Sashe 119
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya malama da ta yi niyar zuwa ta ce da ita ta kira masu mai kunshi ta sauke ta juya tana girgiza kanta da nemawa Furera sauki a wajen Allah, dan ta kula ta matukar daukan abin da zafin gaske, bata san gwara ta yiwa kanta da kyau ta rufawa kanta asiri a kan lamarin auren nan na malan ko zata kankarowa kanta daraja da mutunci a zuciyarsa, to in bandama shirme irin nata abinda baka isa ka hanna ba menene na tada jijiyoyin wuyan? Aure dai nan da yan awani an daura da ikon Allah, gwarama ta ba kanta hakuri ta sha ruwan sanyi
Komawarta ta yi ita akai mata kunshinta da kitsonta sannan ta ci gaba da gyaran bangarenta, domin kayan daki na kasa da kasa Malan ya masu da kayan fitar kishiya, ita kam ai gaba ta kaita , fatanta ta zamo alkhairi a garesu baki daya, dan ko hajiyarta har nan ta zo ta masu fatan alkhairi da nasiha mai ratsa jiki sannan ta yi mata gargadin kar ta saki kishin yarinyar ya sa ta zubar da ladan shekara da shekarun da ta dauka tana yi, domin shi kishi halal ne kuma halita ne, aman idan ka yi hakuri ka daidaita komai zai zo maka da sauki ne bi izinillah
Da wannan ta karra samun kwarin gwuiwar kawar da kanta a lamarin, duba da shima yana yin iya kokarinsa dan ya kiyaye abinda zai iya hasalasu a kan maganar auren nasa
Tana gamawa ta shige wanka dan ta shirya da wuri domin jirgin karfe takwas zasu bi na dare su kwana a cen da sasafe a yi komai da su.
____________________________________
Sosai yanzu ta samu kanta da zafin dake adabarta, tunda wannan abu ya kasance tsakaninta da shi take fuskantar wani sabon mutun mai naci a gareta, yakan yi mata nacin cin abincinta sannan ya mata nacin sakin fuskarta
Bai kuma nuna zai je wajen da ya ki fita da dadin rai ba, aman jikinta ya zamana ne filin wasansa ba dare ba rana, haka kuma lebenta ya kasance har ya saba da tsotsarsa
A haka ta zabi gadajen da za'a zubawa y'ar uwarta da kanta, ta zabi kayan da za'a jera mata, ta zabi labulaye ta kuma zabi kalar da ya dace a sakawa yar uwarta sannan ta shiga rigimar da yaushe zata je gidan ne? A nan ya ringa yi mata kwana kwana da fadin idan an jima har ya samu kanta dare ya tsala sosai barci ya kwasheta tana kan rigimar ita fa atafau a gida zata kwana ta yaya auren NAHIDT gobe gobe aman ace sai gobe zata je? Shi dai yakan shafa bayanta ne ta ciki na ciki, a yanzu kuma da ta yi barci a jikinsa sai da ya saki ajiyar zuciyar da bai shirya saki ba, a sanyaye kuma ya ringa murmushi kasa kasa ya furta" Idan kika tafi ni kuma na yi yaya? Da kin a yadda nake kwana da abu a hannu da kin tausayaminma ni kin karra min tunda dai ai mun warke ko?, Ni kam na zan kuma nesa da ke ta maganar raba gado ba gaskiya, sai dai kowamaa ya yi hakuri......"
(Ga gaisuwa mijin Shuwaa baban Nahidht😍😂🥰🥰🥰a)
Tunda ta farka sallah ta yi dakinta a guje ta rufe ta shiga shirya jikinta ga kuma waya a gefe sai yi suke yi da yan uwanta a nan take ji wai Matan malan sun sauka tun jiya
Baki ta rabe ta zauna gaban madubi ta tsatsara Mak'up dinta sasauka mai fitar da sirrin fuska, sannan ta sake komawa wajen kayanta dake shan turaren wuta ta sauke su ta saka pant da breziya sannan ta kade doguwar Bubu din ta shada dakakiyaa da akai masu aikintaa a waje mai ruwan copee wanda ya ciza sosai ta saka a jikinta
Rigar ta zauna mata a jikinta, sanann ta bude ta yi masifar kyau, haka ta dauko sarkarta ta saka da abin hannu da dan kunne da zobe
Daurin nata mai tsole idon sarakuwa ta kashe ta kuwa kashe shi ya nadu ya yi dassss a kanta
Takalminta mai dan tudu ne da jakarsa ta fitar da su da mayafinsu dake hawa da su farare ne su kuwa gaba dayansu ta dauko wayar tata ta bude jakar tana kokarin sakawa cikin jakar ta fito
Da sauri ya juyo sai kuma ya juya wajen manyan sojawan da suka zo falon suka gama tsara irin zagaye wajen daurin auren da zasu yi dan abinda zai faru wanda basa so a kai ga saka karfi a wajen
Da sauri ya ce" Kunna iya tafiya"
Du sara masa suka yi sannan suka juya da saurin summa suka bar falon
Sake juyowa ya yi dan sake bama idannuwansa kalaci
A lokacin ita dinma shi take kallo da yannayi na matsanancin begen ganninsa cikin manyan kaya , wanda bata taba ganninsa da su ba
Yana tsayen ya kasa motsawa dan ta gama summar da shi da ruwan kyan da ta yi ta karaso a hankali ta tsaya tana dan murmushi tana kallonsa
Fuskarsa ya shagwabe a dan rikice ya ce" Anya kuwa zaki je wajen nan? Ko kuma mu je mu samu katon hijab da nikaf ne? Ni ni ni......"
A hankali ta langwabar da kanta tana murmushi da son jin ya furta soyayarta da kishinta zasu iya saka shi hannata zuwa wajen daurin auren yar uwarta, sai kuma ya yi shiru yana sake takwakwabe fuskarsa
Dan murmushin ta kuma yi a sanyaye ta ce" Ni na ce me?"
Sake kallonta ya yi shima yana so ta bashi haske, aman yar mutuniyar tasa sai ta tsaya iya nan
Hakan ya saka shi fadin" Nine a wahalce, nine zan fi jigatuwa....... IBTISAM kin yi kyau har kamar na ce kin fi kyau kyau"
Kwarai ta yi mamakin jin furucinsa, sai dai kwanakin nan ta gama gane yana da magana a gaban abinda ya yarda da shi, dan haka sai ta yi luuuu da idannuwanta ta ajiye mayafinta tana fadin" Dan haka bara na lulubewa maza gannina a bagas......."
Kyakyawan murmushi ya kasheta da shi yana kallon bayanta har ta shige dakinta kafin yake juyawa ya yi nasa dakin da gagawa shima
Bindigarsa ya daure a jikinsa da alburushi sannan ya rufe ya dauko hularsa ya sake bade jikinsa da mahaukacin turarensa ya fitowa fito yana kanga waya a kunnensa dan jin idan sarkin rawanin ya karaso yana yiwa Aba kuwa?
Sake zuba mata ido ya yi, ta saka abaya bak'a sidik ta nada mayafinta a kan kayan da ta saka , abayan bata da ado ko diz a jikinta sannan budadiya ce sosai, haka kuma nadin da ta yiwa dan kwalin abayar ya amsheta harma ya so ya fi shigar ta dazu kyau
Ajiyar Zuciya ya sauke yana ayana' kyanki ki yi zamanki a dakina na yi ta kallonki ba dare ba rana, idan na fita na dawo na tardo ki, ni kuma sai na je na maki neman dan walahi ko dako zan yi ba zan yarda ki fita ba IBTISAM zan yi na faranta maki mudin raina'
A bayane kuwa sai ya gyara tsayuwarsa ya daga hannunsa wajen kansa ya sarra mata, wanda hakan sai da ya saka ta saki murmushin ba shiri kafin ta sara masa itama
Hannayensa ya bude mata ta zo da dan sauri ta fara ciki, ya mayar ya rufe ruffff a hankali ya furta" Mu je mu daura auren y'armu"
Itama a hankalin ta ce" Aa mu je mu daura auren Abanmu da y'armu"
Murmushi sukai suka fice dan an jima da gyara abin daukansu su din kadai ake jira
Sai da ta shiga ya rage tsayinsa ya gyara mata abayarta sannan ya rufe ya zagaya ya bude ya shiga shima kafin suke dagawa
Tun daga kan kwanar gidan Dad ta ringa gannin tarin sojawan da suke shawagi aka zuba ta ko'ina, sannan lamari na bikin manya tunni baki sun fara yiwa gidan caaaa
Kasancewar da kansa ya dora dokar duk wanda ya zo ko waye daga bakin gate din da suka saka zai sauka ya karasa gidan a kafa a dole doka ta hau shi
Dan haka ya zagaya ya bude mata a hankali ya furta" Bismillah Madam MUHYIDEEN MUHAY"
Idannuwanta ta lumshe sannan ta dora hannun nata saman nasa ta fito lokaci daya ya saka hannunsa yana rike mata jakar tata ,ya kasance hannunta na dana na cikin hannunsa na hagu datan hannun nasa kuwa yana rike da yar pos din tata suka ringa takawa a hankali, shi ya saka farar shada ne kal ita kuma da abayarta a saman shadarta, a jikinta tafukan hannayenta da fuskarta ne kawai ba a lulube ba, ga sojojin dake sanye da kaki sun zagaye su a dole ko baka san da zuwansu ba yadda ake kakauda mutane zai sa ka juyo dan gannin ko su wanene , hakan ya sa kallo ya dawo kansu, aka kuma yi mamaki da kuma rakasu da kallon sha'awa da adu'a , masu daukansu hoto na watsawa haka maroka na ta kokarin kawo gaisuwa , shi kuma burinsa ya kaita ciki ya cireta daga dumbin kartin nan ko zai samu nutsuwa
Sai da ya sadata da cikin gida har kofar baban falon Mahaifiyarsa wanda ya tabata a ciki suke ya ja ya tsaya ya nemi izinin shiga
Ana basu dama ya fara shiga da salama a bakinsa kasa kasa da kuma miskilancinsa
Sai dai mutanen da ya gani da irin shigarsu ta alkyaba ta saka shi dole sakin murmushi yana karra kallon su