← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 138

Sashe 83

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wannan suka koma asibitin, yana ajiyeta ya yi tafiyarsa wajen aikinsa, ita kuma tana dawowa Nahidhma ta tafi ta kimtsa din ta dawo , hakama Mama, wace suka dawo da mijinta domin sai da ta koma ta tarda ya dawo kuma yana ta kiranta wayarta a gida hakama MUHAY ya shige cikin aiki tasa bata tare da shi , a dole ya yi jiransu domin mutan gidan sun nuna su basu san inda suka je ba
Ai kuwa tana yi masa bayani al'ajabin abin ya kama shi, bai yi kasa da gwuiwa ba ya biyota suka koma tare, suka samu yan matan a nan suka wuni abinsu ga abincinsu a gefe da abin sallarsu
Shi ya fahimtar da su ko zaman nan da suka yi ya tabata dan MUHAY ne ya kawo su, domin asibitin nan basa bari ka yi sama da minti talatin a ciki, da zarar ka zo ka ga marar lafiyanka to fa sunna kwatanta maka cewar ka tafi, domin su aikin da suke basa son wannan shige da ficen, Idan wani abin ya taso dole zasu nemeka, aman a yanzu ka basu dama su kula da marar lafiyanka yadda ya dace,

Sunna nan MUHAY ya dawo tare da yarensa uku
Sun shigi sun gaisar da su Mama suka ajiye kayan dake hannayensu suka juya, a nan suka sake gaisawa da Father da MUHAY

Sai da ya je ya gama bayani da likita sosai ya sake jadada masa ba zasu kwana ba , sannan ya dawo ya kwatantawa Mama ya yi masu salma ya yi tafiyarsa gida

Da rarashi, da ban baki su Dad suka fahimtar da su kafin suke iya binsu zuwa gidan

Ko da suka koma gidan kadaice kawunnansu suka yi sukai kuka tsakaninsu bayan sun rungume junnansu

Nahidt a tsorace ta ce" Shuwwa, iidan Mama ta san na yi karuwanci ina tsoron idan wahalar da ta mayar da ita haka bata kasheta ba wannan maganar ta kasheta"

SHUWWA ta girgiza kanta a sanyaye ta ce" Ba zata kasheta ba, da izinin Allah ba zata kasheta ba, sai dai tabas ranta zai bace, kuma kin san cewa daga ita har Abui sun nuna mana soyaya aman ba wai sunna kyalemu bane idan har muka yi abinda zasu horamu, shi yasa a kulun nake ce maki, ki fa ji tsoron Allah ki daina, to kin ce Allah zai yafe maki a yanzu kin daina kina nemansa gafara ba ji ba gani, itama zata yafe maki in sha Allah....."

Da wadinnan hirarakin suka yi dare sosai kafin kuma su zarce da nafilolinsu sannan suka cude waje daya suka yi barci

Tunda sasafe suka wuce asibiti, yau harda matan Dad su biyun dukansu domin a jiya da dare yake fada masu cewar su je su ga narar lafiya, iyayen Matar MUHAY ba lafiya
Kowace da tambaya a ranta , sai dai kasancewar bai bada damar hakan ba sai kowace ta rike abinta suka kuma bi motocin suka je duba su,

Uwar gidansa da wuri ta dawowarta, mai dakin tsakiyar ce ta zauna ta dan jima kafin itama ta tafi , babu wada ta ga mararsa lafiyan haka suka je suka dawo

Sai kusan karfe goma aka basu damar gannin iyayensu na tsayin mintunna talatin, aka shaida masu cewar baci suke kar su yi hayaniyar da zasu iya tashinsu a barcin nan fa, kafin aka barsu suka shige

Su dukansu sun kasance ne a tsaye a gaban gadajen iyayen nasu da kauna da soyaya, da hawaye irin na soyayar iyayen nasu da tausayin abinda ya mayar da su haka

Daya bayan daya suka je suka gansu sannan suka dawo dakin da aka ware masu

Daidai ana kiran sallar azahar a cikin asibitin, ya kasance cikin gari har sun yi salolinsu , a daidai lokacin ne kuma summa suka fito dan gabagar da alwallah a cen wajen pampunnan balbalin asibitin dan ra'ayi

Motarsa ce ta dano kai, ba tare da yan tsaro ba, domin sai da ya sauka a wajen aiki ya je ya dauko Malan da ya sauka shima yanzu yanzun

Tunda suka fito a motar suka gansu, haka suma,

Malan na sanye ne da gari da yar ciki, ya kafa hularsa a kansa hannunsa rike da carbinsa fari kal , haka kuma kafarsa sanye da taklmi sau ciki bakin kirin
MUHAY kuwa yau kaki ne gaba daya a jikinsa babu bambanci sama da kasa hakan ya sa yau ya karra cika sosai yake cika ido

Dan tabota ta yi ta sake nuna mata shi, hakan ya sa gabanta sake balewa ya fadi, kuma abinda ya fi saka su kure su da ido shine kamar wa'inda aka dakatar da su bayan sun baro wajen motar kowane na kallon yar uwarsa

Malan ne ya dan kula da yannayin MUHAY, sannan ya tuna cewa shi fa sirikin MUHAY ne kar bege ya saka su mace su lalace a gaban yan yara guni guni haka, hakan ya sa ya dan yi gyaran murya da dan baza babar rigarsa ya daga kafarsa ya shiga gaban MUHAY din irin da karfin halin nan, irin ai shine baban baba a wajen nan dai kau?

Turus ya yi sakamakon gannin NAHIDT ta taho da dan saurinta, sannan ta dan wara hannayenta, uwa uba ta fashe da tabararen kukan da nan take shedan ne? Ko kuma banzan tunaninsa ne? Ya sheda masa cewar idan ta karaso wajen nan babu abinda zata aikata sai rukunkume shi a cikin bainar nasi, a irin wannan rana da ya dauki azumi , sannan ya zo a matsayin siriki watau mutumen da ya dace har ya bar wajen nan ana dubansa da daraja da mutunci, sai dai kasshhhh, wannan lamari da ya fuskanta ya saka shi jin kamar cikinsa zai juya masa
Yanzun fisabililahi wannan aikin na adalci ne? Da girmansa da darajarsa?
Ba shiri ya dan tatare babar rigar da sauri ya zagaya ya labe a bayan MUHAY dake kallon ikon Allah shima yana jira ya ga wai me zata yi ne haka?

Yana labewar da yaren larabci ya ringa maimaita kalmar sunnanta yana girgiza kansa yana lekenta har ta karaso da mamaki shinfide a saman fuskarta ta ce" Yah habiby yaya haka?"

Ido ya dan rintse dan hanna zuciyarsa fitowa, a hankali ya ce" Yah khalb me zaki yi ne?"

Muhay bai taba jin abinda ya tuko masa dariya ba shiri ba irin na wannan ranar, a hankali ya dantse lebensa na kasa ya baza idannuwansa yana kallon soyayar larabawa a lokacin da Shuwwa ta kyalkyace da dariya har tana dukawa tare da dafe cikinta tana kallonsu, daidai Doctern nan ya fito nurse na rike da takardunsa ga dukkan alamu gida zai je ya hango Shuwwa a duken nan tana kyakyata dariyar nan , hakan ya saka shi sakin murmushi yana sake kallonta kafin ya samu akalar tafiyarsa da juyawa yana nufarta , hakan kuma ya sauka a kan idannuwan MUHAY wanda shima ita din yake kallo harda bin mayafinta da ya fadi dan dariyar ketar da take yiwa Abanta da ya labe, hakan ya bayanar da gashin kanta da yau ta dan caje shi ta saka masa dan ribom, sannan ya sake maida dubansa kan likitan nan dake karasowa daidai NAHIDT ta budi baki tana leken MALAN da ya labe kansa da kafarsa baya so su yi hadewar nan da ta zo masa a kwakwaluwarsa da azuminsa a bakinsa ta ce"ALKALAMIN KADARRATA

PAGE

Na

Sajida

4️⃣7️⃣

*ZO KI JI, KE DAI DAMUWARKI RASHIN SHA'AWA ? KE TUNDA AKAI MAKI AURE KIKE FAMA DA SHI? KIN RASA GANE KANKI?, KE KAWIAI KALLON MUTANE KIKE DU KIN RAME KIN TSOTSE SABODA BAKYA SON ABINDA AKE MAKI MAI SUNNAN JIN DADI?, KE KUMA YAR UWA TUNDA KIKA HAIHU KIKA HADU DA WANNAN DAMUWAR, WATAU TUNDA AKAI MAKI AIKI KIKA RASA WANNAN JIN DADI DA KIKA SABA DA SHI KAFIN AI MAKI AIKIN??????, MAZA JE KI KASUWA HARHADO KAYAYAKI KAMAR HAKA : SOBO JA, GIMJIMBER, QUATRE CÔTÉ, POIVRE SELIM, da Copin ruwa biyu ( ku yi hakuri duk mai so zan turo mata da hotunnan abin domin ni ban sansu da hausa ba gaskiya, ko ku dora a google za'a baku su)....... Zaki hade su ki dafe su gaba dayansu ne, sai ki ringa sha karfe daya kafin lamura su kankama, ko tun da magariba................... Itatuea ne basu da wata matsala, idan kika ga lamuranki sun daidaita kina ita dakatarwa..........*

Ta ce" Ya habiby, me zan yi kuwa? Zan fada maka ne irin halin da Abanmu yake ciki da mamanmu fah"

Kansa ya dan girgiza ya ki ya fito din,

MUHAY dake ta binsa da kallo har ya karaso gannin Nahidt ta dan kare masa sai ya daga kafafuwansa da kyau ya matsa masu ya shiha takawa ya karasa wajen da take kyakyata dariya daidai lokacin da docter ke fadin" Dariya ta fi kayatar da fuskarki yar budurwa"

Da sauri ta dago dubanta kan docter, shi kuma komai ya sauka a cikin kunnayensa
Bai ce komai ba ya dan rage tsayinsa ya mika mata hannunsa na dama hakan ya sa ta juyo da wani saurin tana kallon fuskarsa

Gannin fuskar tasa a hade ba alamun ya taba yin dariya ta saka hannunta a cikin nasa, ya cicibeta ya mikar da ita sannan ya jata suka nufi ciki ko kallon likitan dake kwatankwacin abokinsa bai yi ba dan takaicin yarinyar

Yana shigowa da ita ya saki hannunta yana kallonta ya nunata da yatsarsa daya ya ce" Ki kula, kina wasa da igiyar dake wuyanki bayan har yanzu bata tsinke ba, ki kiyaye ki iya bambance igiyar aurena da ta sauran banzayen da kika aura, abayoyinki da hijabanki gaba daya munafukan abin lulubi ne, ban san a kan wani dalili kike son rayuwa irin ta bude jiki!"
Ya karashe a kausashe yana dan juyawa ya dafe gaban goshinsa hadi da rintse idannuwansa ya ce" Kin ga, me zai hanna ki rufawa kanki asiri ki kama mutuncin kanki ne? Har hanyarmu ta rabu da ke?"

A hankali idannuwanta dake kallon kasa ta ringa dagosu har ta sauke a saman fafadan bayansa da ya bata baya
Kalmar har hanyarmu ta rabu ta ringa maimaitawa a kasan zuciyarta har ta samu ta gane ma'anarta
Chapter 83 · 0% Book details