← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 138

Sashe 17

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiraye kirayen sallar magariba ta fitar da Malan daga dakinsa ya wuce malalaci, matarsa dake dayan dakin na ciki kuwa tunda ya nuna mata mahinmancin baki ya umarceta kan ta fito ta kula da su ta labewarta a nan sai da ya fita ta fito tana mai sake bin NAHIDT da kallo domin du ita ta fi tsole mata ido sannan ta wuce bata ce da su ko ku ci kanku ba

Ana gama sallar isha'i da yan mintuna dirar motoci ya tabatarwa mutanen gidan amaryar da Malan zai mika dakinta ce aka zo dauka, hakan ya sa gaba daya jikinsu ya sake yin sanyi

A lokacin da Malan ya shigo ya saka su gaba ya shiga yiwa SHUWWAR nahisa sai ya kasance suma sun dukar da kawunansu sunna masu jin maganar har cikin bargonsu
Sai da ya gama ne ya bada damar a shigo a tafi da ita, a nan ya sake kurawa NAHIDT ido yanai mata kallon da shi da kansa ya san ba kyau a adininsa, aman irin yadda take cijewa tanaa yiwa yar uwarta bankwana ta kasa tashi daga zaunen da take har aka fice da SHUWWAR Fauziya na kofa tana hawaye ita kuma ta kasa tashi daga ita sai shi ya saka shi yin dan Murmushi a sanyaye ya ce" Allah ya basu zaman lafia"

Sai yanzu ta iya dagowa ta kale shi, hawayen cikin idannuwanta na gangarowa, ta saka hannunta da sauri tana sharewa

Murmushi ya sakar mata yana furta" Tashi na maida ke gida "

Mikewa ta yi ta kama hanya bata bi ta kan matarsa da ta shigo yanzu yanzu gidan dan fita ta yi a sace ta tafi ta aikata abinda take gannin shi zai gyarata, domin ita dai ba zata yarda da irin wannan cin kashin ba a rayuwar mijinta !

________________________________

Satinsa uku da dawowa daga garin su SHUWWAR, dawowarsa har zuwa yanzu zama ne yake yi kadan aiki da yawa
Abinda ya fara bashi ciwon kai shine karancin masu laifi a garin nan
Gari ya riga ya zama capital inda kannanun barayi ne kawai suke bayane na bakin kasuwa, bayansu sai manyan yan hadama dake takatsantsan da takunsu, bayan shi burinsa ya samu waje mai dauke da masu laifi ta yadda zai baza kwonjinsa da horon da ya samu a kasar waje ta dogon karatun da ya yi har ya samu matsayin da yake kai a yanzu

Haka kuma gefe daya mamansa ta jajirce ta murje kan sai ya sake yin wani auren, hakan ya sa ya bada damar samun wata dan ya aura domin shi da kansama a cikin halin rayuwa yake na rashin mace a gefensa

A yau da ya zo gidan nasu ya tardo abinda ya saka shi yarda cewar a duniya idan ka zamto ana yawan ganninka a waje ana iya rainaka sosai, domin yarinyar Fatser yar gidan uwar gidansa ce ta dubi tsabar idannuwansa ta nuna shi take so a gaban mahaifiyarta da mahaifinta inda mahaifinta mamaki ya saka shi tsayar da murmushin da yake yi mata yana kallon mamanta da ta dauki magana tana murmushi tana fadin" Ai ni kam cewa na yi abu ya fi karfina ta samu abanku ta fada masa da kanta ya gani da idannuwansa, Sir ba dare ba rana yarinyar nan maganarta LIEUTENANT GANARAL ne, tun ina daukan abin da wasa har ya zo ya zama gaske a raina domin ta jajirce ta tsaya a kan ra'ayinta, shine dai na ce Yau tunda ya zo bara ta sanar da bukatarta na san ba zata rasa ba"

Mamakin matar tasa ya saka shi kafeta da ido, Ikon Allah, aiki na son rai karara ya bayana a tare da matar tasa, kamar ba ita bace abokin kishinta, abokin ra nuna ana sonsa ana masa meye meye to fa MUHYIDEEN ne, nan har nunawa take zai iya cin gadonsa tana lamari irin na kar a fara yi masu haka din nan, kuma yau itace da fadin irin maganar nan? Bayan ko ga maciji basa yi da mahaifiyar yaron, kishi take yi da ita kiri kiri ?

Fuska ya hade yana kallon y'ar tasa ya ce" Ashe baki da hankali? A nan waye sa'anki a tsakanin ni da Son din? Ashe idannuwanki sun bude haka ne da zaki kawo min raini irin wannan?, Ke yaushe na yi sake da tarbiyar y'ayana da har zaki zo ki dubi idannuwanmu da kafafuwanki a nan ki ce kina son Son?"

Da mamaki hajia ta ce" Aman Elhaj menene damuwar a nan? Inace so halita ne?"

" Dan Allah malama saurara min hakanan, irin haka ne kuke sakawa y'ayanku tunanin da zai halaka su ku dawo kunna nuna baku san lokacin ba, so? Na yaushe? Kin ga bana son aiki irin na son kai da shirme, idan shi yace yana so fine, idan ita ce zata bilo min da wani hauka ba zan dauka ba, ban haifi yar da ta isa da kanta ba, daga ke har ita ina iya baku mamaki a kan harkae SON!" Ya fada da karfin da ya saka MUHYIDEEN dake kallon TV kamar baya dakin dan rintse idannuwansa domin hayaniyar ta fi damunsa fiye da rainin yarinyar gaskiya

A kausashe ya kuma korar yarinyar da tsawa yana rakata da kallo domin da matsanancin kuka ta fita a falon tana mai jin ciwo a zuciyarta, Me abansu yake nufi? Du wannan kwaliyar , da jiran lokacin nan da ta yi ana nufin a banza ko me? Ama wasa abansu yake, walahi wasa yake yi, bai san ta sha walahaula a kan maganar GANARAL ba? Yadda ta iya tunkararsa yau ai ya ci ace abanta ya shiga mamaki da tsoro a kan neman katangeta da shi!

Mahaifinta a kausashe ya dubi matarsa yana fadin" Haba hajia, da girmanki? Da komai? Na san so halita ne, aman idan baki katse hanzarinta ba me kike so ta zame maki ne? Kin ga yanzu maza basa son tsaurin idon nan, ko daya basa sha'awar irin haka fa, ku kiyaye dan Allah, kece baba a gidan nan bayana, ke ya dace ki ringa tsawatar da duk wani hayaniyar gidana ba ki rinka taya yarana neman fitinata ina zaman lafiyata ba"

Ita kam da ya sani, da shiru ya yi da Neman fahimtar da ita yaren da bata ganewa, domin gaskiya ita abinda y'ayanta ke so ko bata so zata mara masu baya ne, ita kam tana yiwa bukatar yayanta biyaya, to idan bata yi ba me ake so ta yi? Bata bin bayan zaburar da yaro ba gaira babu sabar a hannawa yaro nutsuwa da zaman lafia a banza a wofi

Tana zaunen nan maman MUHYIDEEN ta shigo da salama sakamakon kiranta da SHIEF OF ARMY din ya yi tana gaishe sa matarsa wace kamar jira take ta shigo sai ita ta mike ta fice

Zama ta yi tana kallon yannayin MUHYIDEEN dake kallon TV sannan ta maida hankalinta kan mijinta da ya ce" Kin ce kina da magana a kan maganar auren yaron nan, wacece maganar?"

Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye ta ce" Maganar a kan tafiya aikinsa da ya kawo yana so a bashi dama ya je garin cen ya yi shekara biyar, Elhaj jiya ina sauraron redio wani abu da aka yi ana fadi sai da raina ya kiya, na san ba shi ya isa ya hanna ta'adanci ba, aman yana bada gudunmuwarsa ba laifi, dan haka na bashi damar ya je garin aman da sharadin auren nan da ya ce yana so a daura masa a nan zai bar matar, ta haka zai zamto ya ringa tafia yana dawowa wajen matarsa yanai mata weekend, sannan idan matar tana kusa da mu ta yiwu wannan auren ya dore in sha Allah"

Tunda ta fara maganar sai yanzu ya dan dago ya kalleta sannan ya yi dan murmushin da sunna gane murmushi ya yi ne idan yannayin kakausan kallonsa ya dan daidaita kamar na mutane sai ko idan sajen fuskarsa ya dan sake hadewa

A hankali SHIEF OF ARMY ya ce" Yanzun ba zaki daina rigima ba? Shekaru fa aka ce ba wata daya ko biyu, soja ne fa, shine zaki raba shi da iyalinsa ki ce a ajiye maki ita a wajenki? To ki yi mata me?"

Kansa ya sake sadawa yana dan kurawa agogon hannunsa ido jin dakin ya dauki shiru, ya tabata mamansa na son saka mijinta ya yarda da maganar nan ne da idannuwanta, domin ta riga ta shanye magana da ido bale idan tanaiwa mijin nata

Muryar SHIEF OF ARMY ne ke fadin" Ba fa zai yiwu ba zakina wani marairaicewa, shi din bakya tausayinsa ne?"

Sake sada kansa ya yi yana son ya furta cewa ba komai, aman kuma baya so ya katse masu magana

Sai kuma ya ji Sir din na fadin" Hasana, Hasana gaskiya kina takura min a kan maganar yarona, kai MUHYIDEEN shin ka amince da maganar nan ne ko baka amince ba? Idan baka amince ba bani da damuwa zata daina ne ta barka ka yi tafiyarka !"

Dan mumushin ya sake yi a hankali ya ce" Aa Aba, na amince da bukatar Mama"

Su dukansu sai suka samu kansu da kura masa ido
Sarai tausayin yaron nata ke yawo a sasan jikinta, sai dai idan ta duba ta ga idan ya tafi yana iya zamewa ganninsa ya yi mata wahala sai ta karra yarda da wannan shawarar da ta yankewa kanta

Aa hankali ta furta" Yaushe kake son tafia ne?"

Dago da fuskarsa ya yi yana ji dama ace ya iya nuna murnarsa ta hanyar kurma ihu ya yi rawa? Kai da ya gwada domin da ace mamansa ta san irin taimaka masan da zata yi na barinsa zuwa garin nan da ta jima da barinsa, shi baban abinda yake so ya fara dirarwa wadinan tsagerun da suka yi wasa da hankalinsa, shi MUHYIDEEN MUHAY su dube shi au ce zasu zagaye shi da rainin hankali? Sai ya tura mota an dauko su sau dukansu a duk inda suke sun sake buga game din kafin ya shiga cikin gari hankali kwonce ya ringa buga game dinsa son ransa
A dan kagauce ya ce" Yauma sai na je Mama"
Chapter 17 · 0% Book details