← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 138

Sashe 90

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta dan yafitota, Hakan ya sa ta rarafa ta karasa kusa da ita sosai tana kallonta

Mama ta ce" Baki yi barci ba?, Ina fatan lafiya?"

Shuwwa ta sauke ajiyar Zuciya a hankali ta ce" Mama fada mukai da Nahidt din", ta fadi haka ne dan bata san me zata ce ba, gashi so take ta jima tare da maman, haka kawai take ji a ranta koda bai ce ta lekota ba tana iya kulawa da matar da ta ji tarihinsu ta kuma tausaya masu

Mama ta yi dan kurmushi da shakakiyar muryarta ta ce" Kin sha maganinki kuwa yau?"

Shuwwa ta dan girgiza kanta , domin yau bata sha tsumin nan ba ko diz

Mama ta dan shafa gefen fuskarta ta ce" Maza tashi ki ciro a frij ki sha sai ki kwonta saman gadona"

Shuwwa ta gyada kanta, ta mike ta aiwatar yadda Maman ta ce, duda tana tunanin anya zata iya kwonciya saman gadon kai tsaye haka?, Sai kawia ta jure ta zauna a baki baki tana fadin" mama yaushe zaki kwonta?"

Mama ta sauke ajiyar zuciya a hankali ta ce" zan kwonta y'ata in sha Allah"

Daga haka Shuwwa ta yi shiru bata kuma cewa komai ba, aman kuma tana kallon Maman ne dake ta adu'a da carbinta har dare ya tsala sosai, sannan Maman kan juyo lokaci zuwa lokaci ta kalleta, gannin a zaune take ya saka ta mike ta sake daidaita alarm dan ta tashi daukan azumi ta je wajen gadon tana fadin" Oya haye cen kurya kar aje ki fado tsakiyar dare, ko bakya gigin barci?"

Shuwwa ta yi yar dariya ta haye cen saman ta ja bargo ta rufa tana jin maman ta gama kimtsawa ta hau gadon itama ta kwonta hadi da rike carbinta tana ci gaba da ja.......
Ai kam jin mutun a kusanta ya dan rage mata tunanin, uwa uba ga maganin matsala a hannunta watau carbi, tana tsaka da ja barci barawo yayi awon gaba da ita, zuciyarta sakayau ba nauyi ba komai............ta riga ta fadawa mai magani, ya kuma sanyayar mata da zuciyarta........☺️
_____________________________________

Fitsarin da ta tsilala ya jike mata sket dinta jirgif take dan matsa kafarta a ciki, jikinta na rawa tana satar kallonsa

Tunda ya fito mata kwada kwada cewar shin ita ke neman rayuwar d'ansa ? Ya sakata jin kamar zata summa a zaunen da take , harma ta saki fitsari tana mai gannin mutuwarta a gaban idannuwanta

Jikinta na rawa ta budi baki ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 5️⃣2️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Jikinta na rawa ta budi baki ta ce" Sir, na rantse da girman Allah ba ni din ce kai tsaye ke neman ransa ba"

Da karfi ya ce" Ke saurara min, ke mahaukaciyar ina ce da zaki bani amsa irin ta mashaya? Ki fito min a mutun ki min maganar da hankalina zai iya dauka ba shirme ba, idan bakinki ya kuma firtan shirme zan maki aiki irin na shirme, me ya maki? Me ya tare maki?"

"Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, wallahi, wallahi walahi ban san kan zancen ba, kira nake samu da muryar namiji ana ce min idan ban yi biyaya na zuba masa guba ba ni za'a kashe, aka ce in dai shine ba zai taba sona ba ina kallo zai so watana, ba nice ta farko ba , ba zan taba zama ta karshe ba, saima ya lalatan rayuwa ya yi watsi da ni, tun washe garin na tare a gidan nan aka fara yi min haka Aba......." Ta fada tana sake fashew da kuka tana kallon bindigar da ya ajiye saman table kafin ya mata tambayar da yi nara nunin yana iya harbeta a kan maganar nan

Kasancewar dama ya shaki bacin rai ne na matar da yake so, wace bai taba tunanin zai so wata bayan wace ya yiwa soyayar saurayi da budurwa ba, ya fito ya kuma ganninta tana masu labe sai ya hauhawa tamkar fulawa

A kausashe ya ce" Laben da kike yi mana na menene?"

Jikinta na wani rawar ta ce" tun jiya na bar maganar saka masa wani abin a abincinsa Aba, kwana biyu na ga yana fita da wannan bakuwar ne , shine yau ya dawo shi kadai da hajia, shine na je dan na ji ko ya saketa ne?"

Hannunsa yake murzawa yana sake nazartarta da son gane gaskiyar lamarin

A kausashe ya ce" Da wace waya suke kiranki? A ina wayar take?"

Da sauri ta ce" wayar na dakina, da ita ce suke kirana tana saman gadona, tun jiya da na yarda ita na kasheta ban waiwayeta ba"

Da sauri ya mike ya saka daya daga cikin yaransa na amana gadinta ya fito da dan sauri ya nufi dakin, a nan ne ya ga su MUHAY na meeting shi da mutanensa ya tsatsaresu

Da dan mamaki MUhay ya raka shi da kallo gannin yadda yake sauri ya kuma nufi cen bangaren matan gidan

A hankali ya dan girgiza kansa sai kuma ya samu kansa da salamarsu ya koma ya tsaya a hanyar da zai dawo ya wuce

CHIEF OF ARMY na dawowa ya ganshi a nan a tsaye , hakan ya saka shi dubansa har jijiyoyin hannayensa na bali na abinda ke damunsa

Rai bace ya ce"ba dai zaka fada min munafukin dake min zagon kasa a cikin gida ba ko? In sha Allah a yau sai na gane ko waye, kuma da hannuna zan harbe shi da bindigata domin barinsa a doron kasama hadari ne, yana iya daukan rai ba tare da jin kunya ko tsoron Allah ba! Yarinyar nan da ya hada baki da ita ya dauke wayarta da ta bari a dakinta, bai san cewa ya fada a rami ne da kansa ba, na saka cctv tun ranar da mukai maganar nan da kai, kuma a yanzu yanzu zan ga ko waye in sha Allah a yau ba zai kwana lafiya ba"

Da ido yake kallonsa har ya dasa aya kafin ya ce" Aman Dad, yanzu ka gama cewa matarka bincike bashi da dadi, natacen bincike kan haifar da mumunan amsa mai firgitarwa, shin ba zaka yi hakuri har lokacin da na daukar ma mai aikatar ya cika ba?"

A hankali Chief of army ya ce" Yaya zaka min kamawa da abinda yake damuna ne Son?"

A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Dad, a Yanzu zan iya cewa hankalina ya kwonta sosai, da Mama ta ji maganar nan hankakina ya kwonta father, dana shi ya fi damuna fiye da komai fa, tunda har ta ji, ta kuma dauki abun da sauki, sauran du mai sauki ne In sha Allah"

A hankali ya ce" Kana nufin ta hakura da rigimar ne?"

Dan murmushi ya yi dan sarai ya san rikicewar Aban nasa harda fushin mamansa ya karra rura shi, hakan ya sa ya ce" Harma ta kwonta barci Aba"

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi yana sada kansa hadi da girgiza kan nasa

A sanyaye ya ce" Idan mai neman ranka ya fito daga cikin gidana, ban san in har zan iya yi masa hukunci bisa tsarin yadda hukuncinsa zai kama, ina tsoron ko wanene na fara halaka shi da hannuna Son"

Hannayensa ya dan rungume yana kallonsa ya ce" Shima zamu yi masa uzuri ne Abanah, domin ta yiwu nine na ja har ya yi min irin tsanar nan, koma babu abinda na yi masa dole zamu yi masa uzuri in sha Allah"

Chief of army dai sauraronsa yake yi har ya gama sannan ya girgiza kansa ya ce" Yaya matsayin auren yarinyar nan dake kanka? Wannan karron nine ba zan iya yarda ka zauna da macen dake iya yarda ta hada kai da wani dan a kasheka ba, bata da huja koda kuwa yankan namanta kake yi kulun!"

MUHAY ya ce" Dad, na saketa a ranar da na sake bata dama dan na ga ko zata iya jurewa ta ki sake waiwayarsu? Sai dai da kanta ta waiwayesu harma ta amshi maganin ta zuba min a abinci, sani ne basu yi ba gaba dayansu, a tunaninsu motsina suka sani idan na fito waje, basu san cewa ni wanda suke tare da shi ne a tafin hannuna Dad............basu fa da hanyar kubuta bayin Allahn nan, baban abinda ya batan rai har na nufo gida dakin yarinyar cen suka saka camera, kennan har mutuncin iyalina zasu fara shiga? Wannan shine na kasa jurewa Father......... i can't!"

CHIEF OF ARMY ya tsatsareshi da ido sosai yana kallonsa, kafin ya sauke dan murmushi yana dafa gefen kafadarsa ya ce" Alhmdulilah "
Daga haka ya yi gaba ya barshi yana tunanin dariyar kuwa ko ta mecece dad dinsa ya yi?

Tun daga wannan rana abubuwa suka cenza sosai a cikin gidan Chief of army
Chapter 90 · 0% Book details