Sashe 34
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dan murmushi ya yi ya juya wajen da Fauziya ke zaune ta rakube ta hade kanta da gwuiwoyinta tana kuka , takan dago ta sauke dubanta a kansu ta kuma maida ta sake fashewa da wani kukan irin na cikin ran nan mai cin rai din nan ya nuna wajen da take ya ce" Kunna nufin harda wancenma mamansu daya ne?"
Su dukansu ita suka kalla, Malan ne ya furta" Aa, ita din aminiyar NAHIDT ce, tare aka kawo su a kame da ake yi"
CHIEF OF ARMY ya ce" Thats good, ka ga ka aurawa d'anka yarinyar cen, ina kyautata zaton zai samu gata in sha Allah"
Sake kallonta sula yi, haka kuma suka kalli wajen da su Hamza suke sunna ta sake rungumar junna da Hamzan yana ta talabar kumatunsu yana mai yi masu furucin su yi hakuri su daina kuka, in sha Allah damuwarsu zata gushe gaba dayansu, dan an daina aurensu a yau ba damuwa, Allah zai basu abokanan rayuwa masu albarka, gashi ya bayana a garesu zai zamto uwa, ya zamto uba a wajensu, zai zamto gatansu, zai tare masu dukan wata rigima ko raini, zai hanna a zage su , zai daki du wanda ya nemi ya dake su, shi murna yake da ya same su , kuma babansama zai rike su kamar shi ya haife su domin dama so yake yi ya samu wasu y'ayan gashi Allah ya karra masa ai, su kyale wa'incen masu bata farin cikin mutane daga su har yar uwar tasu, su yi shiru su daina kuka haka Allah ya hukunta
A sanyaye Malan ya ce" Tabas haka Allah ya hukunta, na jima ina gannin lamarin launin Kadarrar bayi ciki harda tawa ta jarabawar rayuwa Alhmdulilah, aman ta Shuwwar, ta shuwwar tana bani tausayi ainun, ina mai taya shuwwar adu'ar Allah ya sanyaya mata jarabawar rayuwarta ba dare ba rana "
Sake juyawa Chief of army ya yi yana kallonta, mugun tausayinta ne ke tsirga masa har cen kasan zuciyarsa
Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya fara fita ya bar Baban Hamza zuwa ya sanar masu abinda suka yanke
A lokacin da ya fito ya ga dumbin al'umar da suka saka jikinsa daukan yamyamyam
Da mamakin tarin mutanen da suka taru yake karra bin mutanen da kallo wa'inda idannuwansa suka kasa gannin karshensu , a cikinsu kuma ya ga manyan malamai, ya ga datijawa, ya ga matasa, uwa uba sojoji babu kalar hular da babu
A hankali ya kai dubansa wajen da ya kula sun fi zagayawa hakan ya tabatar masa cewar a cen yake
Murmushi ya yi mai sanyi yana komawa gefe ya ciro wayarsa ya samu ya fita a cikin mutanen daidai mai rike da 🔊🔊🔊 ya fara sanarwar cewa a shirya kowa ya zauna za'a gabatar da daurin aure
LIEUTENANT GANARAL ya dan tabe bakinsa yana mai sake bin mutanen wajen da kallo da bakin gilashinsa a kasan zuciyarsa yana ayana' In ba malan bahaushe ba, a kasar da ake kawo hari yan bani na iya na shiga da boom sunna watsa al'uma, shine akai wannan tarron mai cinkushewar nan aka cinkushe kowa da babar riga, yanzun ka dauki dan dutse ka furta attakhabir ya jefa kusa da liman din cen da babu abinda zai iya aikatawa da ya wuce diban babar rigarsa ya diba da gudu ko ya sume kafin ta tashi da shi din, shirme dai ba zai karewa malan bahaushe ba, daurin auren a yi shi a cikin masalaci mana a watse?'
Zazaunawa aka yi, du aka samu nutsuwa inda suka shiga gabatar da daurin auren da su rabe raben cingam da komai
A bangare guda kuwa CHIEF OF ARMY idannuwansa ke lumshe yana sauraron maganarta a nutse take furta" Har ka sa na ji kunya, wani irin neman yardata? A kan yaron da kaine babansa?, Dan Allah me na yi maka ne da sasafe haka ELHAJ ?"
Murmushi ya sauke hadi da ajiyar zuciya ya datse kiran bayan ya furta mata kalamai masu daraja ya maida dubansa wajen tarron al'umar nan ya daga kafarsa da dan sauri ya dawo jin ana shafa fatiha wanda hakan ke nufin aure ya dauru kowa na iya tashi
Kamar jira yake ana shafawa shi ya fara mikewa, sai dai gannin Father ya nufo da sauri shima ya sha babar riga fara yana masa alamun ya zauna saman kujerar da yarensa suka bashi ya koma ya zauna sannan ya karasa wajen da yake zaune yana kallon fuskarsa a nutse ya ce" MUHYIDEEN, ni kuwa idan na yanke wani hukunci a kanka yanzun zaka iya yi min biyaya kuwa?"
Kai, watau Father dinsa ya cika son saka shi magana ba lokaci walahi, ya fi sau a irga suke irin haka, kuma fa wani yanke hukuncin saima an yanke ake fada masa sai a biyo ta bayan layi da shi, duda ya tsargu kwarai da gaske da tambayar da akai masa a wannan wajen a irin wannan lokacin, aman sai ya dan kafe shi da ido kafin ya dan gyada masa kai yana sake waiwaige ko zai ga abinda Father ke son saka shi
Murmushi ya yi yana fadin" Ka matso kusa da wajen daurin auren nan yi sauri taso ka matso
Da kallo ya raka bayan Father a lokacin da ya ratsa da sauri yana dukawa wajen datijawan nan da abokinsa da malan dake zaune zagaye da goron da aka karkasa ana ta rarabawa
Bakinsa ya karra dan dantsewa yana ayana' Allah , Allah ka sa wani tsagera aka sama min da safiyar nan na ci uwashi na hutama zuciyata!', tunanin haka da ya yi saka shi mikewa da kwarin gwuiwarsa da kakinsa ta sojoji a jikinsa ya matsa da kyau ta yadda zai damki mutun (😌)
A nutse bayan Father ya gama gagaisawa da su ya ce" Ku yi hakuri, na shigo kai tsaye, Malan, Aban su Hamza, Aminina idan har ba damuwa ina nemawa yarona auren SHUWWAR"
Daga Malan din, har sauran al'umar kafeshi sukai da ido, bama kamar Ganaral da ya san waye yaron nasa da mugun mamaki baki bude ya ce" Elhaj, kana nufin SIR?"
Kai ya gyada yana dan waigawa ya ga ashe ya dan matso din kuwa, hakan ya sa ya ringa hamdallah a zuciyarsa
Malan ya kai dubansa wajen da Baban Hamza ya nuna yana fadin ga wanda ake nemawa auren
Tsakani da Allah sai da gabansa ya fadi gannin soja a zaune, sojanma LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY? Soja wa Shuwwar? Ji ya yi hankalinsa ya fara tashi bale da ya kula gaba daya dan halaci irin nasu shi suka zubawa ido, kuma shi suke jira ya bada amsa
Watau shi a rubuce zai bada labarin wacece Shuwwar , domin idan hankalinta ya tashi ko a gabansa hali take rabawa, uwa uba a kan maganar soja?
Yar zufar daje gaban goshinsa ya saka tissu yana sharewa a hankali ya gyada kansa yana mai fitar da iska ya furta" Na bada in sha Allah, Allah ya sa hakan shi ta fi zama alkhairi"
Murmushi Father ya yi ya mike ya juya wajen da MUHYIDEEN yake ya dan rage muryarsa sosai ya ce" Ya dace ka sauka kasa ka ga sirikanka ne fa a saman tabarma kai kuma yaranka sun kawo kujera kuma sun hanna kowa hawa sama sai kai?, Yanzun dai bani sadaki dukan abinda ya samu kasancewar bamu fito da shirin hakan ba"
Da mamaki baki da hanci ya saki yana kallon Father, muryarsa ya dan gyara ya bude bakinsa ya ce" Sadaki?"
Father ya gyada masa kai
A hankali ya sake fadin" Aure zaka yi ne Father?"
Sai da CHIEF OF ARMY ya bude ido da baki yana kallonsa kafin ya girgiza kai ya ce" Aa, ba ni bane, dan da na haifa na kuma isa da shine zan daurawa aure, watau kai"
"Ikon Allah" ya fada kasa kasa sosai yana sake maida dubansa wajen mutanen, 'Watau na zo na kama ne za'a kama ni?' ya sake ayannawa
Fuskarsa ya harhada yana dan kallon Father ya ce" I'm sorry Dad ni ai ban fito da ko sile ba"
Father ya kalle shi kallo irin na ni zaka fadawa haka? Ya san da ya san baya fitowa aljihunsa ba nauyi , dan a rayuwa shi din tafe yake yana bada sadaka a wajen da ba'a sanshi ba, jakar kudinsa koda yaishe zai fita a hannun daya daga cikin yarensa take, aman ya ce bai fito da ko sile ba kau?
Dan murmushi ya yi yana fadin" Gashi kuma daurin auren ya kama ne walahi, bara to mu gani"
Ba zato ba tsamani ya ga Father ya mike tsayinsa ya fuskanci wajen sojojin nan dake zazaune da wa'inda ke ta yawo sunna ta aikinsu na bada tsaro
Abinka da sojoji Father ya bude muryarsa sosai yana ihun" SOLDIERS!"
Duk wani soja dake wajen nan, da wanda ya yo ritaya, da wanda yake bakin aiki da wanda vai saka kaki ba sai da ya ganshi ya mike tsaye jikinsa na tsuma ya ja ya daka kafa daya a kasa ya dora hannunsa a gefen kansa da alamun sarawa cikin kuwa harda MUHYIDEEN, hakan ya sa dukan wani farar hula zuba ido da mamaki da birgewa yanna kallonsu
Muryarsa ya sake budewa da karfinsa ya ce" Dukan mai naira a aljihunsa Koda naira biyar ce kumu harjada solidarity mu hada sadaki za'a daura auren LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY gashi bai fito da ko sisin kwabo ba!"
Idannuwansa da ya zarro zaka ce yadosu ne zai yi kasa
Da mamaki ya ringa kallon yadda nan da nan wajen ya rikice da hade haden kudade na mamaki daga aljihun kowani soja , domin kowa abinda yake aljihunsa ne yake cirowa yana hadawa kafin kace meye wannan an cinbuzo kudi na mamaki a babar riga a kawo gaban CHIEF OF ARMY , sannan sun layu da fuska ta fara'a da farin ciki shinfide a kan fuskokinsu