← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 138

Sashe 29

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kasan zuciyarta ta ayana' fiye da tunaninka, domin na fika zumudin son gannin ranar nan, abinda na koya shine rike zumudin hakan a cikin zuciyata domin a aure hudun da na yi na bayana ban ga alkhairin hakan ba'
A bayane kuwa sai ta ce" Awani? Na me kuma my Hamza?"
Ido ya dan zarro ya ce" To wai me na maki da zaki rama ne my kanwa? Yanzun sai kice bakya duba agogo du wucewar minti kina ayana saura yan awani? Kin ga yama ta yi fa, daga safi ta waye saura kwana daya tak, daga an yi wani wunin sai a fara irga yan awanin da zasu rage Hamza ya zamo mujin Shuwwa"
Murmushi ne ya subuce mata hakan ya sa ta kashe kiran da sauri tana sauke murmushinta a bayane
Mikewa ta yi tsaye ta shiga dan takawa hakan ya sa duwawunta dake cikin tawul jujuyawa a bayane ta ce" Nd shuwwa ta zamo amaryar Hamza.....wayo Allahna ashe za'ai min auren gata nima kuma har a tarra al'uma irin haka? Wayo farin ciki kasheni?"
Tana sambatun farin cikinta wani kiran ya kuma shigo mata wayar
Du a tunaninta shi din ne, domin kira a wajensa har ajiye wayar take yi ta ki dauka sai ya kirayi ta Nahidt yana fadin Allahn da ya sa in bakya son jin muryata ai ga Nahidt ga Fauziya sai mu kwana muna labari sai dai haushi malama!
Number da ta gani ta sakata dan kura lu'u lu'un idannuwanta tana kallo domin bata san number ba, kuma ta sha dawowa ta tarda misss call da number an yi kiranta bata kusa
A hankali ta daga kiran tana karawa a kunnenta ta yi shiru
A sanyaye ainun ya ce" Aure bai haramta tsakanina da ke ba Shuwwar, bai haramta ba, na zo yau na samu Malan dan na fada masa cewar na je na yi bincike ina iya aurenki yake fada min ya maki miji?, Shuwwar ni ban san me na yi nake fuskantar jarabawar sonki haka ba, mahaifina ne ya ja min ko?, Shine ya ringa fade fadensa har Allah ya kama shi ta kaina ko?, Shuwwar wani zaki sake aura ya sake ki kina ji kina ganni bayan kin san ni ba zan taba sakinki ba?, Shuwwar tunda na gila karyar ni mijinki ne a gaban mutumen da na san a lokacin da ya yi niya da yanzu sai dai tarihina kina tunanin zan bari wani ya raba mu ne?, Haba my Shu dan Allah ki cewa Malan bakya son wancen ni kike kin ga in ba haka ba zaki karra yin wani auren a sako ki ne"
Da dan karfi ta ce" ba Amin ba , kai Abdul tsaya ka ji na fada maka gaskiya, ka ga da kai, da babanka, da sojan nan da kake alakanta kanka da jarumi dan ka yi magana a gabansa na tsane ku!, Ku shafa min lafia ka ji? Mijina da zan aura kuma yana sona, Alhmdulilah ya san wacece ni kuma a haka yake son abinsa, kai barama ka ji ka kuma kirana walahi sai na wahalar da rayuwarka, da ace ban yi rantsuwar ni da soja ko police sai a lahira bane da kai kararka zan yi su rufeka na huta!, But yanzu ina mai gargadinka kan ka shafa min lafiya ka ji bayanina?"

Tana gama fadan ta kashe tana zabga uban tsaki a bayane ta mike ta shiga fitar da nikaf dinta da rigar da take sakawa dan karra dumama dumin jikinta domin a yau zasu fara kunshi da kuma alawa dan cire gashin jikinta da ya kwonkwonta lumbuk, tana yi tana mita da fada a bayane tana fadin jarabar banza da wofi sai ka zo ka sa a sakeni, yo in aurena ya zauna sai na tarda mai shinkafa na ce da shi to azalumi na auru yaya ranka?😂

Babar ranar
Kwaramniya ke tashi ta manyan almajiran malan dake sake kimtsa kofar gidan da aka saka manya manyan runfunna har kwaya hudu , irin dankara dankaran nan
Mutanen anguwa tuni suka ringa cika gidan malan tunda garin Allah ya waye dan karra ba idannuwansu kalaci da mamakin lamarin Malan din, domin a cikinsu kalilan ne suka dauki hakan da fuskar fahimta harma suke adu'ar Allah ya sa wannan din idan aka yi shine na dindindin

Dankara dankaran sojojin dake zagaye da anguwar kuwa idan ka gani sai hankalinka ya tashi, tamkar zasu je dan jijibin yaki ne domin tuni Tsohon ganaral da amininsa Chief of army, da aban Hamza suka samu karasowa a yanzu da yake karfe takwas sunna baban falon Malan na alfarma sunna karra tataunawa dan idasa shirya lamarin daurin auren, sannan sunna jiran matan da suka zo da sha tara ta arziki na akwatunnan amaryar su shigo su shaoda masu cewar sun bada kuma an amsa

Wayar dake hannun Chief of army ce ya sake bugawa a karro na bakwai, zuwa yanzun an daga sannan da muryar da ya amsa ya saka shi yin dan Murmushi yana fadin" Kai fa ka ce da kai za'a daura auren nan, kuma ka ga mu tuni muna tare ka da san aminina ne Ganaral, me zai hanna na jiyo jiniyar sojojinka kun karaso anguwar ne? Ka zo son zan ji dadi idan ka zo"

Goshinsa ya tatare yana mamakin lamarin Father dinsa, yanzun har sun je wajen daurin auren da aka saka karfe tara za'a daura shi? Eh lalle yaron nan dan gata ne, watau sun je su yi jiran bakinsa ne ko?

Dan nishi ya dan fitar kasa kasa ya ce" Zan zo "

Chief of army ya yi yar dariya yana fadin" Ina duban hanya "

Daga nan ya kashe yana fuskantar baban Hamza ya ce" ka ce min tun zuwan nan da ya yi sau daya da na ce ya je bai kuma komawa ba?"

Daria ya yi yana fadin" Haba aminina kaima ka san zuwanma da ya yi dan maganarka ce ai, ka ga ranar farin cikin da na yi kuwa? Allah dai ya kara girma aman garin nan ana tsoton Lieutenant ganaral walahi, baka ga yadda ake kwasa tsakaninsa da mararsa jin magana ba"

Shima yar dariyar ya yi ya ce" Ai ana cen ana kwasa da mamansama, aure fa aka daura masa sau biyu kadai ya je , kuma a zuwan nasa biyun sau daya tak suka hadu da matar, cewa ya yi mahaukaciya ce sai tana kafeshi da ido kamar mai farfadiya, kai dai ana nan ana fama da rigimarsa "

Ire iren hirar da suke ta yi kennan sunna shan dariya ga zazafan kunnun fulawa da ya sha uban madara da kayan kanshi yana turiri yana ta tashi a gabansu an zuzuba masu a manyan kofofi na kwalabe , ga sanyin AC da falon ya dauka kai abin dai sai hamdallah kawai

A cen cikin gida kuwa a falon matan Malan bayan an karbi kayan amaryar matar Malan uwar gida itace a tsaye a gaban lamarin, domin a lokacin da malan ya yi tsaye ya dubi idannuwanta ya nuna mata yin hakan shine farin cikinsa ya saka ita kuma mikewa da dukan kokarinta da zuciya daya ta amshi su Shuwwar harma take hidima da su
Ko a yanzun matan da suka zo da akwatunnan sun samu tarba ta mutunci har sun cika da mamakin gannin hakan duba da yadda dan uwansu ya fada masu cewar ko me suka tarar kar su saki su nemi wulakntar da yarinyar, idan har suka ga wani abin batanci a tare da ita kar su manta d'an yar uwarsuma yana da kashi a cikinsa a haka suka amshe shi suka nuna masa so har zasu bashi y'a
Su abinda suka tarar kwata kwata basu ga abin tsatsamta ko na wulakanci ba
Sai da aka gama zube akwatunnan da suka girgiza matan daje falon Nahidt ta fito da waya a kange a kunnenta tana amsa Hamza dake shaida mata suma sun taso da jama'ar daurin aure sun nufo gidan Malan din , hakan ya sa ta shigo falon tana murmushin da ya sake fitar da kamaninta sak sak sak da mahaifiyarta, domin idan baku manta ba Nahidt ce ke kama da mamansu, Shuwwar kuwa ta dauko kamani da mahaifinta wanda shi har suka rabu da shi ya ki jinnin ya ji an ambaci sunnan kasar nan, mutane da yawa kan cewa ai kurciya akai masa wada ta fitar da shi daga kasar kwata kwata harma ya ki jinnin maganar kasar bale mararin dawowarsa cikinta

Idannuwanta ne suka shiga cikin na matar da ta mike tsaye a tsorace ta kafeta da ido
Bakin matar na rawa tana nuna Nahidt ta ce" wannan wannan wannan wacece?"

Amaryar Malan da ta san dama a rina, harma zuciyarta ta gama dumewa da farin cikin gannin haka ya fara bayana, a zuciyarta ta ayana'an zo wajen, dama na san wani sai ya gane da wannan karuwar ce zamu aurawa danmu kanwarta?' hakan ya sa da gagawa ta ce" Wannan? Ai yayar amaryar ce, sunnanta NAHIDT, gidansu a nan baya yake shi Malan din ai taimaka masu ne yayi duba da ba tare da iyayensu suke zaune ba" (Dan adam kennan, domin ba zan ce malan bahaushe kennan ba dan kuwa kaf duniya akoy masu irin halayen nan a kowani yare, hanyar da zata bi ta hanna farin cikin wani take nema dan kawai tana jin tsoron rabarta da farin cikin ke iya yi ya saka ta zama tamkar mahaukaciya)

Dukan mutanen falon da mamaki ita suke kallo da wannan dogon jawabi haka
Da sauri matar ta sake kallon NAHIDT da ta yi mutuwar tsaye cikin shagarta ta watsetsiyar farar shada ta sha zubi blue mai haske da fari hakan ya sa shadar kara fitowa sosai take kyalkyali

Matar ta kai dubanta da sauri kan hannun da ya riketa wace ke zaune a kasa muryarta kasa kasa ta ce" Gimbiya ki zauna, nima tunda na ga wucewarta tun dazun sai da na mata irin kallon nan, aman kema kin san ba zai taba yiwuwa ba, ki zauna kin ji?"
Chapter 29 · 0% Book details