← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 138

Sashe 27

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ya karya masa zuciya ainun harma ya samu kansa da dawowa ya zauna saman kujerar yana kallonta ya ce" Lafia?"
NAHIDT ta rike hannun shuwwar sosai a sanyaye ta ce" Malan, Allah ya saka maka da alkhairi........" Muryarta da ta dauki gargada ta saka shi ya kuma dan dagowa ya dan kalleta kafin ya mike da sauri ya yi gaba ya bar masu gidan gaba daya, ita kuma ta fashe da kuka tana rike kanwarta a jikinta wace gaba daya take cikin wani yannayi
A sanyaye Shuwwar ta ce" ki daina kukkan, idab kuma bakya son auren nan ne wannan karron ba zan yi maki gardama ba, domin na fara tsoron kar aje ko dan ina bijire maki bake gannin ba daidai ba, kin ga idan bakya son wannan ko? Bani da ja, sai na je na ci gaba da zamana har Allah ya kawo min wanda hankalinki zai kwonta da shi Nahidt"
Nahidt ta girgiza kanta aa sanyaye ta ce" baki da hankali ne?, Ni nake cikin farin cikin wannan lamari, nice nake cikin gagarumin farin cikin gannin mutumen da nake maki marari ne Allah ya kawo mana, shushu kin ga irin son da yake yi maki? Ba dare ba rana sai ya yi kiranmu a gidan nan, du irin yadda Abanki ya gindaya masa sharuda kuwa a haka ya ci gaba da neman kyautata mana ba tare da ya taka daya daga cikin dokokin Malan ba duda kuwa ya san ba malan bane ya haife ki aman ya masa biyaya dan ya ga mun yi masa, kin ga kuwa wannan mutumen abin a girmana ne, abin a mutunta ne, kuma kin ji Malan din ya ce a gidansa zamu je a yi zaman bikin ki, yana so a yi wunin bikinki a cen duda na san matansa ba zasu so hakan ba aman dan dolensu na san zasu yi girki su kuma tarra mutane, Shushuna kin san meye yake saka ni kuka? Farin ciki nake yi kan ashe kina iya yin auren gata, auren da yake ba boyaye ba, auren da yake na an san ke ko wacece kuma aka roku alfarmar ana son ki? Hakan na nufin Ashe akoy sauran musulmai masu koyi da koyarwar adinninmu, Shushu wannan baban farin ciki ne ai"

Shuwwar ta yi murmushi tana share hawayen dake saman fuskar Nahidt cikin zazakar muryarta ta ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 1️⃣5️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

*KARSHEN FREE PAGE*

Cikin zazakar muryarta ta ce" Da Aba ke ce min na ringa dakatawa har ya lazumci lamuran aurena sai na ga wanu lazumi kuma bayan ga haza ana so na, nakan manta dumbin samarin dake nuna min so sai su fito min da wata maganar a tunaninsu shine burina, idan kina fada kan saurayin da na kawo a matsayin wanda nake son na aura sai na ga kamar bakya min adalci, kamar baku damu da abinda ya dameni ba, in na je aka sakoni kuma sai na ga waye ya dace na fara saukewa sama da ke? Tunda dama baki so aka yi auren ba, a mutuwar aurena da SUDAIS sai na fara fahimtar wani abu, tun haduwata da SUDAIS idona ya rufe kamar a kan sauran, SUDAIS na nuna alamun na masa da dan barkwoncin yana son ya aureni a nan take jikina ya kama rawa na ringa taro shi ina nuna masa ai ni kawai maganar nan ta aure daa ya fada itace za'a yi domin itace ke rudani, itace farin cikina, kin ga idan zai zo nice dafa wannan, soya wannan, gyara wancen, na zo na shake masa gabansa da abinci na sala wanka na ringa jiran shigowarsa, da zarar ya ce min gayanan har rawa jikina yake na kamma gindaya maku sharuda kan sshigarku, kan shigi da ficenku, du a kokarina kar ya ga abinda zai sa ya daina aurena dan ina jin kunyar ahalina....., A haka ya nemi a yi aurenmu a rufa rufa, kin san da na fahimci yana jin kunyar abokannansa su san yar gidan da ya aura ne ya saka shi aikata haka? Aman tsabar ban san ciwon kaina ba sai na amince ido rufe na nuna nima din ai bani da daraja, Aunty na san da yana zargina, ina hankalce da irin kalamansa da irin yadda yake kiyaye komai a tsantsamce, sai idan ya ga na dan shiga hali na tunani sai ki ga kuma ya sasauto ya shiga yi min kalamai irin na son ya mantar da ni halin da zuciyata ta shiga a kansa, ni dai du a tunanina auren dai idan na yi na tafi ai shikenan, Aunty a haka aka kaini da sharadin ba zaki bini ba, ba ke ba ba Fauziya ba, na yarda kaina na rawa na bi matar babansa daa wata tsohuwa suka daukeni suka sadani da dakina, Aunty a gidan dama dakin nan shine kadai abinda na isa da shi, Mijin da nake yiwa ya gagari idannuna, Aunty daidai da girki irin na kowace mace ni gagarata ya yi dan kuwa ina ji ina ganni banma isa na taba masu abincin da zasu kai bakinsu ba..........., A hankali na ringa koyon yadda matar gidan ke mu'amalantata tana nuna min ita din mai daraja ce, a sannu sannu na farra gane cewar bayan darajar da take son nuna min tana da ita hakama y'ayanta sunna da ita sai kuma na ga tana kyamata bayan du abinda na ga ya zamto al'adunsu su na ara na yafawa kaina duda dama bamu tashi da banzar shiga irin ta sutura ba, Aunty a hankali na ringa karantar cewa auren nan nawa babu inda zashi shima domin mijin da aka aura min din bai nuna alama ba, amarya da aka ce shine ni na fuskanci haka a tawa rayuwar?, Aman kin san me?"
Nahidt ta girgiza kanta tana kallonta
Shuwwar ta saki Murmushi tana fadin" a hakan ba dare ba rana fadawa Allah nake yi Allah ya sa ya tuna da ni ya zo ya bani darajata ta mata a gidansa, Allah ya sa ya daukeni mu yi nesa kamar yadda yake alkawarunta min cewar zai aureni zai yi min meye meye ke dai abubuwan da maza kan yi anfani da su dan rudar da zuciyar yan mata irina idannuwanmu ya rufe har mu ringa gannin rannaku sun mana nisa, irin shigo shigo ba zurfi din nan sai mun afka su nuna mana halayansu na samarin Shaho, a ranar da ya shigi ina sakawa falona turaran wutar da kika hada min a ranar ya zo min da raini, da wulakanci, da fitintinnu da zargi karrara, aman kaina a kasa, so nake ya fuskanceni ko ya ganewa kansa ban san abinda yake zargina a kansa ba.......... Aunty sai a zaman nan da na yi na karanci rayuwata na gane ashe da na tafka kuskure? Domin ba wai samuna a cikakiyar budurwa bane zai sa wasu mazan su bani darajata, tun a farko nice na nuna bani da daraja, nice na nuna bani da mutunci, na nuna dangina haka, waye zai mutuntani? Walahi watan uwarta ce karuwar kuma sananen karuwanci aman dan uban wani namijin dole zai bata daraja dan ta siyawa kanta ita!, Nawa suke yawonsu su tashi yin aurwn bayan sun tsaftace kansu su kuma samu daraja? Ni fa fita nake yi neman sa'ar a aureni, to sai aka aurenin kuma aka ci ubana!"
Chapter 27 · 0% Book details