← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 138

Sashe 89

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nahidht ta yi yar dariya tana fadin" Walahi mama mun zata a cen zamu zauna ne, sai ga soja yace mu zo gida, to dai itace ta yi gardama , har ya koma yan mintunna sai gashi da wata ta dauko Shuwwa cimak kamar baby, Allah mai iko, a yau na ga abubuwa walahi Mama"

Mama ta yi Murmushi tana mika hannunta ta kamo hannayensu, da kyar ta iya budar bakinta tana fadin " ku yi hakuri y'ayana wani abu ne ya fitar da ni na gagaw akun ji?"

A sanyaye Shuwwa take kallonta, a hankali ta dan karra matsawa kusanta tana sake kallon fuskarta

Mama ta yi masu dan Murmushi ta ce" ku je ku yi wanka maza ku kwonta ku huta zamu yi magana gobe in sha Allah "

Amsata sukai suka mike suka nufi cikin dakin

Sunna shiga wata gardamar suka dora da cacar bakin har dai Shuwwa ta fara shiga wanka ta barta da waya a kunne sunna zantawa da babanta bayan ta gama fadin ta mata shiru zata zanta da tsohonta, ita dai ta shigewarta ciki da mutuwar jiki

A nutse ya sake dan bata lokaci a wajen mahaifiyarsa, ba wani dogon magana suke yi ba, aman dukkan maganar da suke yi na tafe da kula da kauna irin ta d'a da mahaifi, tana dan nuna alamu na ta yi dana sannin matsawa har ta ji maganar, shi kuma yana yin iya yinsa dan ya kwatanta mata cewar in sha Allah komai zai wuce, har dare ya tsala ya kamata ya rakata har cikin dakinta

A lokacin da zai fita daga dakin nata ne ta dan yi murmushi tana fadin" MUhay, yaren nan basa birgeka?"

Dan dakatawa ya yi yana dan juyowa dan ya fahimci wasu yara fa?

Mama ta sake yin dan Murmushi tana cewa" Ina sonsu a raina sosai, ina sha'awar yarintarsu, sannan ina son ci gaba da kula da su sosai, ka ga su fa dole sai anai masu uzuri sunma yi kokari fa?"

Sai a lokacin ya gane wa'inda take nufi, dan Murmushi ya yi mata a hankali ya furta" Allah ya tashemu lafiya Mamahnah"

Mama ta amsa shi itama tana kallonsa har ya fita kafin ta mike jiki a mace ta shiga bayi ta yi wanka hadi da dauro alwallah ta dawo falonta ta cenza tufafinta hadi da daukan dardumarta ta fuskanci gabas ta shiga kai kukanta wajen ubangijinta tun yanzu, domin ita gyara da sauki take nema a wajensa, ta san cewa shine kadai ya isa ya sanyaya mata halin da ta tsinci kanta a ciki, ta kuma san cewa idan kana da damuwa ko baka da damuwa ka kasance mai kai kukanka a wajensa sannan mai gode masa a kowani irin lokaci, shine baya gajiya da baka, baya gajiya da rokonka a gareshi, shine mai mayar da baki fari, ta kuma yarda cewa shi zai mata.

______________________________________

Kofar ya kama ya bude ya shiga ba tare da ya yi salama ba, to koda dai ya yin gaskiya kunnayensu basu jiye masu ba sam sam

A hankali Nahidt ta ajiye man dake hannunta a ranta tana ayana' Toh fa, me muka masa kuma ya shigo ya bamu daidai da kugunmu? Ni fa har ga Allah Tsoron mutumen nan nake shi yasa bana haye masa, Allah dai ya raba mu lafiya'

Mikewa ta yi tana ajiye man a nan ta dauki hijab dinta ta kalli wajen da Shuwwa ke zaune saman madubi tana fesa turare a jikinta su bayan kunnenta ne, au hamatarta ne, da dai sauronsu ta ce" Bara na ga ko zan samu netwrk din nan a waje "

Sai da ta zo fita sai kuma ta ja ta tsaya tana dan kallonsa ta ce" Yalabai, dan Allah na ce dama na fitar da miji a taimaka a daura mana auren nan kafin su Mama su ankare da abinda na aikata , ban san yaya zamu kare ba, kar su tsine min albarka kuma a zo a shiga uku"

Idannuwansa ya dago a karro na biyu ya sake kallonta kafin ya girgiza kansa bai bata amsa ba yana kallo ta juya ta fita a dakin, ya riga ne ya gama yin waje ya ajiye yarinyar nan cewa akoy wani abu dake damun kwakwaluwarta, koma menene dai akoyshi abin nan

Dan ribom dinta ta saka ta daure gashin kanta sannan ta mike ta juyo face to face da shi

Idannuwanta ta tsatsara a saman fuskarsa kafin ta dan sauke ajiyar zuciya ta ringa takowa zuwa wajen da yake tsaye

A hankali ya ringa kallonta yana fasara me hakan yake nufi? Har ta zo gab da shi sosai tana niyar take taku dayan da ya rage ta auka jikinsa ya samu kansa da dan matsawa yana sake kallonta da mamaki kafin ya ce" Me kike yi haka ne?"

Dan duduba gefe da gefenta ta yi sannan ta sake kallonsa, da zazakar muryarta ta ce" Ban gane tambayar ba"

Idannuwansa ya yiwa micik micik ya ce" Kin ga , karfa ki dauki abinda ya faru a asibiti a matsayin da niya na aikata, na aikata ne dan wani dalili daban ba abinda kike tunani ba"

Idannuwanta ta dan zaro ta ce" Me na ce to ni?"

Da kallon kar ki rainan wayo ya kalleta ya ce" Dama bana so ki ce din, ki kula ni kar ki fada min!"

Bakinta ta dan tabe tana juyawa a hankali ta shiga dan takawa ta ce" Dadin abin jikinka ai ba laushi ne da shi bale a so fadawa!"

Ido ya dan tsura mata kafin ya saka hannunsa ya damko nata ya juyota gaba dayanta yana kallonta ya ce" Me kike nufi?"

Kasa kasa ta kalla wajen kirjinsa sannan ta dago tana kallon fuskarsa , sai kuma ta shagwabe fuskarta sosai ta ce" Ka ga fa damkar min hannu ta yi da karfi ta ciciboni a gaban mutane har sai da rigar dake jikina ta yi sama har ana gannin cinyoyina , yarenka na kallo ta watsa ni a mota ta rufo, fisabililahi kafin mu rabu ai an wulakanta mutuncinka ko?"

Gaba daya sia ya ji har tsigar jikinsa na neman tashi na bacin rai, da sauri ya kalli wajen kaffafuwan nata sannan ya kalleta da kyau
Wani kunna ya fara ji ransa na yi masa, harma ya shiga tambayar kansa da Colonel bashi da hankali? Shi ya sa akaiwa matarsa tsirara? Lalle zai koya masa hankali kuwa daga shi har ita!

Rai bace ya ce" kina ji, Mama na cikin bacin rai, ki yi kokari ki dubata kafin ki kwonta, shine kawai ya kawo ni!"

Daga haka ya saki hannun nata da ya damko ya juya har yana hada kaffafuwansa wajen sauri ya ciro wayarsa ya danna kiran Colonel

Colonel na dauka da fada fada sama sama ya shiga fadin" Ashe baka da hankali? Da wa da wa kuka je daukan iyalina har za'a dorota a kafada?"

Da mamaki Colonel ya ce" Sir?"

MUHAY ya yi gagawar katse shi da wani fadan yana fadin" Ka saurara malan, kafar katana a waje a gaban karti? Ku hadu gaba dayanku har ita mai karfin a fada kin dalili!" Daga haka kittt ya kashe yana huci ya juya wajen da ya ga an tsura masa ido

Dan murmushin da ya saka gabanta ya kwonci kwonci ya fadi ya sakar mata , wanda ya sa bayan tsoron gannin an shiga da natar MUHAY din dakin cen, ya karra dora mata Tsoron kar dai gaskiya ne da matar tasa tace ya san ko su wa ke bibiyarsa?

Da sauri ta juya tana barin wajen gabanta na ci gaba da faduwa da tarin tsoro a ranta.......................

Sai da Nahidt ta gama kallonsu kafin ta yi murmushin itama ta koma ciki da wayarta a kunnenta sukai salama ta tura kofar dakin Shuwwa tana mai yin salama a bakinta

Gannin shuwwa tsaye ta rungume hannayenta a kirjinta ya sakata yin dan kasakai tana kallonta, sai kuma ta tabe baki ta zagaya zata haye bed ta ji Shuwwa na fadin" Oh, ban taba jin murya mai dadi irin ta sojan nan ba, kaf duniya babu mai dadin muryarsa wollah"

Nahidht ta mike zaune da sauri tana kallonta da mamaki ta ce" IBTISAM wa kike nufi? Ina fata Abanki?"

SHUWWA ta juyo tana kallonta itama ta dafe habarta ta ce" Abana kuma? Me hadina ni kuma da fadin muryar Abana?"

Nahidht ta idasa zama da kyau ta ce" Ke aman bakya jin tsoron Allah, yanzu wannan muryar marar sirri ce zaki ce ta fi ta Akaramalahu alarama ustazu bawan Allah, murya sam ba sirri ba laushi ba lausasawa?"

Shuwwar ta idasa saman gadon tana fuskantarta ta ce" Me zai hanna kowa kar ya fadi aubun kowa kawai a zauna lafiya? Kin ga dai kar ki sa na ce muryar ubana wata sanyi karai ba wani kazar kazar bayan ana son namiji da zarar ya yi magana a waje, kai ko motsi ya yi a gane ba kawai a ringa rarashin mace ba!"

Ido NAHI ta zarro da mamaki ta tafa hannunta ta ce" zan ga annabi in nai hali na gari, yau kuma ke? Yanzu yaushe kika fara sonsa? Wai son gaske ko karya? Ke bari ki ji karya ne a zagi Malan a gabana walahi"

shuwwa ta tabe baki tana kashe wayarta ta jefa mata tana fadin" dadin abin a nan babu abinda ba'a yiwa uban nawa ba, yanzu a wani ce ana sonmu, kuma da kike cewa ni in so soja kema kin san kin dai fadi ne, maganar gaskiya a yita yana da dadin murya, yana da kanshin turarae dadada fajat aman ba maganar so bata taso ba!"

Daga haka ta juya ta barawa Nahidt dakin wace mamaki ya sakata hangame baki tana tunanin kaf duniya ba wace ta rainata irin kanwar tata.

Tunda ta zo dakin Maman take zaune tana kallonta, sujada ce ta yi kanta a kasa har sai da ta fara jin Tsoron rashin dagowarta, harma ta ambaci sunnan kiranta da sunna Mama? A sanyaye tana kallonta
Sai cen Maman ta dago da fuskarta dake cike da hawaye ta yi zaman tahiya sannan ta salame ta juya wajen da Shuwwa ke zaune tana kallonta
Chapter 89 · 0% Book details