← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 138

Sashe 49

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da balaki ya juya ya bi bayanta a lokacin itama ta rasa ina zata nufa, gaba daya ta rikice ganninta da kato ya yi a haka, waima uban me ya fitar da ita da asubar nan ne? Ta bari idan ya yi tafiyarsa sai ta yi aikinta mana, yanzun a banza katon wofi ya kaleta?

"Ke ke zo nan!" Ya fada a kausashe yana nuna mata gabansa

Gaban nasa ta kalla ta karra karewa tsayuwarsa kallo, adu'a ta shiga yi a cen kasan zuciyarta na neman tsari da shi, sannan ta shiga takowa jikinta ba karfi sosai ta nufo inda ya nuna matan

Hannunsa ya saka yana fadin" Ki gyara wannan abin dake jikinki kafin ki karaso min nan!, Kin ga tsayama a cen na fada maki ki fita a harkata a cikin gidana kin ji abinda na fada maki!"

Dukan jarumta, da tsaurin ido irin nata da rashin Tsoro ta yafo tana kallon hannayensa da bemab maboya a dakin nasa kasa kasa ta ce" wai gidansa, gidana dai"

Dif dakin ya dauka domin tsittt ya yi da fadan dan ya ji abinda ta ce
Kai, wayo, anya ba gamo ya yi ba? Anya ba aljanna bace ta shiga lamuransa aka daura masu aure? To aman idan aljanar ce shi me ya mata? Yanzu ace yyarinyar nan ta rasa wanda zata raina sai shi? Cewa fa ta yi gidanta ne fa?

A kausashe ya ce" kika kuma cewa gidana naki ne sai na baki mamaki a cikin gidan nan, kin ga ni fa ba shashasha bane da kike son mayar da ni abin wasanki, sannan da kika fito kike sakin zani a gabana a tunaninki da irinku na kai min da tuni ban zama bunsuru a kasar nan ba? Ki kiyaye haye min har na samu mafitar rabuwa lafiya da ke domin idan kikai wasa sai dai ki sake jewa wani katon a kakarye!, Shirmen banza da wofi, ke mema kika zo yi dakina ne?!"

SHUWWA ta sauke ajiyar zuciya tana kallonsa ta ce" To aman ai gyaran dakin zan yi ko?, kumama ka ga soja nifa ba abinda kake tunani na zo yi ba walahi ko daya, gani na yi a dan zaman da zamu yi da kai wanda nake fatan ko yau ne ya katse nima a yabeni ya fi da ai min Allah wadai kau?, kuma da nake cema gidanka gidana ne ba fa dan ina nufin hakan har cikin raina bane dan dai na dan farkar da yarenka ne kar sunna neman kawo min raini, bayan wannan gidanma ai na gwamnati ne gaba daya......". Ba da tsayaya bane take bashi amsa, irin amsar nan ce kana magana kana marairaicewa kana karya kai da nuni da hannayenka wanda ke nuni ala dole kai a tsoracema kake da mutun sannan a ladafce kake bashi amsa fa ba wai a hargitse ba, idan dai mutun mai rauni ne dole zai birkice a kallonta, idan ba mai rauni bane kuwa bakinsa zai iya yi maka gum ko ka ga mutun ya rikice yana zaginka da magulmaci ka bar masa waje, ba wani gulma ya rikice ne bawan Allah

Shi kam lamarin kukar da shi ya yi ta yadda ya kasa furta mata A ya zuba mata idl yana tunanin idan ya warceta ya dokata da garun nan ta summa yana da zunubi ne ko lada? (😌)

Alamun za'a tada sallah da ya fara ji ya saka shi juyawa da sauri ya fice a dakin ya barta a nan tsaye

Bakinta ta tabe tana kallon madubi ta shiga kunce zanninta a nutse ta gyara a fili ta ce" Ta yiwuma haka aikinsa daga ganni ina daura zanina ka wani kalla kuma ka so nuna nice fitsarariya?, Wollah ka ci kanka tuf tuf ka shafa min lafiya wollah!"

Kayyan ta koma ta kwaso ta dawo ta shiga aikinta da jiki, aiki ne da ta riga ta saba, aiki ne da take yinsa da farin ciki ba da jeka na yika dan ka zamto min dole ba, aiki ne na kwonciyar hankali da sannin hannunta, hakan ya sa a nutse ta gama gyara ko'ina ta kunna turaran wuta sannan ta shiga ninke kayan da ta wanke jiya ciki harda gajerun wandunnansa da ta zubawa turaran ruwa ta dan ajiye saman kujera dan su bushe kafin ta ninke hakan ya sa ta shiga kiciniyar ninke zannin gadon hankalinta kwonce abinta

Budewarsa da shigowarsa da tafiyarsa mai dan gagawa ya sakata dan waigawa ta kalle shi, shima ya tsaya ya zubawa wandunnansa na ciki ido da mamaki ya kalleta da sauri ya sake kallon wajen wandunnan

Itama wandunnan ta kalla, sai ta samu kanta da tsurawa wandunnan ido cike da tunanin abubuwan da a da bata yi tunaninsu ba
Tsintar kanta ta yi da tambayar kanta a kasan zuciyarta' SHUWWA anya kuwa lafiyarki kalau?, Wandonsa fa kika wanke kika kuma fitar zaki ninke, kin ga kallon wandunnan yake idan ya sake kwatanta ki kamar kwartuwa fa? Ke kam kin zama wace bata san ciwon kanta ba, wada ta lalace ko? Yaya kike so ya ce bayan dama ya gama fasaraki a yar duniyar karshen zamani?'

A hankali ta dago dubanta da dan satar kallo ta sauke a kan fuskarsa
Kai sojan nan ba dai kyau ba wollah, saima idan ya hade fuska kyansa ya fi fitowa
Idannuwanta cikin nasa suka sauka tsamo tsamo
A hankali ta dan kikifta ido tana kallonsa ta bude baki ta ce"

😘😘😘😘😘 Morning all, na ce ba yau juma'a ko?😒raba gidanta da karti na mata girki ya matukar kayatata ta ce"😌💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥
*ALK'ALAMIN K'ADDARA TA*
‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 2️⃣6️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya*
2 *Banida zabi*
3 *Duk karyar kada*
4 *Baka ce*
5 *Daga tafiya daukar soja*
6 *Kutkale*
7 *Makauniya ce*
8 *Mage mai kwanciyar daukar rai*
9 *Duk nisan jifa*
10 *Dutse*
11 *Idan Ka Raina Inda Kake*.
12 *Neman Na Kaina*
13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A hankali ta dan kikifta ido tana kallonsa ta bude baki ta ce" Na ga sun yi datti ne sai na wanke su, baka ga darzar da nai masu ba."

Idannuwansa ya rintse yana jin ikon Allahn dake faruwa da shi, ya sake budewa yana kallonta ya ga a tsayen take abinta, d'an kifta ido ya yi yana sake kallonta yana karantarta, gaba daya yarintarta da k'ananun shekarunta ne suka bayyana a idannuwansa.
Sai ya samu kansa da tunanin anya ta zarce 17 kuwa?, Haka kuma ya shiga tunanin shin me ya saka ta zab'i rayuwar bariki da aure auren maza a rayuwarta duda ya san da wahala abinda aka ce ta ratso ta zo kasar nan ta zamto nutsatsiya, aman sai ya samu kansa da tunanin koma meye bai dace ace yarinya karama irinta ce ta saka kanta a muguwar rayuwa har haka ba.

Abinda yake bashi mamakin na gaba shine, irin yadda take tsayawa a gabansa kamar tana jiran ya yi magana ne kanta tsaye tana kallonsa bai san me take kallo a jikinsa ba kallon nata kuma ba irin na matarsa ta cen bane, ita wancen daga nesa ne take kura masa ido da zarar ya kalleta kamar munafuka sai ta sinne kai.

Ita wannan bata kallon nasa sai idan tana jira ya bata amsa, irin yadda take kuma bashi amsa kai tsaye na matukar bashi mamaki, wai shin ita bata jin tsoronsa ne?

Iskar dake bakinsa ya furzar yana nuna mata hanyar fita ya ce" Kin yi bakuwa ki je."

Ido ta karra kura masa ta kalle shi ta kalli hanyar da ya nuna mata, ta ce" Ni kuma? Bakuwa a nan?"

"Ya salam" ya fada yana dafe gaban goshinsa ya tattara hannayensa ya dago duka biyu ya ce" ke, mu nawa ne a dakin nan? Ko aikena kikai na je na gano maki ke din ko ba ke ba?"

Da sauri ta zagaye shi tana fadin" Sorry " ta nufi hanyar fitan

Har ta kama kofar zata bude muryarsa a ciki ciki ya ce" SHUWWA."

Turus ta yi tana jin gabanta na faduwa haka kuma ta juyo a hankali tana kallonsa.

Hannunsa ya dago a hankali ya nuna mata hannunta sannan a saman lebensa ya ce" Give me."

Hannun nata ta kalla, ido ta zarro domin gajeran wandonsa ne a hannun nata baki irin mai hade da pant din nan mai raga raga
Da sauri ta karasa ta kama hannun nasa da hannunta na dama ta saka masa wandon ta rufe tana karra zarro Idannuwanta ta juya da gudun da ya saka shi bin kafafuwanta da kallo da hannayenta da take yarfewa ta fice a dakin kwata kwata.

Kofar da ta rufo masa ya kurawa ido na dan lokaci yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya nufi wajen da wandunnan nasa suke ya ajiye dayan ya nufi wajen bed dinsa ya zauna yana kai hannunsa kusan hancinsa dan ya dan goge hancin nasa.

Sansanyan kanshin turaran ruwan da ta zubawa wandunnan ya daki hannayensa hakan ya saka shi lumshe idannuwansa a hankali sanan ya sake budewa ya zubawa hanyar da ta fita ido yana sauke ajiyar zuciya kafin ya tabe bakinsa ya dan karra kwontawa dan yau sai karfe tara zai bar gidan.

______________
Chapter 49 · 0% Book details