← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 138

Sashe 113

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'anya zan iya wannan rigima kuwa?, Shin me yake rabata da mazan da take aure? Idanfa nima sai ta gama rikeni ta yadda babu kai iya kwatata bayan ubangijin da ya hakiceni sannan zata nemi barina?, Anya zan iya hakura da wannan.......?'

A hankali ya sake maida kansa jikin kujerar yana girgizawa kansa kai ya shiga ambaton sunnan Allah, dan ya sani ne wannan kokowa da ta zame masa ba ta gwa da gwa ba tabas sai ta cin masa, ya tabata sai ta kaishi wajen da babu mai iya fitar da shi'

Tunda ta shiga ta darwaye butar shayi ta zuba ruwa ta jona ta samu kanta da jinginar da bayanta a jikin garun kicin din

A hankali ta tsunduma a kogin da zata iya kiransa na bege , wai dama haka ake ji? Yanzun wajen sai kaikayi yake yi mata, yai zafin bai kai na ranar nan ba, yau da sauki sosai zama ta iya cewa wani mahaukacin dadi ta ringa ji a dukan gabobin jikinta

Ya salam, duniyar da ba soja gaskiya ba dadi, du garin da ba soja basu ji dadin rayuwarsu ba, kai Allah ya yiwa soja albarka ya karra masa lafiya da fasaha.....ita kam dukan mai zagin soja bata tunanin zata iya dubansa kuma ta kyale shi gaskiya ( 🤣 kuma ke yau? Sojan Shuwwa? Soja fa?)

Karar da butar ta fara na nuni da tana tafasa ya farkar da ita , da dan sauri ta karasa ta cire sannan ta hada masa shayin mai kauri mai kanshi sai turiri yake

Tana fitowa ta sake dakatawa wajen abincin da ya dace ace an masa cin kari aman yanzun har sha biyu ce ta gita su kansu basu sani ba ta wuce ba, kai jama'a dama yaka abin yake?

Bayan ta jera masa komai ta dawo wajen da yake din nan a haka ta same shi

A sanyaye ta furta" Ga abincin "

A hankali ya dago yana kallonta sanann ya kalli abincin da ra ajiye
Ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zamansa yana gannin yadda take zuwa
Kunshin hannunta yake ta kallo tamkar bai san menene a hannun nata ba
Dan murmushi ya yi domin kunshin yai masa kyau sosai da sosai , ya janyo plate din abincin ya yi Bismillah ya fara ci

Itama nata ta ja ta fara ci din tana kakauda kai , sam ta kasa kallonsa ido cikin ido, bata san dalilin da yasa take jin matsananciyar kunyarsa har haka

Aa hankali ya ce" Zaki kuma guduwa ?"

Shinkafar da ta saka a bakinta ta idasa cinyewa ta ce" Ina?"

Dan kasa kasa ya kalleta ya dan juyar da kansa sannan ya ce" Idan na kuma kokarin zuwa wajen da yake halalina, zaki barni na je kuwa? Ina nufin idan na shirya sakawa ba zaki gudu ba?"

Kwaruwa ta yi ta shiga tari ido a waje tana kallonsa kafin ta cire kanta ta warci mug din ruwa ta mike da wata irin katsananciyar kunya ta yi dakinta a bayane tana furta" Innalilahi na shiga ukuna".....

Da kallo ya rakata na mamakin me hakan yake nufi?, A hankali ya fan muzguta ya furta" KUNYA?....... Wauhhhhhhhhhhh"
Ya yi wani murmushin yana girgiza kansa ya ci gaba da cin abincinsa

Sai da ya gama ya koma dakinsa ya yi wanka ya cenza suturarsa ya fito da niyar tafiyarsa

Har ya kusa fita ya samu kansa da tuna kashedin da ta yi masa na jiya kan ya tafi bai fada mata ba, ba dan tsoro ba sai dan tsaro ya dawo ya dan bubuga kofar
Jin kamar tana sallah ne ya bude bakinsa a hankali ya ce da ita zai fita sai ya dawo

Tana jinsa a labe har sai da ta tabatar ya fitan sannan ta bude ta fito tana cike da jin kunyar sake gaduwa da shi kam ita dai
Bata zauna ba sai da ta tsaftace dakinsa sannan ta sake fitowa falonta ta duba gyaran da sukai mata sannan ta kile ta je ta yi wankan itama ta yi sallah ta kuma komawa kicin, suka hadu da masu aikinta suka yi girki sasauka sannan ta salamesu ta dawo falonta ta kwonta ta kunna TV da kuma wayarta sunna ta hira da yan uwanta kan dinkunnan da ya dace a jejere su saka saboda auren hajia baba watau Nahidt

Tana nan kwonce sai dai ta zuba tsumin da aka rakota da su ta sha sosai sannan ta sake komawa ta ja mika tana dafe mararta da bata san me yasa ta cika yi mata nauyi ba yanzun ta dora da harkar wayarta har magariba ta sanyo kai sannan ta mike ta sake kunna turaren wuta ta shige dakinta dan gabatar da sallah sannan ta yi wanka ta kimtsa kantaALK'ALAMIN KADARATAH

Na

*Sajida*

Page

6️⃣5️⃣

*yar* *uwa idan* *kina* *da*
*matsalar daukewar ni ima kuma kin rasa hanyar maganceta,to ga dama ta samu ki samu abubuwan nan guda uku, ganyen zogale,cucumber, da kuma madarar ruwa, yadda zaki hada shine ki samu ganyen zogalenki mai tsafta danye fa amma ki wanke shi sannan ki dauko cucumber dinki ya danganta da yadda kike so inma dayawa zakiyi ki sa a fridge ko kadan kike so iya wanda zaki sha a take duk yadda kikayi dai yayi amma fa in akwai matsalar watu zai iya baci gaskiya so idai zaki sha din anaso ki juye madarar ruwan gaba daya a sha daya kenan to akwai kuma wadanda su basa shan ma ko wace irin madara wannan suma zasu iya hadawa su sha ba tareda sun sa madarar ba,wannan hadin yar uwa wllh ya nada matukar kyau sosai ki jarraba ki gani sati yayi yawa zaki na mamakin kanki, ke oga ma sai ya ce sweet heart miye sirrin ne*😍😍

*zakuma ki iya gyara danyen zogalen ki kidaura shi akan wuta inya dahu ki tace ruwan a gefe inya huce ki sa zuma ki hada ki gauraya zaki iya sawa a fridge ko ki sha ahakan ma*

*emergency ne yar uwa ki jarraba ki gani Allah yasa mu dace*😍
(Wannanma Alkalaminta ne, my kyauta daga Allah🥰)

Kamar yadda ya shigo jiya, yauma ya dan cika daren kadan sai dai bai kai irin na jiya ba, danma harkar takardar katin gayatar daurin auren da suka buga da sunna irin na garaje da suka dora wanda zasu tura shi masarautar garin su gayaci sarkin garin da dukan wani wanda suke cike da zargin shine ya aikata haka wajen daurin auren Yar Chief of army duda yawanci an san sabon chief of army din nan dai bashi da Y'ar da ta kai haka aure, aman haka suka saka ta gidan sarautar da sunnan Nahidht MUHYIDEEN MUHAY zata auri atajirin malamin nan watau MUHAMMAD ranar asabar ne daurin auren watau yau saura kwana uku rak a daura shi, hakan ya sa a yau yau sai da ya tada mutun aka tuka shi dan a tabatar masa da an saka sakwani a hannayen wa'inda ya dace au samu, watau ba zaku gane bane, an matukar wulakantar da dan Adam ta yadda yake so komai ya kasance a lokacin da ya dace ya kasance!, Zai aikata aiki ne irin na kan uwar wa da wabi!, Jifan da zai auna baya tunanin kan wani zai sha!,

Sai da ya kimtsa kansa da ledar da ya shigi da ita wace du idan ya kalleta sai ya ji wani dasss a zuciyarsa kafin ya mike da niyar zuwa dakinta, jin shirun ya yi yawa

Sai dai bai idasa hakan ba sai gata ta kwonkwasa, ba tare da ta jira amsa ba kawai ta turo da yar muryarta sama sama kadan ta ce" Salamu alaikum da mutun kuwa?"

Shiru ya yi yana kallonta, sannan ya bu carbin dake hannunta da kallo fari kal irin na yatsar nan mai kyalkyali, carbin masha Allah yai masa kyau, tana sanye da zumbulelen hijabin da haka kawai ya raya a ransa abinda ke kasan hijabin tabas bai taka kara ya karya ba

Daga saman dardumar da ya gama shafa'i da wuturi yake kallonta, itama din sai da tai masa kallon kurilah kafin ta yi yar dariya tana fadin" Yalabai wannan lebe naka wai hala wani abu kake goga masa? Allah dai ya sa ba na abin bane"

Ya gama sannin tana son cewa ba na shan giya bane, hakkan ya sa bai wani kulata ba, har ta karasa ta zauna saman gadonsa da ya sha sabuwar shinfida ta farar abin shinfida ta kaikaita zamanta tana fadin" A duniya, na tsani na yi shinfida na kuma hau, ji nake gaba daya raina na kuna idan na kashe kaina na yi shinfida kuma na hau, yalabai kaima kana jin takaicin nan ko?"

Sake kallonta ya yi ya ga magana fa take yi, aman kuma carbin dake yatsarta tana ja, hakan ya saka shi sake kureta da kallo a hankali ya ce" Me kike ja ne?"

Carbin ta kalla ta yi dariya tana fadin" gaskiya da yawa, aman na fi jam Astagfari dan tana daukan nauyin adu'o'in da yawa Yalabai, sannan salatin annabi dan kaunar da nake masa, sai kuma ya latifu saboda bana so kudi ya yanke min yalabai, Allah dai ya sa mu mutu cikin kudinmu da lafiyarmu da imaninmu kuma mu je cen mu samu aljannah, kai Allah amen "

Bakin da take sake surutu da su shafa Allah amen din nata duka ya bi da kallo , nan take ya shiga wasi wasin anya kuwa zai aikata abin nan da ya wuni da niyar shi a yau da wannan yarinyar mai aljannu? Anya kuwaa wannan zata iya tarbiyantar da wani ?, Ko kuma riketa yake yi abinsa Idan ta sama masa sai ya samo wata abokiyar zaman da za ta ringa ba y'ayan tarbiya?

Gabansa ya nuna mata ya ce" Zo nan"

Wajen da ya nuna mata ta kalla , ta diro daga saman bed din ta taho tana fadin" Ko na kawo abincin nan ne? Nima ban ci ba ai"
Chapter 113 · 0% Book details