← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 138

Sashe 94

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MUHAY ya sauke numfashi a nutse ya ce" Dad dazu na samu damar fara gabatar da bincikena nima, to dama hotonsu na dauka tun a cikin zanar nan, sai na samu na binciko irin masu kazagin nan , maganar dai da nake yi na tura sako an saka a hannun mutumen cewa ina mai mika kukana wajen sarakanmu su kula da mahaukatan kasarmu, ya dace a ringa kama su ana basu kulawa domin summa mutane ne, na dan samu ne na hada da wasu hotunnan na kwatanta cewa a cikin garin nan na gansu..........., Maganar dai da nake yi Dad tunda na dawo nake samun kira ta number daban daban, harma a Wajen aiki an fada min cewa an turo mutane daga masarauta wai ana so a fadi inda aka ga mahaukatan kaf ana so a fra kilace su, kuma ana gaishe ni............, Inaga koma menene ya kawo kansa fa kansa, ni kuma na daga masa kafa ne dan ba da dan aikensa zan yi ba, lamarin nan tuni na saka shi a cikin jerin karar da na ba alkali ya fara nazarta.........ina kyautata zaton da *SULTAN* muke tare, kuma an masa sihirin da ya fitar da shi ne daga kasa harma daga rayukan al'umar dake iya tunnawa da shi"

Ai Dad bai san lokacin da ya kai zaune dabak a kasa ba, gaba daya jikinsa har rawa yake yi a rikice ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, Ka tabata kuwa Son? Aman waye zai aikata irin wannan mumunan aikin?, Saboda me?"

MUHYIDEEN ya ja fasali a cikin numfashin da yake saukewa ya ce" Dad , *KUDI, MULKI, MATA* sunna da karfin da zasu iya saka bawa aikata aikin dana sani, ta sanadiyarsu komai na iya faruwa, ina kyautata zaron kujerar da take tasa ce ake so aka kauda shi"

Dad ya ringa girgiza kansa muryarsa na rawa ya ce" aman kuwa idan haka ne duniyar gaba daya ta fita a raina Son, wai ina zamu shiga da rudaninta ne? , Bata da komai a cikinta sai kazanta da shirme, bata da komai sai tashin hankali, ni yanzun nine na sauki SULTAN a gidana? Yaya zan yi na iya yin kamar ban gane shi bane? Son ka dawo yau please ka dawo in ba haka ba ni ba zan iya shiga na hada ido da ido da shi ba walahi"............

Dan murmushi MUHAY ya yi ya ce" zan zo jibi Dad, ka yi kokari kar ka nuna masa ka gane komai, mu bashi dama ya samu nutsuwar zuciya, dazuma mun gana da Hamza da kuma Malan, su dukansu sun gigice jin an gansu harma Hamza ya ringa kuka da fadin shi ba zai je ba ai yarda shi ta yi, Malan dai ya dan masa nasihohi inaga da ya gane ko rabon su yaran nan na iya fitar da ita ko me dai da sauransu, summa sum ce zasu zo goben nan, aman na dakatar na fi so na gamsu da lafiyarsu"

Dad ya amsa shi cike da jin girmansa a zuciyarsa da kaunarsa a ransa ya ce" Allah ya albarkaci rayuwarka yarona, ya jikan Mahaifinka, ya karawa mahaifiyarka Lafiya, zan taboka in sha Allah"

Da amen ya ringa amsawa ya katse kiran yana kalle kalle a wajen da ya zauna dabar da duwawunsa tsabar ya ji labari mai rikitarwa

Gannin Maman Muhay na tambayar sojojin nan ko sun gansa ya saka shi mikewa ya nufeta

Da kula ta ce" Haba abansu, ka san da kyar na raba rigimar cen ka tafi ka barni? Hala kuka ka yi?"

Kansa ya girgiza yana shafa fuskarsa ya idasa kusa da ita sosai ya ce" Aa Mama son ban yi kuka ba, hala dukansu suka yi?"

Kai ta girgiza tana murmushi ta ce" Du fa y'ayan nawa ne suka fi rikicewa, to ai dole hankali ya tashi mana, shine fa suke ta kuka da yare kala kala sunma bayar da hakuri, shi kuma mahaifin nasu ya yi gumm, dama mamansu tunda ta yi shiru bata ce masu komai ba, shine fa kamar zasu mutu kuka tun karfinsu sai da na duka nima na bada hakuri kafin mahaifinsu yace to laifin me suka yi? Haka Allah ya hukunta......ni yanzun na fara tunanin anya kafin a masa kurciyar nan ba wani baban atajiri bane ba kuwa?, Kai ko ba attajiri bane mutumen nan yana da iza a tare da shi Abansu"

Dad ya ja gwauron numfashi ya ce" Hummmmmmm?, Uhummmmmmm, "( 😂 magana a baki ba halin fadi kai tsaye),

Mama ta dan karra kallonsa sosai kafin ta ce" Mu je ka ci abinci ka huta kaima, summa abincin suke ci da yaren"

Kofar ya sake kallo kasa kasa ya ce" wai me kuka dafa masu ne?"

Mama ta ce" Cuscus ce"

CHIEF OF ARMY ya ce" Allah dai ya sa an masu kamar kala uku haka, jus fa? Ina fata kin masu ire iren jus din nan naki kala kala masu dadi, wai ACn nan dai bai rage sanyi ba ko?, Maman Son anya ba za'a kaisu babaan gidan nan na GRA ba?"

Mama ta yi sakai tana kallonsa, har sai da ya ankara sai kuma ya yi dan mursmushi ya juya ya nufi hanyar bangarensa yana fadin" Gani na yi bakinmu ne kuma sirikanmu"

Mama ta sake bin bayansa da kallo kafin ta gyada kanta ta bi bayansa tana fadin" Uhum Abansu kennan"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 5️⃣5️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Abincin suka ci a tsanake, yan matanma na ci a cikin baban plat guda, sai dai jikinsu har yanzu ba a sake yake ba

Sai da suka gama suka tatare komai suka dawo a lokacin mahaifinsu ya sake fuskantarsu a sanyaye ya shiga yin adu'o'in da ya saka su dukansu suka daga hannayensu sunna amsawa har ya yi ya gama kafin ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana kallonsu ya masu alamu da su matso kusa da shi gaba dayansu

Sunna matsowa ya fara rike hannun iyalinsa a sanyaye ya ce" Allah ya sa wannan jarabawa tamu itace silar shiga aljanarmu TINANAH"

Mama ta lumshe idannuwanta tana amsawa a sanyaye

Ya dora da fadin" Kin yi hakuri sosai Tinanah, kin jure, kin kuma jurewa, kin zauna da ni a haka, na yakusheki na maki komai aman kin hakura kin zauna da ni, Allah ya yafe maki dukan kura kurenki, ya faranta maki, ya bani ikon faranta maki duniya da kiyama"

A tare wannan karron suka amsa gaba dayansu

Tinanah na kallonsa ta ce" Papah, har yanzu ba zaka iya fada min abinda ya kaimu masarautar garin nan ba? Ka ga an dauke mu ne a lokacin da ba na kamu ba, domin ibada ake yi kowa nada damar yi aman mu sai aka kama mu, a irin wajen da ba'a kamu ko daya a nan aka ritsa mu, tun daga nan sai a bakin dakin nan da muka farka muka ganmu a ciki, tunda ka buda ido ka bi dakin da kallo da hoton mutumen nan dake da rawani ka rikice ka fita a hayacinka kennan sai kwanan nan ka dawo yi min magana irin na da, shin a kasar nan wa ka takawa da zafi, ko kuma an hadaka ne da wani daban?"

Fuskarta yake kallo mai dauke da ramar da ta yi, aman irin yadda gashin kanta ya mata lufluf har zuwa dan sajen da take da shi a gefe da gefen fuskarta abin sai ya sake bashi sha'awa, shin yaya zai dubeta ya ce mata shi wane ne kai tsaye haka bayan ta hadu da dan saurayi ne a Makka sun kula zumunta ta soyaya sun yi aurensu a matsayinsu na masu nema gaba dayansu?, Bayan wannan baya so a yanzu yanzuma y'ayansa su san wannan maganar gaskiya, yana gannin kukan da suka yi haka ya isa haka, duda ya dauki matakin da ya tabata zai iya sake saka su a hadari, aman ya zama wajibi a Yanzu ya fuskanci mai nemansa ka'in da na'in ya amshi abin aron da ya ara harma ya wulakanta shi saboda shi

A sanyaye ya ce" Zan sanar maki bi'izinillah".

Daga haka ya yi shiru da maganar da ta tambaya, ita dinma sai ta yi shirun bata ja maganar ba domin ta san ko ta ja ba riba a tafiyar, dan ba musu yake so ba, idanma ta ringa nacin abu to fa ya mata shiru ko garu albarka

A hankali ya sake kallon yan matan y'ayansa, ya yi murmushi ya mika hannunsa yana dan jan habar SHUWWA dake kallonsa itama a sanyayaye ya ce" Sunnanki IBTISAM, ke y'ata ce, kece tarbiya, kece kamala, kece takama, kece kwaliya, kece daraja Ebtisemmmmmmmm, abinda ya faru ya wuce, shin za'a daidaita a kamanta rayuwa mai adalci gabanan kuwa?"
Chapter 94 · 0% Book details