← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 138

Sashe 11

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya rintse ido da karfi a lokacin da bai shiryawa hakan ba kafin ya bude idannuwan nasa yana kallonta ya ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une, subahannalah wala haula wala kuwata ila bilah, subahannalah subahannalah subahannalah, wani irin saki kuma? Yaushema aka daura auren shi kuma wani irin abu ne ya gita haka ya sau ki?"

Da mugun kaunar Bawan Allahn da shekarunsa shi din kansa ba zasu wuce arba'in da biyar a duniya na a kasan zuciyarta na irin yadda karrara damuwa ta sakinta da akai ta bayana a tare da shi bayan basu hada dangin ina ko na aba ba da shi take kallonsa kafin ta ji zuciyarta na neman tsinkewa.......................................................................mmmm💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 7️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Sosai zuciyarta ta fara rawa, ta jure, ta daure, ta kawar da kanta a kansa sau kusan uku dan kar ta aikata Abinda zuciyarta ke son sakata aikatawa aman ina, sai da ta samu kanta da fashewa da kuka tana zaunawa gaba dayanta a kasa maimakun da farko da take tsugune a kan kafafuwanta

Kanta ta sada sosai tana yin kukan da ba ihu ba salalami aman kuma kuka ne mai tukowa daga cen kasan zuciyarta yana fitowa fili wanda ya saka shi sake jin ciwon maganar sakin nan
Hankalinsa a tashe ya ce" shin wani laifin da ya cencenci a yiwa sunnar ma'aiki irin wannan wulakancin kika aikata masa da ya sake ki ne, Yah Allah karshen auren ne ya tabata? "

A hankali take gyada kanta kafin ta sake sada kanta cikin kukan ta ce" Laifi ya ce na aikata masa Aba, ya ce an ce masa mamana karuwa ce shi yasa ba zai iya zama da ni ba, na yi iya yina dan na kwatanta masa cewar yayata ce kuma bana so ana kiranta da sunnan nan aman abin ya gagara karshe ya sake ni sakin da Allah baya so watau saki uku tashi daya Aba"

Carbin dake hannunsa yake ja da gagawa gagawa yana ambaton Allah a hankali kafin ya cire dubansa ya ce" Ita Nahidt din abinda na hanneta da aikatawar ci gaba ta yi da aikatawar ne?"

Kanta dake kasa ta gyada abin na cin ranta ta ce" Ko yau har yanzu basu dawo ba, ban san ina suke ba, aman ina cike da Tsoron da kuma jin haushin gannin dawowarsu su dukansu biyun"

Wani zafi ya sake ji a cen kasan zuciyarsa
Shi da kansa shekarunsa ba zasu wuce arba'in da biyar ba a duniya, Allah bai azurtashi da haihuwa ba, haka kuma a wajen mahaifinsa kafin ya rasu ya bara masa gado na makudan kudi da na karatu na mamaki, mahaifinsa shi daya tak ya malaka mai rai a duniya, matansa biyu sunna zaune da shi har yanzu duda natsalar rashin gannin kwayakwayensu a tare da shi, aman ba wace ta tafi dan baya haihuwa, ya kasance yana matukar tausayawa rayuwar yan matan nan, IBTISAM na kiransa da Aba kai tsaye abinta, aman yayarta tsabar takadariya ce takan kireshi ne da sunnansa kanta tsaye abinta, idan yan laushin na kusa kuwa sai a ce da shi Malan

Ya yi ya yi da yayarta kan ta dauko kanwar tata da Fauziyar dukansu su koma gidansa da zama, yana so ya taimakawa rayuwarsu, yana so ya basu yanci irin na kowa, aman tashin farko ta nuna masa hakan ba mai yiwuwa bane domin zaman na iya haifar da fitintinu masu yawan gaske kama daga zamantakewarsa da iyalinsa, da mutanen anguwa da wajen daukan karatunsa, ana iya sako su a gaba a ce sai yadda aka yi da su bayan basa ra'ayin hakan sam sam
Da wannan ta murje ido ta ki maganar

Bai san me duniya ta yi mata da zafi haka ba, bai san yaushe zata daidaita lamuranta ta bar komai ta koma ga Allah ba, bai san yaya zai kwatanta irin ciwon da yake kwana yake tashi da shi a kasan zuciyarsa na irin dabi'un NAHIDT ba, a yau ya tabata idan har ya samu barci to fa sai dai barawo jin an sake jadada masa NAHIDT na aikinta wannan abu dake saka shi yin amai, dake kona masa zuciya, watau bata bari ba bayan a da gaske ya san cewar bata barin ba fa, kawai dai bai san dalilin da ya sa baya so sam a ringa tunasar da shi cewar bata bari din ba

A sanyaye ya ringa furta" Ki yi hakuri IBTISAM kin ji? Ki daina kukan haka, Allah ya sa hakan shi ya fi zama alkhairi a gareki da mu baki daya, kin ga ki share hawayenki wani hannin ga Allah baiwa ne kin ji?"

Kai take gyadawa tana share hawayen nata ta ce" Haka ne Aba tunda gashi har Allah ya fitar min da wanima , sunnansa Sudais kuma shi bama tsoho bane haka kuma bashi da aure sannan ka ga bashi da rusheshen cikin nanma sam"

Bai san lokacin da ya maido da dubansa kanta ba yana furta" IBTISAM ki yi shiru da magana"

Shirun ta yi tana kallonsa, haka shima yana kallon kuruciyar dake dawainiya da yarinyar a bayane ba a boye ba, ta yadda idan ta yi wasu abubuwanta a bayane ake iya gannin yarintarta da komai nata

A nutse ya ce" IBTISAM yaushema kika fita a ciwon abinda wancen ya maki? Kin ga bana son aikin gagawar nan fa, shi yake sakawa mu aikata aikin dana sani, gagawa fa aikin shedan ce IBTISAM"

SHUWWAR ta karkata kanta tana fadin" Aba walahi ba maganar gagawa a cikin lamarin nan, tunda safe muka hadu da shi a wajen kallon taron da aka yi yau, a kadan mun yi awa uku da shi muna zantawa, ya fada min ko shi dan gidan waye, ya fada min sana'arsa, ya fada min cewar mamansa ta rasu, aman matar babansa bata da matsala ba zata tsane ni ba zata so ni tamkar y'ar cikinta da ta haifa, ya fada min zan daina kukan maraici haka kuma yayata zata yi alfahari da aurenmu, ya fada min komai Aba yana da nutsuwa sosai kuma yana sona"

"Ya salam, ya salam, IBTISAM dan kawai ya farfada maki duka wadinnan shikenan ya gama zama mutumen kirki sai aure? Wani irin neman aure ne haka da gagawa haka?"

SHUWWAR ta shagwabe fuskarta ta sanyayar da muryarta ta ce" Aman ai kai kake cewa jan maganar aure bata da dadi, yawan tsayawa zance bashi da kyau, idan aure za'a fito a yi a fito a yi kar a tsaya tsaye tsaye ko?"

Dan murmushi ya yi yana fadin" Du na sani, to aman IBTISAM idan ke ya fada maki wanene shi, ke me kika fada masa a kanki? Ina nufin yadda ya fada maki komai a kan rayuwarsa kema haka kika fada masa?"

Tsai ta yi da hirarta tana mai maimaitawa kanta tambayar Liman, kanta ta dago tana kallon fuskar Liman mai dauke da ni'ima irin ta ma'abocin riko da adinin musulunci

A hankali ta ringa tunano hirarakinsu da SUDAIS, gaba daya a hirarakin nasu basu yi maganar da ta shafi usulinta ba, sannan bata fada masa ainahin wacece ita din ba, da aure auren da ta yi da dukan dalilin da yake sakawa ana sakinta ba

Gaba daya sai ta samu kanta da mutuwar jiki da dukan gaban jikinta muryarta a sanyaye ta ce" Aba, idan na ce masa zaune muke daga ni sai aunty sai Fauziya a gidanmu, sannan na ce masa su aunty ke ciyar da ni sannan basa aikin komai, sana'arsu lalataciyar sana'a ce anya zai so hada zuriya da ni? Anya zai so aurena kuwa?"
Chapter 11 · 0% Book details