← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 138

Sashe 25

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sasautawa ya yi domin shi da kansa da yake yin maganar sama sama ba sabawa ya yi ba, wahala hakan ke bashi ainun
A sasaucen ya dora da fadin" ba zaku gane cewar babu wanda Allah bai san da zamansa ba tunda shi ya halici abinsa ne?, Shin baku yarda cewar a yanzu yanzu kunna iya mutuwa bane?, Ko kun kai wajen da babu ruwanku kin rayu a kyamace a cikin duniyar kuma ku koma kiyamar ku tarda azabar wanda ya halice ku tunda har kuka ringa rayuwa kamar ba zaku koma gareshi ba?, NAHIDT, SHUWWAR, Fauziya ina da tambayar da nake son yi maku ba yau ba, shin haushin wa kuke ji da har kuke wulakantar da rayuwarku a banza a wofi?, Iyayenku kunne shedar aure suka yi suka haife ku a kasa mai tsarki, yaya haka kuma?!"
Ya idasa yana sake kallonsu, ya ci gaba da fadin" ina Tsoron mu kai matakin da zan zame maku abokin gaba, idan na ce abokin gaba ina nufin wanda zai ringa hakon rayuwarku karfi da yaji dan ku gyara rayuwarku, gwara na zamo maku wanda zai tirsasaku tunda na kula kun rigaya kun mayar da kanku wa'inda basu san ciwon kansu ba!, Zan koma masalaci za'a zo a kwashe akwatunnan nan a maida su gidan su Sudais! Bashi da abinda zai ba Shuwwar! Bashi da shi na ce!" Ya karashe da karfin da ya saka SHUWWAR din kanta kallonsa domin da farko du kawunnansu a kasa suke
Da sauri kuma ta maida kanta dan walahi har cikin ranta take jin maganarsa, kai wacema ke masa fito na fito din kanta a kasa bale su

A kausashe ya ci gaba da fadin" Hamza, mutun ne kamar kowa, sai dai kuma namiji ne kamar kowani namiji, ba zai kuma shigowa gidan nan kansa tsaye ba har sai na gama tantance hakan, Shuwwar kar ki kuma fita, ki zauna daga yau ki lazumci astagafari, ki ringa azumin litinin da talata, ke koda ba ranakun nan ba ki yawaita yin azumi kinna fadawa Allah sannan kinna barawa Allah zabi a kan rayuwarki, shi ya yi ki, shi ya dora ALKALAMIN KADARRARKI a haka, shi yake da ikon mayar da baki fari, a wajensa ne kawai zamu nemi sauki , ina fatan kun ji abinda na fada maku kuma kun dauka"

Daga haka ya mike ya basu baya ya fice fuskarsa a mugun haden da ya saka suka raka shi da kallo riiiiii kafin Shuwwar ta ce"

Shin labarin na birge ku kuwa?......ku garzayo ku turo shaidar biyanku dan mu taka mu shige cikin labarin Alakamin kadarrata tare da ku........ in sha Allah gobe zamu tsayar da freee page🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥺💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣4️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Ikon Allah, du rashin kunya irin ta y'ayan nan ashe idan suka hadu da wanda zai kausasa masu dan kankin kansu zasu kasance masu biyaya ne harma bakinsu ya yi shiru? To dai gasu nan a gaban Malan, sun yi shiru kamar basa nan, ya gama fadan ya kuma tambayi idan har sun fahimci yarensa sun yi alamun dake nuna masa cewar sun fahimce shi

A nutse ya mike yana daukan carbinsa ya juya ya fice a falon gaba daya ransa a cakule sannan ya yi niyar daukan mataki a kan yawon su SHUWWAR, dan ya kula idan ba sakawa abin birki ya yi ba tabas Shuwwar ba zata samu lafiya ba, bama ya bukatar sannin abinda ya fitar da ita daga dakinta wannan karronma, abinda SUDAIS ya fada masa a wayama ya wadatar, sannan zai je ya samu Malan ya tambayeshi shin dama akoy wata yar tsama a tsakaninsu da zai sa ya wulakanta rayuwar yarinya ya sa a saketa a ofishin sojoji kamar wata yar ta'ada a barta ta kamo hanya ita daya tana kararamba a titi ? Yanzun da ba dan Allah ya kawo Hamzan nan ba da ai shikenan ta afka a wata sabuwar rayuwar mai wahalar fita, shin idan a cikin y'ayansa yan matan akaiwa haka yaya zai ji? Walahi, walahi, walahi yadda Shuwwar ke kiransa da Aba ta kuma sada kai idan yana magana sai ya ji ciwon wulakancin da akai mata tamkar an yiwa gudan jinninsa ne, kai yau da shi wani takadarin dan duniya ne da ya auri daya daga cikin y'ayan malan ya maka mata saki a cikin jejin Allah ya barta da kanta ya ji idan akoy dadi!, Shin me yasa mutanenmu suka cika son kansu ne? Menene anfani sako dan mutun a gaba dan aure ya hada ku ne? Abin bacin ran yanzu abun ya zama ba macen ba namijin ba, kowama aikata son ransa yake yi kai tsaye abinsa

Su kam bayan fitarsama a kadan an dauki minti biyar sunna zazaune su dukansu babu wada ra motsa
Cen Shuwwar ta sauke ajiyar Zuciya tana kallon Auntynta ta ce" Ashe babama da babansa "

NAHIDT ta juyo da sauri tana kallonta ta ce" Ke SHUWWAR da wa kike?"

SHUWWAR ta girgiza kanta tana hayewa saman doguwar kujera ta ce" Ba da kowa ba "

NAHIDT ta sake juyowa sai karra cika take tana batsewa a bayane ta furta" Sai kace ubanmu? Gaskiya mutumen nan ya iya wulkakanci, yanzu tsakani da Allah meye laifin Hamza?"

Fauziya ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Bashi da laifi, ko daya bashi da laifi, sai dai kuma abinda Aban Shuwwar ya fada gaskiya ne, ya dace wannan karron mu bi komai a hankali, gagawar me muka tsinta a cikinta ne banda wahala?"

Shiru ta yi bata basu amsa ba, sai salamar da aka yi aka ringa shigowa da kayan abincin da ya saka su bin masu shigo da kayan da kallo, sai da suka gama ajiyewa a baki baki yaron ya duka yana fadin" Malan ne ya ce a kawo, ya kuma bada wannan ya ce a bada"

Ambulope din Fauziya ta amsa idannuwanta a waje ta buda ta fitar da abinda yake ciki
Gaba dayansu sai da suka zarro ido suka kalli yaron da ya gama yi masu bayani ya mike ya yi tafiyarsa

A bayane Fauziya ta ce" Allah kennan, kin ga yau muma irin haka ce ta same mu? Lalle Aban Shuwwar ba shuwwar kadai ya haifa ba, muma babanmu ne"

NAHIDT kam bakinta gaba daya ya mutu tana bin kayan cimar da kallo, harda madarar peak, da kidin gwongwani, sai ta samu kanta da jin dadin haka a cen kasan zuciyarta aman kuma ta ki yarda ta bayanar da haka a fili saima bara masu wajen da ta yi ta nufi cikin dakinta

___________________________________
Chapter 25 · 0% Book details