← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 138

Sashe 14

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A sanyaye ta ce" Yaushe rabonka da mamanka?"

Dagowa ya yi yana kallon hannunta ya ce" a kadan an yi shekara biyu Mama"

Idannuwanta ta lumshe tana hanna kanta bayanar da bacin ranta a hankali ta ce" Yin hakan ba kyautawa a ciki, dan ka saki y'arta sai kuma ka yanke zumunci da ita? MUHAY Ouseinata ce fa"

A nutse ya ce" Mama, Fareedanta ta san aure ya haramta tsakanina da ita dan saki uku ne aman kuma take damuna"

Mamansa ta ce" Baka san Fareeda ta yi wani auren ta rabu ba? Dan ta kasa zama da wancen mijin ta fito? MUHAY tana sonka, me zai hanna ka maida yar uwarka dakinta?"

Fuskar Maman nasa ya kure da kallo yanzunma, a kasan zuciyarsa kuwa yana ayana' da kin san sirrin dake boye a cikin guguwar alkalamin kadararki yah ke mahaifiyata, da zuciyarki ta buga a yanzu a take, sai dai zan ci gaba da yin iya yina dan gannin na kare ki da jin labarin da zai girgiza tunaninki Umunah.....in sha Allah ba zan yarda wani abin tashin hankalin ya same ki ba mudun ina iya hannawa'

A bayane kuwa sai ya yi mata diffff
Ta sake jan maganar, ta yi nasihar , ta yi rarashin, ta hada da fada fadan aman tunda ya ja bakinsa ya yi shiru a kan maganar sai ya zamto tamkar kurma a gabanta

Kanta ta cire tana fadin" Na rantse maka da Allah idan har baka maida ita ba, to fa sai dai ka samu wata ka aura, babu abinda zai saka na yarda na zuba maka ido da shekarunka da aljihunka da lafiyarka ka zauna ba mace a gefenka, domin ka kai minzalin da Mace taka ko ba taka ba mace take a gabanka!"

Shi kam yau harda yaren nan da ake cewa kunya mamansa ke son bashi
Hakan ya sa muryarsa ciki ciki sosai ya furta" Yinwa nake ji Mama, kin ga cikina ya hade da bayana sosai, inaga Yinwar ta kamani da yawa ne"

Duda ta san harda son kawar da maganar da suke yi ya saka shi sako maganar yana jin yinwa dan ya san idan kowani irin bacin rai take ciki bata wasa da cikinsa ne, ai kam sai ya ga ta dan zarro ido tana fadin" Sorry MUHAY, ina zuwa"

Daga haka ta mike ta nufi cikin bangaren da kicin dinta yake, hakan ya saka shi rakata da kallo yana murmushi sannan ya juyo da kallonsa bangaren TV yana mikewa ya hau saman kujera ya kamo duniyar labarai ya kafawa TVN ido yana bin dukan labaran da ake gabatarwa

Garzayo ki samu naki yar uwa a kan farashi mai sauki ta hanyar yin transfer ko tura katin MTN🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 thanx

Sajida ce💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 9️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Soyaya ke gudana a tsakanin SUDAIS da SHUWWAR
Tabas a dan kwanakin da ya yi yana kai kawo gidansu Shuwwar ya shaku da ita, uwa uba zai iya rantsewa cewar yana sonta har cikin zuciyarsa, du kuwa da irin abubuwan da yake dan fuskanta wa'inda ya yi masu uzuri ainun duba da sune kadai ke rayuwa da junnansu ba iyaye a gefe dole za'a iya fuskantar irin haka, sannan a anguwar mutun biyu suka zo masa da maganar ya fitar da kansa a lamarin yaran nan yan iska ne, sai ya murje ido duba da dan adam a yanzun ya auri mugun halaya na hasada da zagon kasa yana aikatawa dan uwansa ba tare da ya taka masa ko ya kashe masa ba, ya fi so ya ganka a wulakance hakan shine farin cikinsa ba dan kana tauye masa wani abu na rayuwa ba

Abinda suka tashi da shi a gidansu tare da matar mahaifinsa kan ta bashi y'a ya saka shi fitowa a mutun ya nuna ai shi yana da wada ya tsayar jira yake a sake yi masa magana dan ya gabatar da ita a nema masa aurenta

Ai kam mahaifinsa ya yi farin ciki da hakan, sannan ya saka ranar nema masa auren yarinyar bayan ya gama fada masa bayanan yarinyar marainiya ce tana zaune da yayarta ne
Kwarai mahaifin nasa ya yi tunanin yayar tata ai wata babar mace ce mai shekaru, hakan ya sa bai masa maganar danginsu ba, sannan ya nuna ga wajen wanda za'a je neman auren hakan ya sa mahaifinsa samun nutsuwa da maganar auren domin ko ba komai Malan sanane ne a kafafun redio da talabijin da muryar yadda addinin musulunci da wa'azi, saima ya dauka mijin auntyn yarinyar ne, watau mijin NAHIDT din ne

__________________________________

"Ki gane SHUWWAR, bana son abinda zai iya kawo damuwa a cikin maganar aurena da ke, SHUWWAR ina sonki, ina so ki zamto uwar y'ayana, ki yi hakuri yannayin da Aunty ke fita ta kuma dawo ne ke damuna, bana so sanadiyar haka wani abin ya je gidanmu, gidanmu dauke yake da mutane masu yawa, matan mahaifina hudu ne reras, a cikinsu babu wace bata dauke da irin nata halin , sannan a cikinsu wace ta fi kowace iya juya shi ce ta bani y'arta dan ina baban d'ansa na kiya domin bana son auren hadi, bana son aure a cikin familly dina, irin auren nan yawanci wahalarsa ta fi dadinsa yawa, zama ne na tauye junna, zama ne na mulkin junna, bale gidanmu ina gannin yadda ake so a yi da mahaifina danma shi din jajirtace ne wajen neman kariya a wajen Allah, ai da tuni an fi karfinsa an saka mu a uku" Sudais ya fada a nutse yana sake gyara zamansa a saman kujerar da yake zaune

SHUWWAR ta sauke ajiyar zuciya, tana sanye da jar riga doguwa mai dogayen hannaye , kanta yafe da dan kwalin rigar ja, ta sake bin dakinsu da kallo wanda yanzu auntynta ta dawo tun fitar sasafe da ta yi a gidan sai yanzu ta dawo daga yawonta kusan karfe takwas na dare kennan

Wata ajiyar zuciyar ta sauke a sanyaye ta ce" In sha Allah zan yi mata magana"

Murmushi ya yi yana fadin" To menene na yin sanyin kuma? Ko dai na bata maki rai ne?"

Da sauri ta girgiza kanta tana danne abinda take ji ta ce" Kaina ke dan ciwo ne SUDAIS"

Da kulawa, da tarin soyayarta, kamar yadda ya saba yi mata ya ringa yi mata sannu yana mikewa hadi da fadin bara ya je ya siyo mata magani, sai dai ta dakatar da shi tana fada masa tana da magani a daki ba sai ya wahalar da kansa ba, kasancewar dama karfe takwas ta yi a haka sukai salama ya tafi da damuwar gannin damuwa a fuskarta

Da ido ta raka bayan motarsa har ya bacewa ganninta kafin ta sauke ajiyar zuciya
Ji ta yi idannuwanta na cicikowa da kwallah, ta afka a tunanin ta yaya zata iya fada masa aurenta uku, a auren uku babu wanda ta tare ake yanka mata tikitin saki?
A yanzu da ya kwatanta mata cewa ahalinsa rufe suke da tashin hankali a tare da su sai ta karra jin tsoron fada masa magana makamanciyar wannan, ita da kanta takan tambayi kanta wai anya bata dauke da bakin aljanni da ake fadin yana lalatawa mutun aure? Anya dalilin yayarta na bariki kawai zai hannata auruwa ne?

Jiki a mace ta koma ciki
Tana shiga ta dauko wayarta ta dawo ta zauna ta shiga doka number Malan ba ruwanta da lokaciN da ya ja

NAHIDT dai ta kalleta sau daya ta maida dubanta kan series din da ake haskawa suke kallo a tare
Chapter 14 · 0% Book details