← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 138

Sashe 9

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido ta kikiftaa tana kaiwa wajen madubin dakintaa ta ce" Wani irin toh, ba toh ba zaka ce min, ka fada min sone take ta kashe min kai, ka fada min yadda abin ya faru, yaya aka yi ka sani? Me ka yi mata? Wani ne ya aikota? Tun yaushe ta fara zuba maka kwalba a tea? Yaya aka yi ka gane kwalba ce ta zuba maka a tea? Shine suka zo suka nemi da na yi maka magana ita da mamanta? Ka fada min ni kuma sai na yi shara'a da su domin ba zan taba yarda da wannan ba"

Idannuwansa da ya rintse gam dan da karfi maman nasa ke magana ga dukan alamu kai kawo take yi ranta ya yi kololuwar bacin nan tana jero tambayoyin da ya rantse da Allah a yanzu dai da ya wuni bakinsa na haikar magana idan ya ce amsoshinsu zai bata sai an kwontar da shi a gadon asibiti koda baya so ya saku kansa da bude bakinsa da kyar ya ce" Mama kar ki shiga cikin gwagwarmayata da magautana, ni na tabata idan ba *ALKALAMIN KADARRATA* ne ya zo da zanen sai sun cin min ba sai dai su yi su gaji, abinda ba zan iya dauka ba shine a fara hakonki, inda kike din nan hankalina a kwonce yake, so plz ki huta mamanah"

Kasa furta komai ta yi a tsayen da take domin ya kashe kiran ne

Tana kokarin maida masa da wani kiran mesage ya shigo kamar haka" Dan Allah ki yafe min , kukan nan da kika yi kuma ki saka min albarka ki share hawayenki, zan zo gobe tare da Shugaaban kasa.......mamah i love you"

Daga haka ya kashe wayar yana saje mayar da idannuwansa ya rintse ya kwontar da kansa a baya yana jin kansa na sake sarra masa, gaba daya duniya ita daya ke masa irin haka abinta a lokacin da ta ga dama abinta, yanzun babar rigimar da yake tunanin mai kwontar masa da tarzomar hakan sai Allah SHine maganar kaurowarsa garin nan da aiki har na tsayin shekara biyar, yaya zata yarda da wannan kudiri nasa? Anya zata amince masa kuwa?........

I don't know oh LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY😍

Shin yaya wannan salon? Yana shiga cikin zuciyarku kuwa?

Maza garzayo ki samu naki a kan farashi mai sauki yar uwa NAIRA DARI UKU NE KACAL TA ASUSUN BANKINA, KU TUNTUMBENI TA NUMBER WAYANA KAMAR HAKA +22793811618 "na'💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 6️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

Idan ana dara fidda uwa ake ina gwanin wata ga nawa, duk inda kaji wane ba banza ba, Shin kunsan banbancin zaƙin suger dana zuma kuwa? idan baku sani ba kuzo na banbance muku, shi sugar zaƙi ne cau dashi bashi da ɗanɗanon zuma domin kuwa ita zuma tana wanke ƙwaƙwalwa, misalin Zaƙin hannun Rubutun wannan fasihiyar marubuciyar taku, Duk wanda yasan labaranta ya karanta littattafanta ba sai na basa labari ba, domin kuwa bata rubutun shirme rubutu take mai cike da nutsuwa da kuma fasaha, ingantaccen labari ne mai cike da ƙalubalen rayuwa, tsantsar Soyayya yaudara cin amana munafurci, ƙulla ƙulla, gami da Izza, *ALKALAMIN KADARRATA* labarine mai cike da sarƙaƙiya gami da wahalar warwara, zaren labarin a duƙunƙune yake gashi da kaifin gaske kaifin yankan zaren munafuki yafi kaifin reza da almakashi muni, zarene na zana mai yankar mutuwa, shin kun fahimci zaurencen kuwa? Idan baku fahimta ba ku kasance da ni *SAJIDA NIGER* a cikin wannan sarƙaƙƙen labarin mai cike da ƘIYAYYA labari ne mai jan hankali gami da nishaɗantarwa kun san alƙalamina baya rubuta shirme, ku biyoni cikin wannan labarin domin jin ya ɗanɗanon yake.

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Taro ne aka gabatar mai sunna taro wanda sai da yama ta yi aka ba al'uma damar fitowa ta kafofin sada labarai

A cikin wa'inda suka dauki wanka suka fito cikin gari harda SHUWWAR da yan uwanta
Kowace ta nufi hanyarta da irin kudirin dake cikin zuciyarta a lokacin da mutane suka fara watsewa a wajen taron

A hankali SHUWWAR ta gama yarda da abinda zuciyarta ta saka mata kafin ta juyo ta sauke dubanta a saman kwaltar tana karewa dukan motocin dake wucewa kallo

Cen ta hangi alamu na mota mai motsi na karasowa hanyar da take tsaye hakan ya sakata Sauke ajiyar zuciya a hankali ta saka kafarta ta shiga tsalakawa zuciyarta na dokawa tana tsale cike da tsoron kasadar da zata yi da tunanin Allah ya sa ta yi dace a kudurinta

Ido ta rintse sakamakon horn din da aka dana mata mai kukan gaske sannan aka danno kai kanta da tunanin ai zata kauce tunda shigarta ta farar abaya batai kama da mahaukaciya ce ita ba bale kuma yannayin fuskarta bai nuna makauniya bace ita bale a yi tunanin bata gani ba haka kuma bata ji ba Horn din da ake yi mata

Sai dai direban ya makaro a lokacin da ya kunnace mata wuri ne ya iya take birkin gaba daya hakan ya saka motar bada wani karra kuuuuuuuuuuuuuuuuu sannan ta daki kafafuwanta a da gasken gaske kafin take tsayawa inda Shuwwar ta yi tangal tangal ta saka ihu tana sakin jakarta da sabuwar takardar shedar yar kasa ce ita da ta saje domin wancen din ta nemeta ta rasa kadai a ciki ta fadi kasa sannan ta bita ta zube tana dauke numfashi a mugun tsorace domin bata taba tunanin wannan matukin motar zai iya sakin kansa har ya zo ya bigeta ba, koma waye wannan an yi dan airs walahi

Haya haya haya, kafin ka ce meye wannan, nan da nan wajen neman dinkewa yake yi da al'uma, hakan ya sa sojoji biyun da suka zo da gagawa bada damar yan uwansu su karaso su talafa masu dan a tsagaita cinkushewar hanyar domin Sir bai jima da keta hazo ba, a awa dayan da zai yi kuma a sararin samaniya bata cika bale ace ya sauka garin da zai je, karma ace har ya saukan ba zai iya dawowa da wuri wuri ba balema dawowar tasa ba wani abu ne mai wahala ba idan ya ji ana bukatar ya dawo din zai dawo ne yanzu yanzu ba tare da bata lokaci ba, gashi wanda yake cikin motarma baba ne na polisawa tare da masu bashi tsaro zai nufi gida ne hakan ya faru

Alamu take hange, kuma take ji a kunnayanta masu nuni da kamar wannan motar da ta kadeta ta soja ce

A lokacin da hannu ya kawo dan juyar da ita domin ana yi mata magana ne kan tana farke kuwa? Ta yi shiru, ta yi bakam tana saurare har sai da ta ga alamun hannu zai taba jikinta ta dago da sauri tana dan ja baya hadi da kurawa kakin jikinsa bakake irin na police ido lokaci daya tana fadin" Ka ga kar ka taba ni, ina wanda ya kade ni ne?"

Datijon da ya zubawa kyakyawar halitar ido ya yi dan murmushi yana fadin" Motocina ne suka samu hadari da ke yan mata, ina fatan baki raunata ba? Bismillah kawo hannunki na taimaka maki ki tashi"

Wani shegen takaici mai zafin gaske ne ya taso mata a cen kasan zuciyarta, yanzun du irin wannan wahalar da kasadar da ta yi da rayuwarta dama da mai kaki zasu hade ? Gaba daya sai ta ji hakan da ta yi bashi da anfani, wannan police din kuwa take ji a kasan zuciyarta da idan ta zage shi zata wanye lafia da ta aikata ta ji sanyi a kasan zuciyar tata

Da baya da baya ta sake ja tana girgiza kanta hadi da fadin" Ba sai ka kama ni ba zan iya tashi "

Tana fada ne tana son kama motarsa ta mike da kyar tana sauke mawuyaciyar ajiyar zuciya ta juya tana faman fadin" Ba sai kun rike ni ba ban ji rauni ba, aa ba sai kun rike ni ba ban ji ciwo ba....." A haka har ta samu ta ratsa mutanen ta wuce tana jin takaicin mai kaki a zuciyarta, ta tsani soja, soja bai yi mata ba sam, tana da dalilai na tsanar soja a rayuwa, soja yana da baban kamasho a cikin zanen kadarta!
Chapter 9 · 0% Book details