← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 138

Sashe 53

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Yunk'urawa yayi zai mik'e da wani mugun sauri Shuwwa ta rigashi mik'ewa, d'aurin k'irjin da tayi ne ya warware hakan yasa da sauri a rikice ta dafe k'irjin, a tunaninta sake shak'o wuyanta zai yi, dan haka ta juya da gudu ta shiga haurawa sama har tana juyawa dan ta ga wai shin ya biyota ne ko kuma ya ya ya.

Mahuydeen dake tsaye yana bin ta da kallo da fari mamaki ne ta bashi, amma da ya ga tsakaninta da Allah gudun ceton rai ne take da mugun tsoron nan, yanda take taka matakalar da mugun gudu ba ta ko tsoron ta kifo k'asa, yanda take rik'e da zanin a hannunta ga d'uwawunta dake ta gudun su ma daga cikin zanen duk da ba d'auri ne ta masa da ya fito da surarta ba.

Me zai yi in ba dariya ba? Haka kawai ya ji dariya ta sakosa a gaba dalilin mahaukaciyar yarinyar nan, abinda ya jima bai yi ba sai gashi har da neman k'yak'yatawa yake.

Lokaci d'aya kuma sai ya yi gum da bakinshi kamar dama dole aka saka shi dariyar, wani basaraken murmushi ya saki yanzun tare da jinjina kai a zuciyarshi ya ayyana "Haka ya kamata ki kasance kina gudun fanfalak'i idan kin ganni."

A hankalce ya juya dan zuwa aiwatar da abin da ya fito da shi, sai dai a jikinshi yake ji ko ya kwanta yanzun na zai samu bacci ba saboda makirar yarinyar can, dan in dai ran shi a b'ace yake baya iya samun bacci, duk da ma dai ya d'an samu nishad'i tunda har ya yi dariya, amma hakan ba yana nufin zai samu bacci ba ne yanzun

_________________________________

Kamar jiya, yauma haka suka wuni sunna aiki, yau aikin yaa sha bamban da na jiya domin daidai da girkin ba an dafa ci idan ka yi niya bane, an dafa da ka kaleni zaka soni ne, watau irin girkin nan da zarar mutun ya kalla zai ji sha'awar ci ko yayane, hakan ya saka Shuwwa shiga a cikin takaicin aikin da Nahidt ta dage suke yi har sai da ran Nahidt din ya baci da gannin tana aiki ba kaza kaza ta ce" Ke wai me haka yake nufi ne? Aikin uban gidanki kike yi a haka ne? Yuaushe kika koma yin aiki da munafurci ne?"

Shuwwar ta dakata tana cire safar hannunta da ta saka take faman aiki a kusa da tukwane ta dauki tissu ta share dan gumin da ta tarra tana kallon kicin din da tunanin wai ina hanyar da iska ke dan fita ko shigowa ta dubi auntynta ta ce" Mah, wahala ce fa muke yi, domin a tsamtsamce yake da abinda zai kai bakinsa"

Da dan mamaki take kallonta ta ce" A tsamtsamce kika ce?, Yaya aka yi kika sani?"

Shuwwa ta watsa hannayenta tana kallon yamboll din da NAHIDT ta sakata dakawa dan fitina ta ce" domin jiyama na yi girki a gidan nan, kuma bai taba komai ba, daidai da liptona dinsa sai da ya tarda ni dakina ya sakani sha sannan ya tafi da shi, na tabata ritsani ya yi dan ya ga idan zan iya sha ne ko me........, Ina tsoron ko yana tare da tsoron cin abincin kowa a rayuwarsa "

Nahidt ta dan kura mata ido na dan lokaci sai kuma ta saka yar dariya tana fadin" Kin san me ya fado min a rai? Marin da kika sha a lokacin da kika ajiye abincin Rislane ya zo taba maki nono kika kiya uwarsa ji take abincin ne kika ki ci ta wanka maki mari, kai a ranar kin daku shuwwa"

Shuwarma ta saka yar dariya tana zarro idannuwanta ta nunota da hannunta ta ce" Kema ai kin dakun kin manta da kika cewa uwar jaka kema ta wanka maki mari? Aman mun masu tsiya kai da bamu bato saudiya ba sanadiyar kayar da uwar nan da muka yi da sai an yanke mana kai a tsakiyar gari dan a kiyaye gaba"

Yar dariyar raha suka yi tuna ranar da sukai gudun ceton rai,
Daga bisani Nahidt ta dubeta da kyau ta ce" ribar aikatau din da muka yi menene Shuwwa?"

Shuwwar dake zaune saman yar karamar kujera ta dan sake kura mata ido tana kallonta aman ta ki ta ce da ita komai, hakan ya sa ta sake sakin murmushi ta ce" Ribarsa shine, naci wa farin cikin uban gidanmu, girkawa ba tare da tunanin za'a taba ko dan tsakure ba, girki da soyayar abinda muke dafawa...........Shuwwa karasa min mana?"

Shuwwar ta lumshe idannuwanta tana tuna rayuwarsu a sanyaye ta ce" naci da maimaici a kan lokaci, tsafta da kwanoni masu fuzgar maganadisun kwalon idannu, kula, hankalta da yannayin wanda ya ajiyemu, shi abu mai daraja shi yake janyowa kansa daraja ne"

Dan murmushi Nahidt ta yi a sanyaye ta ce" Ba lallene ace dan ya ki ci ko dan ya saka ki sha yana tare da tsatsamcin cin abinci, ta yiwu damuwarsa ta tsafta ce, ta yiwu a matsayinsa na baba ba lallene kai tsaye ya aminta da girkin macen da ta shigo da niyar zaman aure da shi ba, dole yana da bukatar yarda da ita, yana da bukatar gane hannunta, idan har ya sha Lipton dinki na jiya zan iya ce maki yana da kyautata zato a gareki, ko kuma akoy abinda ya tabatar masa cewa har yanzu baki fara kauce hanyar da zaki nemi ransa ba, Shuwwa yaya aurenku ya kasance? Kai tsaye fa aka sarka ku, me yasa aka maku irin sarkawar nan? Wanda ya sarka din shine barazana wa nutsuwar d'ansa? Ko kuma ke din nan kece barazana wa tunaninsa?"

Shuwwa dake mayar da safunnan hannayenta ta juya wajen aikinta a hankali ta ce" Nama fi zargin cewa kamar nice barazana wa nutsuwarasa, domin na kula da kallo irin na kiyaye , irin na gociya, ko nace irin na tsatsani da mutun din nan da yake min da zarar na matse masa waje
Tabas , na shi tunani a kan sake saken matayensa, sai na ji ina so na san a kan wani dalili yake sakinsu shi kuma? Ba wai dan ni na zauna da shi ba, lalallaa nakan yi sha'awar talafawa mutun , bale shi din nan kin san kama da me yake min?"

NAHIDT ta girgiza kai tana kallonta

SHUWWA ta ce" kama yake min da dan jariri irin lukutayen nan mararsa hakurin nan......, Oh my god idan ya harzuka wollah hanyar da zan shige nake nema"

Nahidt ta kilkile da dariya tana nunota da yatsa ta ce" Nice kat, du iskancinki SHUWWA na ga an riko damatsunnanki sai na koma na rufe daki na shiga tayaki da adu'ar kar ya karya ki, kai aman Shuwwa mijinta duniya ne, kin ga damatsunnan kuwa?"

SHUWWAR ta yatsina baki ta ki ta baya amsa domin ita abinda Nahidt ke fadi din ta gama ganota dan ta saka mata ra'ayin mutumen nan ne, so take ta sakata ta kamu da soyayar mutumen da shi da kansa ba wani son kansa yake yi ba?, Yaya zasu kwasheta kennan? Ta katashe rayuwarta a birkice ko?

Nahidt ta shiga ciro manyan kuloli tana son zaban wa'inda zasu zuba abincin tana fadin" Ki iyakance kowace yar aiki da kama maki girki, wannan aikin bai kai rabin wanda kike yi kika saba yi ba, kar ki dorawa kanki cewar sai kin yi abinci kala uku, biyu, ko hudu, ki gyara takardar girkinki ki ringa yin daya kwakwaran da idan aka ci an san an ci girki mai dandano, ki sani ko LIEUTENANT GANARAL ne shi, yana so ya ringa gannin ana tatala masa, namiji na so ya ga an san ciwonsa, ba kawai da ya bude a kwashe a zubar ba, na fi ganewa ki ringa yin kalolin juss kina shake frij dinki da su , da dan abin marmari su cak ne, su biscui ne, su soye soyenmu na mata ne masu dandano kina ajiye as idan an gama cin mai nauyi a dan yi kallin TV ana dan lalube lalube ana dan tsakura, harkar zata fi tafiya daidai!"

SHUWWA ta dafe kanta ta juyo tana kallonta, a hankali ta furta" Ba sauki a lamuranki NAHIDT sai na Allah"

Da haka suka yi aikace aikacensu, sunna yi Shuwwar na leka yan falo, tana gamsuwa da aikinsu, sunna gamawa ta salame su ta koma wajen yar uwarta suka yi komai suka gama

Babu yadda SHUWWAR bata yi ba kan Nahidt ta bita dakinta su shirya ta ce ba da ita ba, ta mata rakiyar amarya daga shi idan ta ganta a dakinta to fa haihuwa ta yi,
Wannan takaicin ta shaka ta yi tafiyarta ciki ba tare da ta tankata ba domin ta kula so take su raba hali ne
Kafin ta je nata dakin sai da ta fara shiga nasa ta sake tatare gajeran wandonsa tana fadin" sangarta bata da kyau, kai ba zakana boye dan ciki ba salon a dauka ka nuna kamar an ganka a zirrr ne? To Allah ya taroka soja!"
Chapter 53 · 0% Book details