Sashe 8
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaki SHUWAR ta ja tana fadin" Dan Allah ki daina cewa mamana ce ke duba fa ki ga kalar gashin da kike da a saman kanki wa kike so ya yarda ? Ka ga yayata ce fada mata me na maka kake biye da ni !"
Murmushi ya sake yana kallon yadda suke shirin kaurewa da wani fada a tsakaninsu ya budi baki yana fadin" Kun ga, dan Allah ku yi hakuri ba maganar kudi ba ya kawo ni nan, haka kuma ba wani aiken babana da zan yi, abinda nake son sani, abinda ya fi daga min hankali a kan SHUWWAR , dan Allah SHUWWAR a shagon babanmu ake maganar budurwarsa harma aka jadadan an daura masa aure da wata mai sunna irin haka jiya, dan Allah, dan annabi shine nake so ki fadan cewa ba ke bace , domin idan kece na shiga uku na lalace"
Fauziya ce ta iya budar bakinta wajen fadin" Da aka yi me kuma?"
Kallon Fauziya ya yi yana fadin" Baiwar Allah Idan haka ne hakan na nufin wannan matar da kike gani matar ubana ce fa, kuma ni kuma na kamu da sonta bilhaki bilahilazi"
NAHIDT ta kalle shi da sauri sai kuma ta kalli SHUWAR da ta saki baki da hanci tana kallonsa itama
NAHIDT ta ce" Ka ga, ina ga mu shige ciki mana wannan maganar ai ba ta a yita a waje bace ka ji? Bismillah"
SHUWWAR ta ce" wani irin ya shigo daga ciki kuma kamar kina son amsar maganarsa a bayane bayan ni ba bariki nake aikatawa ba kema sheda ce? Ka ga bawan Allah eh nice aka dauran aure da babanka jiyan nan"
Da sauri NAHIDT ta ce" Eh kuma ya sake ki ba tare da ya kwonta auren ba ko dan an ce ni yar bariki ce, ko akoy abinda ya shiga tsakaninki da mai shinkafa ne bani da labari?"
Kai SHUWWAR ta dafe jikinta ya fara mugun yin sanyi ta ce" Aunty, ko dai so kike ki nunan mu je ciki da shi ta yadda zamu tatse shi kudinsa kamar yadda kike gagawar kawowa tunaninki? Kar ki ce min bayan halin rayuwar da muke ciki kin manta cewar D'a baya auren matar ubansa koda kasa ta binni idonsa? Da ace ba'a dauran aure da mai shinkafa bane ake iya duban wani abu makamancin haka, aman aunty so kike mu fara shiga hurumin ubangijinmu kuma?"
"Kin ga SHUWWAR kar ki sakani a uku bayan wanda nake ciki mana, ni bana nufin aure ya shiga tsakaninki da shi dan Allah aman kuma ya shigo cikinma ai ba laifi bane ko?" NAHIDT ta fada tana kallonta da tsatsareta da manyan idannuwanta
SHUWWAR ta girgiza kanta tana juyawa wajen ABDUL Mutalab da ya kai duke a wajen ya kurawa waje daya ido a sanyaye ta ce" Ka yi hakuri , ban san sunnanka bama, ka ga du iskancina bana son taka dokar ubangijna,, domin na yarda da mutuwa kuma na yarda da tsayuwa a gaban Allah gobe kiyama, shi yasa nake kiyayewa, nake matukar kiyayewa dan da tarin laifukana idan na sake bayana da irin wannan wanda nake tunanin cetonsama zan iya rasawa watau annabi Muhammad sallalahu alaihi wa salam"
Ta sake sauke ajiyar Zuciya tana fadin" ka ga sakina ya yi a cikin motarsa bayan ya gama zazagin yayata da sunnan karuwa, shi yasa na tarda shi gidansa nima, idan dan wannan ne ka barshi ya rama abinsa, aman ni babu wani abu da zai iya shiga tsakanina da d'a namijin da ba muharamina ba da ya wuce aure, AURE nake so na yi, so nake na yi aure mai daraja na raya sunnar ma'aiki, ina so idan na mutu mijina ya salaci gawata, ina so na haihu na samu ahali irin na kowa, ina so na zauna a kasata duk rintsi na kula da y'ayana na basu tarbiya, ina so na rayu da su har karshen rayuwata, kai a ganninka idan na fara biye biyen y'ayan mazan da suka sakeni na nemi Allah ya zuba ruwan sanyi a saman ALKALAMIN KADARRATA kuwa?, Zaman lafia nake nema, bana neman idasa lalacewa"
Daga haka SHUWWAR ta yi shigewarta ciki da jakar kudinta a hannunta ta bar yayarta da binta da kallo baki a sake tamkar tashar anguwa uku sannan ta maido dubanta kansa da sauri jin wata murya garjejiya ya bude yana fashewa da kuka
Ido suka zarro daga ita har Fauziyar sunna kallonsa yana zaune dangalgal yana fadin" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, leke leken abanmu sai da ya kaishi ya leko wannan yarinyar kuma ya aureta dan wulakanci sannan ya saketa? Gashi Allah zai kama shi a kaina bayan ni kadai Allah ya bashi d'a namiji na kamu da son abinda yake haramun a gareni koda ya bar duniya? Innalilahi wa inna ilaihi raj'une yanzu yanzu fa na ganta a gidanmu idona ya rufe a kanta ashe haramun dita ce Ita din? Aunty kun tabata Shuwwar ta haramta a gareni kuwa? babu irin sabanin bakin nan da malamai kan yi a kan wasu fatawowin ? Kun tabata harshensu ya zo daya a kan wannan lamarin? Ba abinda ya shiga tsakaninsu fa"
Kallon junna suka sake yi a karro na ba adadi suka kuma kallonsa, gannin tsakaninsa da Allah kukansa yake ya saka aunty cike da tausayawa ta ce" Ka ga, ka daina kukan nan hakanan, ka tashi ka shigo ka zauna har a ga yaya garin idan kana iya fita sai ka tafi gida, kar ka damu Allah zai daidaita zamu tambayi malaman mu ji ka ji?"
Kai ya ringa gyadawa aman bai shiga ba ya sheda mata yana iya yawo shi dan takardarsa ta likita da kuma wada aka basu yanzun a hannunsa take
Sunna tsaye sai da ya fita sannan suka kalli junna Fauziya na fadin" Yaya zaki ce masa ya dawo bayan kin san wannan abun haramun ne kuma kin san ta san haramun ne ko daureta muka yi muka kaita zata kunto kanta ta dawo ta same mu, balema ta yaya hakan zai iya faruwa?"
NAHIDT ta shiga takawa dan ta he ta sanyo motar gida sannan au rufe tana fadin" Ke baki ga zai sume mana ba a nan? Ni ba dan hakan zai gyaru ba na ce zamu tambayi malamai kuma ma ai ilimi fadi gareshi, ko waye kai ba zaka ce ka san komai ba a kan lamarin, idan fa akoy wata aya da ta halata hakan? Bayan wannan kawai dan dai gani na yi idan ya sume mana ina zamu iya shiga da shi ne a haka"
Ita dai tana biye da ita ta bude mata gidan da kyau ta sanyo motar ta rufe suka rurufe ko'ina suka nufin falon
Sunna shiga Fauziya ta sake ja ta tsaya ta ce" Kin ga, kin sha saka kila wa kala a kan maganarki ki dawo kanta, koda hakan halak ne ki ajiye maganar dan gidan mai shinkafa, kin ga mutun ne mai iyali, y'ayansa yawa ne da su a duniya, koda auren muka je wasu suka daura masu mun siyar mata walahar rayuwa, ba zasu taba karbarta ba koda bayan ran mahaifinsu, maganin kar a yi karma a fara , ki ajiye kwadayin hakan gefe mu fuskanci reality da sauki a garemu baki dayanmu"
NAHIDT ta ce" to uwata, na ce to uwata Fauziya,, na kula du kun daukeni a wata dakikiya ko wata kura, na ce maku na bar maganar ko?"
Fauziya ta tabe baki ta yi gaba a ranta tana ayana' da ace ban san ko ke wacece a kan maganar son farantawa IBTISAM bane da sai ki fadi haka, ke burinki wani wanda zai sota a haukace kamar wannan saurayin, wanda koda ya ji menene sana'armu ba zai gujeta ba ki aura masa ita, bayan idan har muka yi haukan kaita gidansu yaron nan soyayar sai ta dawo ta zama kiyayar da kare ba zai iya sinsinawa ba, baganin kar a yi kar a fara'
__________________________________
Aikin da suka wuni yi, suka kuma raba dare a kai ya saka shi magana yana lumshe ido tamkar wanda ya yi marisa
Wayar dake kange a kunnensa ya sake saurarawa yana jin muryar mahaifiyarsa dake magana cikin hawaye wanda hakan ne ya saka shi ajiye komai ya masu alamu ya shiga ciki
A hankali ya kai zaune bakin gadonsa muryarsa a shake dan ya wuni yana ihu da bakinsa ya ce" Kuka kike yi?"
Shiru ta yi tana hadiye kukan dake tukota hakan ya saka shi fadin" Mamah, kin san irin ilar kukanki a kaina fa, saboda Allah dan kawai na saki mace sai ki yi kuka?"
Yanzun kasa rike kukan ta yi tana fadin" Kawai ne? Sakin macen na ce kawai ne? Ana cewa kai ta haka hau ya shigeka auri saki shin gaskiya ne? Yaya kake so rayuwa da mace wace zata zamto ta amsa dukan komai a kan daidai bayan ita din da kanta an hakiceta ne da kashin hakarkarinka dake tankwashe? MUHAY daga kara siga a tea?"
A hankali ya ringa murza hannunsa ya ce" Ba iya shine damuwar ba "
Mamansa ta ce" Mecece damuwar?"
A hankali ya ce" Nikakiyar kwalba ce ta zuba mij a tea ba siga bane ya yi yawa"
Sai da mahaifiyarsa ta mije tsaye a zabure tana fitar da idannuwanta ta ce" Ka ga, kar ka fadi haka dan zama da ita ya fice maka a rai, ka riga ka yi mata saki uku ba dawo da ita zan yi ba, fada ne nake maka dan ka gyara halinka dan bana so gobe ka sake sakin wata kai tsaye daga ta yi dan laifi, domin na gaji da irgen matan da ake yi maka MUHAY"
A hankali ya furta " Toh ba zan sake ba"