← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 138

Sashe 104

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

SHUWWA ta sake komawa jikinta ta labe tana ta sauke ajiyar zuciya hadi da kallon bayanta dan du a tsorace take
Hankalin Nahidht ne ya fara tashi da gasken gaske, dama iyayen du basa nan matar Dad an yi asibiti da ita da yarenta dake koke koke sai sune a gidan, sai ta fara jin tsoron ko wani ne ya biyota haka? Ko kuma wani abu ne ya samu mijinta
A rikice ta sake riketa tana fadin" Shuwwa wai menene? Wani ne ya biyo ki? Ko wani abun ne ya samu mijinki?"

Shuwwar ta girgiza kai a birkice tana fadin" Ba zan kara ba, na zata zan iya abinda kuke fadi ashe ba zan iya ba, wayo Allahna ni tsoronsama nake ji, kennan ya wulakantani shikenan ya sakeni? Ai gwarama sautan da suke sakina basu yi komai da ni ba!"

Fahimtar inda maganar ta dosa ya saka Nahidt rungumeta a jikinta a sanyaye ta ce" Hey babyn auntynta, wanu irin kar ya taba ki?, Haba autan mama mijinki ne fa , kece fa mai kokari mai jajircewa"

Tana girgiza kanta ta zauna tana kallonta ta ce" Wani irin jajircewa gareni a gabansa?, Burina na faranta masa, ban sani ba ko bani da sa'ar a soni domin Allah ne?, Tubeni fa ya yi yake neman amsar abinda na dade ina rikewa nawa da nufin ya kwace m......"
Rufe mata baki da ta yi tana girgiza mata kai ya sakata yin shiru tana jin yadda zuciyarta ke dokawa da karfi sannan ta sake kwontar da kanta a saman cinyar Nahidht dake dan shafa bayanta

Sai da NAHIDHT ta kula ta dan fara dawowa cikin hayacinta kafin a sanyaye ta ce" Sirrinki ne fa, ibtin Aba sirrinki ne wannan, duk matar dake bayana sirrinta da mijinta lalle ta yi asara koda kuwa Allah ba zai hukuntata ba, balatana haramun ne, sannan yaya kike so ne?, Me kike so ne?, Ai yama yi kokari da yake kallonki kina dauke da abinda yake malakinsa , aman bai taba nuna maki yana so ba sai yau, shine kika guje shi, haba yar albarka kin san da ba'a gudun namiji ko? Duk soyayar da yake maki idan dai ke din nan kin zamto wace bata yi masa adalci walahi zai iya hakura da ke ne domin a kan wannan lamari maza basu da hakuri fa, Na san cewa a cikin duhu kike aminiyatah, na san cewa a cikin wasi wasin so ko kiyaya kike daga wannan bawan Allahn, aman zan fada maki wani abu, wasu mazan Allah ya sa kin fi zinari kyali, kin fi gol daraja ba zaki taba ji daga bakinsu sun bude sun furta maki kalmar so ba ko wani abun, su haka Allah ya halice su, ba zaka iya cenza su ba fa, ko me zaka yi ba zaka iya cenza su ba SHUWWA, koyon zama ake yi da su da halinsu sai a ci ribar zama da su, su a aikace suke nuna kalar tasu soyayar, kece baki yarda cewa wannan bawan Allahn na sonki ba, aman mu dake tare da ke mun riga mun yarda, Shuwwa ba zaki iya tantancewa ba, aman idan kina waje idannuwansa a kanki, haka kuma idan ya fuskanci wani na iya kallonki koda yayanmu ne baya iya boyewa, da idannuwansa da kuma motsinsa yake yakin dukkan wani abun da zai rabe ki, aman sai na ga ke sam bakya duba da haka........... Wani irin cutarwa kuma kike magana a kai? Ni fa ina gannin girmansa da kimarsa koda duk duniya zata ki shi, domin shine silar samun farin cikinmu da muka rasa.....shin ke bakya gannin hakan ne kanwatah?"

Shuwwa da idannuwanta ke lumshe tana biye da dukkan bayananyar uwarta ta dan dago ta ce" Nahidht so kike ki ce min shi a haka zan rayu da shi tamkar dutse? Bayan ni burina na rayu da namiji mai min kukan yana sona? Ya ringa min ihun yana so na?,ya zamana tamkar jelata sai abinda na ce ya yi zai yi? Ya nunan so a gaban kowama ya kareni da dukan karfinsa ya shagwabani? Yaya zan iya rayuwa da mutun mai halayarsa?"

Nahidht ta dan zarro ido da mamaki ta ce" Ki ce kawai rayuwar mafarki kike so ko kuma nace rayuwar karya?"

Shuwwa ta ce" Kina nufin babu soyaya a gidan aure? Ko bashi da zuciya ne shi a jikinsa?"

Nahidt ta yi Murmushi tana girgiza kanta ta ce" Babu soyaya ake zaune? In babu soyaya an saka maku wuka a kawunanku ne?, Dukan gidan dake dauke da mace da mijinta da y'ayansu koda tana zaune da shine domin y'ayanta to fa idan aka bincika akoy soyayarma, halaya ne na yau da gobe ke disasheta, da ace zasu kamanta dawo da kyautatawa da zata dawo , Shuwwa da kin fada ya yi uwarsa ce ke?, Ko kuma da kike so ya zamto tamkar jelarki kece mijin ba?, Kin ga ibada ne aure, zama ne na ibada, dukan ibada kuma sai da juriya da hakuri koda za'a kai ga ci, ki sani rayuwa baban nasarar da kika yi a yanzun amsa sunnan matar aure, zaki idasa ga ci ne idan kika yi hakuri kika ci gaba da zama da shi, Allah na tuba rayuwa ai zo mi zauna zo mu saba ne Shuwwa, zaman da yake kulun cikin dariya da farin ciki ina tsoronsa, ai zama dole akoy sabani wani sa'in, aman kuma ana ganewa ana hakuri da junna shine daidai, kin ga ina so ki fahimci wanene mijinki sannan ki masa adalci a zamantakewarku, kar ki yi wasa da damarki, kar ki yi sakaci da aljarki Shuwwa, ba zan so ki kasance mai yiwa mijinki rikon sakainar kashi ba, idan kuwa yana zuwa kina kauce masa babu abinda ba zai faru ba ciki harda daina gannin girmanki da karo wasunki da zasu tarbe shi da zarar ya buda hannayensa., Ba'a barin namiji da yinwa Shuwwa, ba'a yi........"

Fuskarta ta shagwabe sosai tana langwabe kanta ta ce" Ni tsoro nake ji ne Nahidt, walahi tsoronsa nake, kuma yanzunma cewa ya yi yana jin yinwa da ishirwa kin ga baima ci abincin ba inaga ya kwonta barci"

Nahidt ta sake kureta da kallo kafin ta yi murmushi tana girgiza kanta ta ce" Mace bata kadan, komai girman namiji kuwa baya fin karfinta Shuwwa, rijiya ce mai daukan guga, haka kuma babu wanda ya girma da dadi koda girman bariki ne, sannan ki kokarta ki koma ki gani ko zai yarda ya ci abincin yanzu kin ji? In bandama abinki mutumen da kece shedar yawun yan bariki a kansa ne kike son yin wasa a lamarinsa?, Koda yake baki san menene kalmar nan ba, bana so ki santa ta tsiya kanwata, bana so ki san sharin yar bariki, domin wata yar barikin komai taurin kan namiji sai ki ga ta shawo kansa cikin sauki bale naki mijin da yake da bukatar hakan? Wai har kin manta niyarki a kan kudurin mamansa a kansa?"

Ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya tana ta auna magangannun Nahidt din, har aka fara kiraye kirayen sallar magariba Nahidht ta mike tana fadin" Abanki fa gobe zai juya dan ya sanar masu wai da wata magana, ban san ta mecece ba da ba zasu iya bara min shi ya karra kwana biyu a nan ba ni kam"

Ita dai da ido ta rakata har ta shige bayi kafin ta sake gyara zamanta tanaa jiranta

Tana fitowa a bayin itama ta shiga ta kwabe suturarta ta shiga tsaftace jikinta kafin ta dauro alwallah
Sai da ta cenza kayanta ta yi sallah sannan ta mike ta koma bangaren nasa da wani hijab din ba wanda ta cire aa jikinta ba

Tana shigowa ya yi daidai da dawowarsa kennan daga masalaci da carbinsa a hannunsa na hagu yana ja a hankali, a hannun damar kuwa waya ce yake ta gwada kiran Dad dan ya ga basu dawo ba, ya yi ta gwada kiran wayar mamansa bata shiga, gashi harda sultan a yan rakiyar bayan yanzu yaronsa ke fada masa tarkonsu fa yana daf da kama kurciya domin wanda aka danama ya. Haukace a kan neman su a cikin garin dan anma buga hotunnan an yadda da sunnan ana nemansu za'a fara kilace mahaukata ana basu kula.....to dai ya yi saken da aka gano sunnansa ne a jikin jaridar dake yada labarun

A lokacin da Dad ya daga wayar muryarsa a matukar sanyaye ya yi sakama kafin ya dan saurara yana jin amsar Dad din sannan ya ce💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 6️⃣0️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A lokacin da Dad ya daga kiran muryarsa a matukar sanyaye ya yi magana sannan ya saurara yana jin abinda Dad din ke fada kafin ya ce" Ina fata jikin da sauki Aba?"
Chapter 104 · 0% Book details