Sashe 52
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuwwar ta zaro ido tana kallonta ta ce" Kin k'auro ina?, Ni da nake shirin tafiya sai ki k'auro? Waye ya sauke kin ? Ba dai wancen dunkum d'in ba kau? Nahidt tsakani da Allah me yake yawo a kwakwalwarki ke kin san ai ba zama zan yi da mutumen nan ba, na san kin gane da ba zama zan yi da shi ba, shine zaki kauro kema?, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Nahidht ina yayan namu yake yo? Gaskiya sai dai mu koma wajensa tare, waima me yasa baki zauna a wajen yayan namu bane?"
Nahidt ta zaro idanuwanta da fada fada ta ce" Ke da barin gidan kun ci uwaku! Na ce kun ci uwaku!, Kuma da kike cewa wai ina yayanmu yana nan baima san na kauro ba, ni ba zan iya zama a gidansu ba sai kumbiya kumbiyar munafurci suke yana sando baya so a ga zai je dakin Fauziya, itama wai ni take jin kunya dan wani tsohon munafurci, ke ni gidansuma ba hayaniya walahi ni kuma na saba ana haya haya ko yayane kau? Shuwwa wai ko dai korata kike ne? Kudi kika yi kike korata ne?"
SHUWWAR ta rafka tagumi da hannayenta bibbiyu tana kallon yayar tata, wai irin abin nan take yi na daukaka karamin abu dan ta sakata a uku, wai da wani yare NAHIDT take so ta kwatanta mata dala dala waye MUHAY ne?, Da yaya take so ta kwatanta mata shi din ba kalar maza yan soyaya bane? MUHAY bai yi kama da wanda zai iya tatalin mace ko ya nuna mata yana sonta ba, domin shi matan suke yiwa haka ta yaya shi zai fara yiwa wata? Shikenan ita sai ta zama banza a banza kenan? Ta zauna da k'aton sai dai ita ta ringa rarashinsa shi ba zai rarasheta ba? Ai ba haka bane rayuwa gaba daya ba haka bane ba, ita burinta ta samu namijin da zai kasance mai yawan maimaita mata kalmar so, wanda zai ringa fada mata ba dare ba rana cewar itace so dinsa, wanda zai zama tamkar redio idan tana gefensa, aman wanna mutumen idan ya budi baki dan ya mata masifa ne, a kwana biyun nan da ta yi da shi zata iya cewa kyautata masa b'ata masa rai yake!
A hankali Nahidt ta ce" Da kin san abinda ya koro ni gidan nan da sasafe da baki nemi na koma ba, dan na san ranki sai ya baci Shuwwa."
Shuwwar ta cire taguminta tana kallonta ta ce" Wani abu aka yi maki?"
Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tana aron jarumta zata fara magana wayarta ta shiga kuka.
Kin dubawa ta yi domin a tunaninta yayansu ne ko Fauziya, bata san cewa Malan bane, da ta dauka ta gindaya masa sharudan da ta gama zanawa ranta sannan ta fada masa ya ji kunya wollah, ta danne wayar ta hade hannayenta ta ce" Abanki, Shuwwa Abanki ne ya ba matarsa waya ta zageni ta ce min karuwa?"
Gaban SHUWWAR ne ya fadi tana kallonta ta ce" Aunty, kalle ni, kalle ni, dan Allah ki fada min gaskiya kin ji? Aban nawa?"
Nahidt ta taba hannu tana fadin" To karya zan maki ne?, Na rantse da Allah tsakiyar dare muna maganarki da shi jiya kawai ya tashi ya kai mata wayar dakinta ta aniya duran ashar harda mamanmu da abanmu ta zaga, ta kuma ce min karuwa wai ina kiran mijinta tsakiyar dare!"
Zuciyarta ce ta fara tafasa a zaunen da take tana kallon auntynta ta dan wara zamanta tana kallonta ta ce" Nahidht, dan Allah ki rufa min asiri ki fada min yadda abin ya kasance kin ji? Kar ki saka na aikata abin kunya, domin idan matar nan ta taba ni ta kwana lafiya banda ke, bana tunanin zan iya kyaleta a yau Nahidt, me ya hadda ku waya da Abahna? Kin tabata shi ya kai mata waya? Abana ba zai aikata haka ba Nahidt, ki fadan yadda abun ya kasance."
D'auke hannunta ta yi daga na ta hannun da mamaki ta kalleta tace "Kai! Shuwwa a ganinki k'arya na fad'a? Zan miki karya ne dama ? Wallahi gaskiya nake fad'a miki, ke abun kunya fa Abanki ya riga daya aikatashi, sai dai fatan kiyaye na gaba kawai."
A zafafe take kallonta har ta muskuta ta gyara zamanta, wara k'afafunta tayi sosai irin zaman nan wanda ko masifa kake za ka ji dad'in jijjiga jikinka yanda kake so, hannun rigarta d'aya ya fad'i har ya sauko kan damtsenta, ba wai dan ta mata yawa ba sai dan kalar zaman da ta yi ta dafe hannunta d'aya akan cinye.
Kafin ta ce wani abu suka ji takon saukowarshi daga sama, da d'an sauri sauri yake saukowa saboda wasu takardu da ya ke son ba wa d'aya a cikin yaransa ya kai masa ofice.
Sam bai kula da tsiyarsu dan yi yayi kamar bai gansu ba ya nufi hanyar ficewa daga falon gaba d'aya, a yanayin neman fitina da rigima ba tare data gyara zamanta ba tace "Ji mana."
Har zuciyarshi bai yarda da shi take ba, dan haka ya wuce abinsa har ya kama k'ofa zai fita ta d'aga muryarta yanda zai ji ta ya kuma fahimceta tace "Ji mana malam soja."
Cak ya tsaya hannunshi na kan hannun k'ofar amma ya kasa jawowa ya bud'e, a saib'ance ya juyo ya zuba idanunsa akan ta.
Nahidt da ke kallon Shuwwa da mamaki ta rarako ido ta rufe baki mamaki na neman kasheta tace "Muhammadu Rasulillahi sallalahu alaihi wa sallam! Allah ka jik'aina tun man mutu ba."
Sassauta muryarta tayi a hankali tace "Shuwwa ashe dai haukan da na ji ana rad'e rad'i a kan ki gaskiya ne? Yanzu ke dan ubanki wannan d'in ne daga zaune kike kira da ji mana...Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"
Zunbur ta mik'e ta d'auki mayafinta tace "Bari in koma d'akina, wannan lamari na ki sai addu'a."
Kallon fuskar Nahidt yayi sanda ta kawo kusa da shi, d'an kaucewa yayi kad'an tare da sakin hannun k'ofar ta rab'a ta fita, saida ya ji ta rufe k'ofar ya dawo da dubanshi a kan ta.
Tasowa tayi tana gyara hannun rigarta daya fad'i ta kai kusa da shi sannan ta tsaya, kallon fuskarshi tayi tace "Dama ina so zan fita ne anjima, zan je wajen Abana."
Gefensa ya d'an kalla yana sakin murmushin gefen labb'a mai ciwon gaske, yayin da zuciyarsa ke ci gaba da raya masa duk Dady ne ya ja masa wannan wak'i'ar, amma yanzu zai wa tubkar hanci ta yadda za ta banbance aya da tsakuwa.
Damatsenta ya damk'a da k'arfin da ya san za ta iya d'auka, ihu ta saki na balakin daya ziyarceta amma sai ta ji bakinta ya sake yin d'uff ta kasa furta komai.
Gaba d'ayanta ya d'agata, irin d'agawar nan dake raba mutum da k'asa, kuma gata a hannayenshi ya rik'e damatsenta, wutsil wutsil da ta ji k'afafunta na yi a doron k'asa yasa ta duk'ar da kanta dan ta tabbatar wai gaske d'agata ya yi, duk'awar da ta yi ce ta sa hular kanta fad'owa har saida ta shafi fuskarshi kafin ta dire k'asa.
A kid'ime ta d'ago dan ta kalli fuskarshi ta rok'eshi Allah Annabi ya sauketa k'asa dan yanzu ta tabbatar a sama take.
D'agowar da ta yi da sauri ta sa gashinta daya fincike tsabar jijjigar daya fara mata ya rufe masa fuska, iskar bakinshi ya huro da k'arfi ya hure gashin daga fuskarshi, hakan yasa ta rintse ido saboda iskan daya huro mata a fuska.
Ido cikin ido suka kalli junansu wanda ita na ta suka rarako waje su d'an d'auki launin ja, bakinta dake bud'e alamar tsoro da firgita yake kallo, d'an tsurut da shi amma a haka take iya yanko masa magana iri iri.
Jijjigata yayi, kamar dai yanda zaka zazzage shinkafa ko dankali a cikin buhu, hakan yasa Shuwwa rintse ido kan ta ya shiga gigil gigil gaba d'aya jikinta na d'aukar jijjigar musamman k'afafunta dake sama, a k'asan mak'oshinta ta dinga fad'in "Aaaaaa! Kakkkkk...sssory."
Dakatawa yayi daga jijjigar da ya ke mata yana kallon fuskarta dan samun gamsuwar ta jijjigu ko da saura, daga tsayen nan ba tare da ya rusuna ba ya saketa da tunanin ta fad'o yanda zata d'an samu karaya ko shida ce a k'afa, amma ikon Allah sai ta fad'a kan k'afafunta amma rashin k'warin jiki da kuma dawowar da bata yi ba daidai saboda wannan shocking da ya bata, sai kawai ta yi zaman yan bori k'asa har saida ta sake lik'e idanunta gam ta dafe k'ugunta tace "Washhhhh!"
A hankali ta fara bud'e ido har ta bud'esu fes akan shi, zabura tayi ta Waro ido da zulumin me ye kuma na sunkuya gabanta yana kallonta, tsugunno yayi irin na maza yana k'are mata kallo yana so ta dawo hayyacinta sannan ya fad'a mata abinda ya ke son fad'a mata.
Marairaicewa tayi ta tank'washe k'afafunta tana sake rik'e k'ugunta da nufin ko ya tausaya mata idan yayi tunanin ya karya mata k'ugu.
Nunota yayi da yatsa fuskarsa a kausashe yace Ke! Kin san wa ye ni? Ke wacece da za ki dinga neman ja na a k'asa? Wane irin aljanu ne a jikinki? Idan na kirasu za su tashi?"
Hannu ya kai zai kamo gashinta da niyyar ya kira aljanunta ya ce su tashi dan su yi cin uwa da su ko zai ji daidai, ita kuma a tsorace ta ja baya tace" Na ce sorry ko."
Cak ya tsayar da hannunshi yana kallon fuskarta, kallon daya tsareta da shi yasa ta sadda kanta a marairaice tace" Ka yafe min dan Allah, in dai babu abinda ka sha ka k'yale ni haka."
_Ta kuma._😂💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 2️⃣8️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*