← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 138

Sashe 16

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ai kam daga Fauziyar har Shuwwar din mikewa suka yi suka shiga daukan akwatinta da suka shirya mata da komai suka fice waje inda makekiyar motarsa fara ke gare suka tsaya kowace zuciyarta cike da tunanin yaya zasu kwashe da Malan ne? domin kwanakin nan NAHIDT ta zama tamkar wata mahaukaciya, kadan take jira a yi ta masifa da ita

Tunda suka fita sai ta samu kanta da sada kanta kasa

Shima a tsayen da yake gaba daya du wani kuzarinsa ne ke barin gangar jikinsa, aman a cikin zuciyarsa banda neman tsari da shedan babu abinda yake yi domin su biyun nan da aka bari shi dai bai ce komai ba, aman yana tsoron yarinyar sosai

A sanyaye ya ce" NAHIDT me zai Hanna ki tashi ki yi kokari a matsayinki na baba mai ilimi ki dauki wayarki mu tafi Ba sai an yi rigima da ke ba?"

Har ga Allah so ta yi a kai gwauro a kai mari da su dukansu, so ta yi a yi masifa iya masifa ta yadda zata kawo raini irin nata har maganar auren nan ta lalace, kwata kwata bata son auren nan da wannan wai shi SUDAIS , a ranta take ji wani jinyatar mata da kanwa ne za'a yi, hakan ya sa take a tsorace sosai da maganar

Aman kamar wanda wannan mutumen ya yi mata asiri sai gata ta mike ta yi gaba yana biye da ita ya janyo kofar tasu ya rufe har suka fito bakin get dinsu inda sabon mai gadinsu yake tana kallonsa kasancewar datijo ne ta ce" Baba, zamu je a raka SHUWWAR gidanta, Idan an yi katari na yi bako a ce ina dawowa"

Baban dai yadda take share fuskarta yake kallo kafin ya amsata inda Malan kuwa ya ji kamar an soka masa kaya a lokacin da ta ce idan ta yi bako, watau yanzun bakin zata fara kawowa gida?

A haka dai ya tisa keyarta har suka karaso wajen motar suka kama suka bude
Tana saka kafarta daya ta kama ta shige tana mai fashewa da kuka tana dora kanta saman cinyarta

Jikin SHUWWAR ne ya yi mugun sanyi itama ta dora kanta a saman bayanta tana hawaye ta ce" Dan Allah ki yi hakuri, ki bar fadan nan haka mana?"

NAHIDT ta rike hannunta sosai tana hawayen ta ce" A tsorace nake, an yi gagawa a maganar auren nan, tsoro nake ji kar ya sake ki ki sake fadawa wani halin zubar da hawayen, kin ga gidan family ne za'a kaiki , SHUWWAR idan suka wulakanta min ke fa?"

SHUWWAR ta lumshe idannuwanta kasa kasa ta ce" Zan ci uban du wanda ya nema, zan rike makogwaron du wanda ya bukata, zan taka du wanda ya taka ni, haka kuma zamu yi zaman lafia da du wanda ya so hakan NAHIDT, ki daina damuwa haka dan ALLAH, kin fa san wacece ni ko?"

NAHIDT ta yi dan tsai da kukanta kafin ta dago tana yar daria daidai sun shanyo kwanar kofar gidan Malan mai gadi ya bude direbansa ya nausa hancin motar cikin makeken gidansa ta talabo fus💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 🔟

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Ta talabo fuskar kanwar tata ta ce" ke kadai nake da ita sai Fauziya aminiyata a duniya, SHUWWAR kar ki yi wasa da farin cikinki koda na second daya ne, kin ga ko uban wanene ? Zan iya ja da shi a cikin gari ko jeji, ki rufa min asiri, SHUWWAR ki rufa min asiri idan uwar mijinki bata sonki dam ki dawo gida, kin ga idan ta maki wani abin zan iya zuwa har gaban danta na kwasheta na watsar"

"Subahannalah......" Malan ya fada yana juyowa ya kalli NAHIDT
Itama shi ta kalla jin zai ahiga harkarta bayan ita dai bata kama sunnansa ba
Samun kansa ya yi da jifanta da harare yana fadin" Ke, kar na ga kin dauki hudubar nan na fada maki, ke kam maimakun ki yi mata hudubar da zata anfana da ita sai ki sakata a motar tsiya? Fito fito fito ku wuce mu je"

Bakinta ta tinziro gaba tana bude motar tana rike da hannun SHUWWAR kam hakama FAUZIYA dake janye da akwatin SHUWWAR din suka bi bayansa

Hankali kwonce ya ratsa mutanen da suka yi dafe dafe dan tarbar bakin da komai har suka idasa shiga falonsa

Amaryarsa dake tsaye ta dauki wanka cikin rantsatsan lesh dan kasa da kasa tana baza kamshi daman bata kai kanta wajen iskancin daguwar abincin daukan amaryar da ya dauka ya jajibawa kansa cewar y'arsa ce yarinya gabjejiya dan kawai bai samu haihuwa ba sai baza abu yake shi ba mahaukaci ba, ba bigage ba, hakan ya sa ta ja ta ki shiga komai sai uwar gidan ce ta je ta tsaya a kan komai domin ita ba zata taba take dokar Malan ba gaskiya

Juyowa ta yi jin salamar sanyin idanniyarta, wanda zafafar kauna irin tasa ta Malan ke karra daukan shaukinta yana sake zaunar da ita tare da shi, domin a zama da malan haihuwa ce kadai babu, aman dukan wani farin cikin rayuwa sunna samunsa a wadace, haihuwar kanta likita ya shaida masa lafiyarsa kalau, lokaci ne bai kawo kansa ba Wanda basu cire rai ba

Fara'ar dake saman fuskarta ce ta dauke a lokacin da ta ga abinda ta gani kartin yan matan nan da ta tsama har cikin zuciyarta bama kamar yayarsu wada idan malan zai ambaci sunnata yake lumshe ido ba tare da ya san yana aikata haka ba ya sakata zarro ido tana fadin" Malan ko dai kaine ka daurawa kanka bamu sani ba?"

Har ga Allah maganar fitowa ta yi da radin kanta hakan ya sa ita da kanta ta sha jinnin jikinta, bama kamar yadda ta ga Malan din ya mata kallo daya tak bai ce mata komai ba ya juya yanaiwa bakinsa bismillah domin ya kula ba zasu samu tarba a wajen matarsa ba

Bayan sun zauna ya juya yana yiwa matar tasa magana suka nufi ciki hakan ya sa SHuWWAR, da NAHIDT binsu da kallo kafin su kalli NAHIDT da ta ja tsaki tana fadin" Ciki za'a shiga a yi munafurci ga dukan alamu!"

Murmushi Shuwwar ta yi tana sake girgiza kanta ta juyo da fuskar auntynta da ta sake juyar da kanta tana fadin" Mamahnah"

Idannuwa ta kura mata tana kane su ta ce" Alamun cuta sun bayana a kalamanki"

Murmushi ta yi tana sake dage girarakinta ta ce" Kece mamana, kuma kema kin san kin isa da ni, ki tayani farin ciki da adu'ar Allah ya sa na shiga kennan, kin ga ki kuma daina yin fada da Aba, shi din mai sonmu ne, in ba ke ba wa ya rabe mu? Wa ya janyo mu? Wa yake son alkhairi da mu? Wa yake yi mana fada?, Kin san da Alkhairinmu ne shi, me yasa kike fada da shi ne bayan ba abinda yake yi maki?"

Baki ta tabe tana fadin" Haka zaki ce ba Abinda yake yi min? Ke bakya gannin abinda yake yi min ne?"

Murmushi SHUWWAR ta yi tana fadin" to ki yafe masa"

NAHIDT ta sake turo baki tana sake kallon dakin da suka shige suka kule a cikin zuciyarta tana ayana' An dai ji kunya walahi!'

Su dai a zaune suke a dakin nan dake fitar da dadadan kanshi, haka kuma nan da nan aka karama su da karamawa mai matukar daraja
Chapter 16 · 0% Book details