← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 138

Sashe 4

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Wannan labarin ba Free bane na kuɗi ne zaku samesa a cikin farashi mai sauƙi, Yar uwa karki sake a baki labari Hajia da abaki gara ki bayar karki manta da marubuciyar BAƘA CE, MAGE MAI KWANCIYAR ƊAUKAR RAI, KUTKALE, WATA KOKOWAR nasan kun san waɗannan littattafan da daɗin su, ku hanzarta biya ko da kuɗinka sai da rabon ka.*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰🥰

Da kakarfar Muryar nan tasa bai basu daman sauke hannayensu ba ya ce" HOW ARE YOU FELLINGS TODAY?! (Yaya kuke ji yau?)"

Gaba daya suka dauki amsa da fadin" Fine Sire "

Kafafuwansa ya wara da karfi ya doka ta dama a kasa hadi da mikar da hannunsa ya doki dayan da shi da wani gigitacen karfin kuwa ya furta" Me kuka ce?"

Ai yanzun da suka amsa gaba daya anguwar sai da ta dauka tamkar sun yi anfani da amsa kuwa wajen maimaita masa lafia suke, hakan ya saka shi firfito da idannuwansa da suke da girma da wani ihun ya ce" Kuna lafiar kuke amsa min magana tamkar Mata?, Na ce Maza ne A gabana ko Mata ?"

Wannan karron sai da suka doka kafafuwansu daidaiya a kasa kafin suke sake daukan magana da karfin gaske wajen fadin" Maza ne Sire, We Are Fine!"

Bakin gilas dinsa ya Maida ya sake wara tsayuwarsa a yadda yake wanda kana gani ka san takadarin mutun ne marar tsoro, saima kalar askin dake saman kansa ire iren askin da sojoji ke dorawa saman kansu muryarsa a hadenta ya ce""It's your tung that will kill u , had it been that u are sick i could be linient to u, but since you are all well,
Will neet at the battle field! ( ya yi daidai, Bakinku ne zai yanka wuyanku! Domin da ace baku da lafia ne zan sasauta maku, Tunda lafiyarku kalau zamu fuskanci junna a filin aiki!) "

Juyawa ya yi a take ya shiga taku mai hade da gudu gudu yana kai kawo ya ce" KUN san da zuwan shugaban kasa a gobe dan taron da za'a gabatar a kasar nan, kuma kun san kasar da muka sauka ko ta su waye?, Kun san ko su waye yan kasar a cikin kasata, sun yi fice a faranta min ta hanyar aikata abincina abin nishadina abinda idan ba shi raina ke jagule domin ina son mai aikata shi ko dan na damki wuyansa na jagalgala rayuwarsaa na koya masa ladabi da biyaya na ware masa aya a cikin tsakuwa na gwada masa waye BABANSA!, INA SO daga yanzu Lungu lungu, sako sako na garin nan zaku bi ku kwamushe min tsagera, idan na ce tsagera ina nufin kama daga yan shaye shaye, masu tafia wando a sasabce, masu nikaf din karya, Ku gane da yan bariki idan sun yarda sun fito dan nuna su sune, da budurwar da zata maku tsagalta a cikin aikinku, ku kama min su ku rufe min har sai Mai kasarsu ya bar garinsu kafin ku fitar min da su, bana son na sake maimaici ko na kama wani mai hular da zan koyawa aikinsa a nan, am i clair?"

Da karfin ihu wajen ya amsa da "Yes Sire"

Dakatawa ya yi ya juyo wajen manyan sojojin da suke biye da shi kowa da takardar Budget dinsa ya ringa amsa yana saka hannu har aka zo kan Lieutenant Kamara Guje bayan ya sara masa ya ce" Sir kana nufin ko dan waye, ko yar waye?"

Gilas din idannuwansa ya cire ya sauke jajayen idannuwansa a fuskar Kamara kafin ya kawo hannun ya daka a gefen hannun Kamara wanda har tsakiyar ransa ya ji dukan sai dai ba damar ya nuna domin wannan din ai dama ya samu kafin ya sasauta muryarsa ya ce" Kai bagwari ne ko? KAMARA ina nufin ko jinsin kare ya maku gardama ku rike shi bale mutun da ya san waye kai? Da na bada cigiyar kowa ya rike dansa a gida wanda ya bari ya fito nama ne mu kuma kuraye ne zamu ci!, Ka fito a shirye da niyar yin aikinka kuwa?"

Da karfi ya sake sara masa yana amsa shi da Yes sir, hakan ya saka shi gyada kansa yana dan dukan gefen kafadarsa again ya furta" Repos ! "

Sai kuma ya daga kansa bangaren mutanen dake bayan Manyansu,
gaba dayansu har zuwa yanzun hannayensu a kafe yake wajen goshinsu haka kuma dubansu a gabansu yake, a shirye suke shiri mai sunnan shiri

Da hannunsa ya matsa gaba kadan ta yadda kowa zai iya ganninsa da kyau ya ja ya tsaya tare da doka kafarsa daya a kasa lokaci daya kuma ya daga hannunsa gaban goshinsa kadan ya sara masu da karfi yana mai fara wak'ar sojoji wace kowani soja du girmansa, du takamarsa zaka ga yana da wakokinsu a kansa kuma yana iya yin wakar a kowani yannayi

Ai kam muryoyi maza sai zuka bude , tun karfinsu sunna amshi sunna karra jin kwonjinsu na budewa ya sake budar bakinsa da karfi ya furta" Repos!" ya sauke hannun nasa ya juya ya bar wajen ba tare da ya kuma yiwa wani magana ko wani alamu ba ya karasa wajen tafkeken apash din da aka ajiye masa ya hau yana murda ky din ya warce shi da gudu ya nausa cikin garin dan yin patrui, watau kama tsagerun shima da kansa

Ajiyar zuciya suka sauke a tatare sunna karasawa gaban yarensu dan su karra daidaita yannayin aikinsu domin tafiyar nan dai da LIEUTENANT GANARAL aka yita ba da wani wanda zasu yi sakensu son ransu ba, dan haka idan sunna son zaman lafia kawai su aiwatar da aikinsu yadda ya kamata

___________________________________

SHUWAR ki saurara abinda nake fada maki, a gidan redio, A gidan TV a komai da kika sani na sada labarai sun fada sun sake fada cewar LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN ne ya sauka a garin nan, ke me yasa bakya son zaman lafia ne? Ki dawo ki zauna ya fada ya sake fada kar wanda ya fita, idan kika fita wani abun ya ritsa da ke yaya kike so na yi ne?"

Gilas din dake saman fuskarta ta sasautawa gani ta kaleta kasa kasa kafin ta ce" Aunty, tsakaninki da Allah abinda ya sa kike min kugin kiran nan tun daga cen cikin falo kina gudu har na tsaya na zatama wani mugun abu ne ya faru? , Kin ga da mai a motar nan kuwa?"

Bata bata amsar da mai a mota ba sai kokarin karra nusar da ita kar ta fita da ta kwatanta yi aman ina, kai tsaye SHUWAR ta saka hannunta ta janyo kofar ta rufo tana daga birkin da ta dane da kafarta wanda ya dan dakatar da motar ta ja motar a hankali a hankali kafin ta idasa janta ta wuce gaba dayanta

Tuki take tana mamakin garin gannin du irin tarin al'uma irin na garin nan yau sai daidaiku ke yawo a cikin gari

Ita dai take motarta ta yi da gagawa ta yi kwana ta idasa gidan Elhaj Mai shinkafa

A kafarta ta sauka ta idasa shiga bayan sun gaisa da mai gadin du a tunaninsa wajen y'ar Elhajin ta zo hakan ya sa ya barta ta shige hankali kwonce

A kanta ta gama hardace yaya gidan nan yake tunda a kulun idan sunna tare shine yake yi mata bayanin yadda gidansa yake da bangarensa da na matayensa

Kai tsaye ta durfafa cikin falon da idan bata haukace ba kamar yadda yake ce mata bangaren dama shine nasa na hagu kuwa na matansa wannan shine bangaren daman

Kofar falon da take hangen makekiyar TV ta madubin shigar ta saka hannunta ta tura ba tare da ta yi salama ba ta shiga tana kale kalen falon har idannuwanta suka sauka a kansa shi da matarsa sunna zaune wace itama ba zata wuce da shekarunta ba domin haihuwarta daya a gidan har ya ga ta tsufa yake son sako SHUWAR din

Da yar gagawar maganarsa ya ce" Ke ke, SHSSSSSSHUWAR me kike nema a nan kuma?"

Sama da kasa ta sake binsa da kallo kama daga yannayin jikinsa har zuwa tumbinsa masha Allah
Gaban goshinta ta dafe tana fadin" Kai Allah, kai jama'a kai yanzu in banda hauka irin naka ko nice karuwar ai ka yi hakuri da ni ta yiwu ka samu iri a gidanka, koda yake na ga wannanma ba laifi dake zaunen, Watau ELHAJ kai sana'arka ce haka idan na kula?"

Fuskarsa ya hade sosai yana kallon matarsa ya ce" Ke Umi tashi tashi maza maza ki tafi bangarenki, kuma idan na ji maganar nan a bakin daya daga cikinku walahi sai na sake ki na rantse maki"

Da sauri Umin ta mike tana sake kallon SHUWAR tun daga sama har kasa ta wuce ta gefenta ta tafi

Mikewa ya yi yana fadin" Har gidana zaki shigo ki nunan akuyanci? Ashe baki da wayo? To na rantse maki na fiki iya iskanci idan tunaninki ke yar iska ce, zan yagalgala ki nai maki dala dala, abinda kika hannani kamawa zan kama yanzu na fatataka shi har sai ranki ya bace, kuma ko ina aka je kece marar gaskiya domin ke kika tardo ni har cikin gidana"
Chapter 4 · 0% Book details