskure bakinsa ya mika mata yanaa fadin" Ki kurkure bakinki mu yi sallah idan kina da alwallah"

Kikifta ido take tana kallonsa da tunanin shi haka lamarinsa yake yanzu mutun yanzu ba mutun ba, fuskar ta cika kukukub kamar an wanka masa mari, ko me ya tuna ya bata masa rai ne? To sallarma wai ta mecece za'a yi ne?
Bakinta ta tabe gannin bai nuna alamun yana son magana ba, itama sai ta ari lamari irin na basarwa, lamari irin na kamun kai, watau ta wani cicije ta kuskure bakin nata ta koma bayansa tana shinfida dardumar dake ajiye gefe tana cicijewa
Duka yana tsaye ne yana kallonta har ta gama basarwar ta tsaya tana sasada kai

Bakinsa ya tabe ya shiga yin kiran sallar a hankali har ya gama
Yan sekwani tsakani ya tada sallar inda ta shiga binsa a nutse har suka yi suka gama
Bayan zaman tahiya da adu'o'i ya juyo a hankali ya dora hannunsa na dama a saman kanta a bayane sannan a nutse ya shiga karanta adu'a kamar haka" *Allahumma inni as'aluka khairuha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a'uzubika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi.*"

Watau har ya yi ya gama kanta a sade yake duk kuma wajen da ya nemi alkhairinta , ya kuma nemi da Allah ya kare shi da duk wani shari dake tare da ita a zuciyarta fadi take ' *NIMA HAKA ALLAH, NIMA HAKA* ' Har ya gama ya shafa fatiha yana kallonta ya ce" IBTISAM dauko abincin cen mu ci"

Wajen da ya nuna ta kalla, gannin manyan ledoji farare ya sakata kallonsa tana fadin" Abinci kuma? Na fa yi girki me ya hadaka da siyan abincin titi?"

Sai ya ji ya ji dadi da ta ce ta fa yi girkin, da kuma nuna masa da ta yi darajarsa ta wuce ya siyi na titi, gakan ya sa a dan sanyaye ya ce" Dama kaji ne na gani a gashe sai na siyo "

Dan tsam ta yi tana mikewa ta ce" ai su gaskiya rashin cinsuma hadari ne, su fa da ka gansu a soye ko suna tsuwat tsuwat abin sha'awa ne da su , shi yasa cinsuma alkairi ne, Allah ya sa sun gasu"
Chapter 114 · 0% Book details