← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 138

Sashe 54

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ta yi wankanta, da su shiga ruwan dumi da zama, da su anfani da ruwan wanka, da komai da komai sannan ta fito ta shiga mulke jikinta da hadin humurarta mai mai a ciki wada suka hada suka raba gida uku su uku
A nutse ta ciro bra da pant a cikin saitin kayan mijinta na biyu tana kallon su domin shi dan kasuwa ne dake odern kaya waje yan kasuwa na siya a wajensa, hakan ya sa ya ringa lodo mata yan kasa da kasa masu daraja da kyau da tsari,
Dan murmushi ta yi tana ciro doguwar gown a cikin akwatin dogayen rigunanta mai ruwan ash da duwatsu a gaban
Dora su ta yi saman turaren wutar da ta zuba ta ci gaba da gyaran jikinta zuwa gashin kanta
Sai da ta gama sannan ta shirya ta dauki san kwalin da yar siririyar agogonta ta daura a hannunta ta nufi waje a nutse ta sauko kasa a lokacin karfe takwas na dare ne hakan ya sa tana idasa saukowa ta shiga neman Nahidt, aman bata ganta ba

Ta juya da niyar nufar dakinta aka bude falon aka shigo
Shirun da ya dauki wajen bayan ta rintse idannuwanta gammm tana tuna yadda suka rabu dazun sannan tana jin kamar kallonta ake yi ya sakata juyowa a hankali gabanta na dan dokawa sukai ido hudu da junna

A tsaye yake kikam ya cire hular dake kansa, sansanyan kanshin falon da tsaftarsa sun kara haifar masa da lumshe idannuwa a kan yinwar da ta ciyo shi wadda ya dawo da ita daga office ga kuma gajiya
Yawun bakinta ta hadiye da kyar tana cire idannuwanta a kansa a kasan zuciyarta tana fadin' idan kika yarda kika ringa guduwa da zarar kin ganshi kin shiga uku, zaku kula saka ne ta yadda zai zamto tautau da kuda ke da shi, ke maza je ta gabansa nuna masa kema fa jaruma ce!'

Kirjinta na dokawa da komai ta ringa taka kafafuwanta masu dauke da jan lalle ta wuce da sando tana dauke numfashi ta nufi wajen diner
Ta tabata bashi da kunyar kallo ita kuma tana son isar masa da wani sako ta haka, hakan ya sa a hankali ta bude kular abincin da suka dafa a sanyaye ta ciro cokali ta saka cikin abincin dake wasar wasar ta juya alamun cakudewa take yi sannan ta dauki guda ta dan juyo irin idan kana son yiwa yaro rowar nan ta ciro harshenta mai laushi da color din jarirai ta lashe lebenta na sama kadan ta karashe da cije na kasan gefe guda, sannan ta kanne ido daya tana kallon gefe kadan aman face dinta gaba daya a barinsa take wace ta tabata in dai yana tsayen har yanzu to fa ita yake kallo ko dan ya samu na cin zalin!
A hankali ta saka yambos din a bakinta ta datsa ta gutsura ta lumshe idannuwanta daga cikin makogwaronta ta shiga dan gurnanin fadin" Ummmmmmmmmmmmmmm,awnnnnnnnnn,ayneeeeeeeeeeeeee so, so , so dadiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiihhhhhhhhhhhhhhhhhhhhu i swear😌😌😌😌😌😌"

Idannuwansa ya cire da sauri daga kanta ya juya ya shiga haurawa da uku uku yana wani irin saurin da ya sakata bin bayansa da kallo

Ajiyar Zuciya ce ta kwace mata a hankali ta ajiye ta sha ruwa ta rufe ta juya ta nufi dakin yayarta jikinta tamkar an zare mata lakah

Dakin ta kama ta murda ta shige, tana shiga ta hangota saman salaya tana jan carbi, saman makeken bed dinta kuwa wayarta sai harke take da alama kiranta ake yi

Wajen wayar ta nufa tana karra karewa dakin kallo da mamakin tsaruwarsa da dankareren bed din dake cikinsa

Wayar ta dauko tana dubawa
Gannin Aban shuwwa ya sakata dan yin tsam kafin ta daga ta koma saman kujerar dake kusa da Nahidt din ta amsa salamarsa a nutse ta furta" Abana barka da dare"

Da sauri NAHIDT ta ringa idasa jan carbinta ta daga hannu bata yo roko ba ta ce" Allaah ka gyara komai Alalh fatiha" ta taso da sauri ta zauna kusa da Shuwwar tana kallon wayar

A nutse ya ce" Y'ar gidan Aba ,ina yayar taki take ne?"

Nahidt ta mata nunin cewa ta ce bata nan
Shuwwar ta tabe baki ta ce" Abana ta ce na ce bata nan"

Nahidt ta zarro ido tana kallonta, shi kuma ya yi dan murmushi yana fadin" Yanzu Nahi abinda kika yi hankali ne ko aikin da ba na hankali bane tarewa a gidan kanwarki?"

Nahidt ta tabe baki a sanyaye ta ce" Ai dama na san haka zaka ce, shi yasa da na zo na tambayi mijin wai idan na kwana a nan za'a ce na yi aikin hauka ne?, Sai yace min wannan shirmen hausawa ne harma ya bani takardar da ko dare na yi ni yar gida ce ba bakuwa ba, Alhmdulilah da kanwata a gari ba zan ringa rabe rabe ba, ko ka ake na je gidan Malan mai matar so?"

Malan ya yi shiru a hankali ya ce" Amshi wayar "
Wayar ta kalla ta kalli Shuwwar, ta amsa ta mike hakan ya sa Shuwwar dirowa tana zuwa ta karra kunnenta tana sauraro

A hankali ya ce" Kin amsa?"

Ta tabe baki ta ce" eh na amsa"

"NAHIDT, tsakani da Allah da annabi yanzun menene a cikin nan na bacin ran da zai saka ki yi tafiyarki mu yi ta nema? Yayanki gayanan bai koma gidansa ba shi da matarsa har yanzun so suke su ji daga gareki domin ya je barikin an hannashi shiga ai basu sanshi ba, Nahidt menene a ciki dan Furera ta amshi wayata? Kema kin san ba zan kyaleta ba bayan magangannun da ta fada ai ba kyau "

Nahidt ta yatsina bakinta ta ce" Ka ga dai kawai idan dan ka ce wannan ne ka kashe, meye zaka ce mata da ya wuce ka lalasheta an kira mata miji tsakiyar dare ko? Wai nice karuwa? Malan na taba nuna maka hali ne fisabililahi ?"

Kallonsa ya kai kan Hamza dake zaune yana sauraro, tsam ya mike ya fice a dakin hakan ya saka Hamza yin murmushi yana girgiza kansa kasa kasa ya furta" Allah na gode maka, Allah ka yafewa marainiyarka"

Malan na fita ya ce" Ke, idan kina magana ki daina irin wannan da ni na fada maki, kuma da kika ce haka ni da na san lafiyarki kalau ai ba zan daga ba, ai ba adalci bane da ace y'ata ce ta kireni tsakiyar dare sai na daga kaina tsaye ,aman ke kin san mata da shirme da hade hade ko? Ta ga damar ta yi mana wata fasarar daban ko? NAHIDT to yaya kike so na yi akoy fa haki a ciki wanda Allah ke iya kamani da shi a bayane ke kin sani ko?"

Nahidt ta ce" kar ka damu , ka yi hakuri ni bama zan kuma kiranka ba"

Malan ya yi dan tsai a hankali ya ce" Ni ai zan kireki kulun kulun "

NAHIDT ta ce" Bana so Muhamad, bana so dan Allah"

Malan ya ce" Nahidt ni ina so, kuma babu yadda na iya sai na yi, dan Allah Nahidt na tambayeki mana?

Nahidt ta gyada kanta bata ce komai ba domin jikinta gaba daya ya mutu murus ne sai Shuwwar ce ta ce" Um"

Ya ce" Dan Allah da kika fito daga gidan yayan ina kika je? Daga cen kika je ina?"

Nahidt ta bude idannuwanta ta sauke a kan fuskar Shuwwar da itama ita take kallo, a sanyaye ta ce" Daga cen gidan Shuwwa na zo Muhammad"

Ajiyar zuciyar da harta Shuwwar sai da ta ji ce ya sauke a sanyaye ya furta" Allah ya miki albarka, ya karra kiyayeki da ke da kuluhin musulmi"

Kasa amsawa ta yi, domin ta gane samun relief dinsa na jin bata je yawon banza bane, gaba daya sai ta ji gwuiwoyinta sun mata nauyi, hakan ya sa ta lumshe idannuwanta tana sauraronsa a hankali ya ce" Ki dawo kusa da ni "

SHUWWAR ta zarro Idannuwanta tana kallon yayar tata, sannan ta maida dubanta wajen wayar da sauri ta saka hannunta ta katse kiran kafin ta fasa ihun da ya zo mata tana kallin Nahidt ta ce" Tun yaushe, tun yaushe aka fara irin haka da ubana ake son munafurtata, a fasara min tun yaushe ?"

Nahidt ta lumshe idannuwanta hawayen dake ciki suka samu damar zuba a hankali ta rungume jikin Shuwwa muryarta na rawa ta ce" Shuwwa?"

Shuwwar ta lumshe nata idannuwan itama tana sauraronta
Nahidt ta ce" Shuwwa babu abinda kike tunani, babu ko daya shuwa, wulakanci ne irin na Abanki shuwa, so yake ya idasa kasara min dukan wani kuzarina Shuwwa bayan ya san shi bai nuna haka ba, hasalima ba zaya iya ba, shuwwa na shiga uku na cuci rayuwata....." Ta fashe da kukan da ya saka shuwwa lumshe idannuwanta tana dan taping din bayanta a hankali ta jata kusan gado ta zaunar da ita
Kasa ta Duka saman kafafuwanta ta dora kanta a saman cinyarta tana lumshe idannuwanta ta ce" Astagfrullah wa atubu ilaik, Astgfrullah wa atubu alaiki"...........

Nahidt ta lumshe idannuwanta tana dora hannunta saman na Shuwwar din bata iya cea komai ba

A hankaki Shuwwar ta ce" Kin yi laifi, Domin ba zan ce maki mema kika yi ba bayan kin aikata laifi mai muni a wajen ubangijinki, sasaucina daya ne kina son gyarawa, kuma Allah kuwa gafurun rahim ne ai , Nahidt ki so shi idan kina son Abana, ki so abinki Nahidt, Abana mutun ne mai daraja, mau mutunci Nahidt ke kin san uban marayu ne, a kalaman Abana na gane yana cikin halin muradinki yana shayin furta maki, Nahidt ki karra matse masa lamba har ya fada da kansa sannan ya wahalta kafin ya samu....."

"Shuwwa matansa?, Anguwarsa?, Mutanen dake zagaye da shi? " Nahidt ta fada muryarta na rawa rawa

Shuwwa ta ce" Mu hada su da Allah, wanda yai mana gori shi da Allah, wanda ya zagemu dan kadararmu shi da Allah, wanda kuma ya ce a fili zai yi fito na fito wannanma dan ka kare kanka ai ba laifi, bana tunanin Furera zata kayar maki da gaba, aunty kuwa dama inaga yanzun ta gane hanya Nahidt"
Chapter 54 · 0% Book details