← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 138

Sashe 19

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanon abinci daya ne ake miko mata tun na safe sai wata safiyar wanda ta ajiye haka a matsayin sunna tunanin tana girki da kanta ne kila, bata san mutanen gidan na girki sau biyu ne kadai a wuni, lokacin dorin na biyu kuwa ba'a kawo mata sam!
Bai neme ta ba, bai nemi inda take ba, sai dai ta hango giftawarsa ko ta ga wata yar budurwa mai yawan zama da zumbulelen hijab har kamar ya kayar da ita na ajiyewa SUDAIS abinci shi kuma ya dauka ya ci
Bata taba sannin cewa SUDAIS yana cikin jerin mazan da suke dauke da fushin rayuwa ba dare ba rana ba'ai masu komau bama bale irin abubuwan da matar malamin da ya daura aurensu ta fada wanda ya sake bincikawa ya ga eh gaskiya ne ya saka shi kulatarta a zuciyarsa sannan ya yi niyar yi mata kishiya kwana kusa dan ya horata kuma ya dauki budurwa da fari koda zai iya kusantarta

"Ki bani amsa mana ina maki magana" ya sake fada a harzuke hakan ya sakata mikewa tsaye tana kallonsa ta ce" Ka ga, ka sasauta fushinka ka saurareni mana SUDAIS, eh na taba yin aure wannan gaskiya ne"

"Kin taba yin aure ko kin yi aure aure ana sakinki daga an daura maki?, Kennan gaskiya ne matsalar biye biyen mazan ne kema ke damunki ake sakinki aure? Idan wanu ya sake ki dan ra'ayi wani ba zai sake ki ba dan jin dadi, SHUWWAR kin ha'inceni kin rufe ni kin saka da aureki a rufe ko?"

Gabanta ne ya fara faduwa gannin kamar abun na nema ya zama baba, hakan ya sa a birkice ta shiga kokarin ganar da shi abubuwan da sula faru tana mai sasauta muryarta a kan rasa tana mayyar da fushinta gefe ta ce" Haba my SUDAIS, ban kawo maka maganar auren da na yi a baya bane dan babu wanda na tare a cikinsu, babu wanda na je na dora tukunya a cikinsu, SUDAIS hasalima auren kawai ake daura min *ALK'ALAMIN K'ADARRARTA* na datse igiyoyin auren nawa ba tare da na kasance mace a gidan miji ba, ka yi hakuri dan Allah idan hakan ya bata maka rai, maganar auntynama gaskiya ne, idan ka kula fitarta da dawowarta kan sakani a hali na bacin rai da tashin hankali, aman duka wannan baa matsala bane tunda ni bana aikatawa"

SUDAIS dake kallonta yana dane wayarsa dake ringin ya ce" Me zai tabatar min da kema ba hakan bane SHUWWAR?"

SHUWWAR ta sauke ajiyar zuciya tana fadin" Domin ni budurwa ce SUDAIS...." ta idasa fada tana sada kanta cike da jin kunyar furucinta

Shima sai ya samu kansa da kureta da kallo, maganar da ta fada na neman yin tasiri a kwakwaluwarsa ya ce" Kina nufin, baki taba wata mu'amala da wani namiji ba a duniya?, SHUWWAR ina iya ganewa fa da zarar na kusanceki"

Kunya ta hanna mata amsa shi, tana ra karra sada kanta aka kuma doko masa wani kiran, hakan ya sa ya amsa yana dubawa da dan sauri domin mahaifinsa ne

Abinda baban nasa ya fada ya saka shi mikewa tsaye a rikice tana fadin" camp din sojoji kuma? Aba kuma SHUWWAR SHUWWAR tawa aka ce? Me ta aikata da har za'a turo daukanta zuwa camp din sojoji?"

Cikinta ne ya juya a zaunen da take hakan ya sa ta kafeshi da ido tana son fahimtar abinda ake fada masa a cikin wayar nan tasa

Wayar ya kashe yana kafeta da ido ya ce" SHUWWAR me ya hada ki da motar sojoji aka zo daukanki har cikin gidanmu? SHUWWAR kin kuwa san darajar mahaifina a garin nan? Motar sojoji du irin yadda yake kare mutuncin kansa da ta iyalinsa yau a zo nemanki me kika aikata?"

SHUWWAR ta mike a rikice tana kikifta manyan idannuwanta ta ce" Innalilahi wa inna ilaihi raj'une motar motoci kuma? Me mes na aikata dan Allah?"

Gannin kamar raini irin na Shuwwar karra ci gaba yake yi a wajensa ya saka shi miko mata hijab dinta yana fadin" wuce mu tafi domin Aba ya tafi ba yau ba ya kuma nemi alfarmar kar a dauke ki a bayan mota zan kaiki, wuce mu je idan wata jarabar kika janyowa kanki cen ki karata, SHUWWAR ba zan boye maki ba na fara tsintar dana sani a aurenki da na yi"

Sosai magangannun suka soketa aman kuma sai ta hadiye ta bi bayansa cikinta na ta kukan tsoro da tunanin uban me ta yiwa soja kuma ita?

Ido ido ake yi a dakin bayan jin magangannun da suka bayana masu ga kuma wanda ya saka aka dauko sun yana zaune a hakimce tamkar wani sarki yana kallon su

Takaici, bakin ciki, tsana bata taba tunanin zata ji a kan wata halita irin yadda lokaci daya ta ji a kan wannan bawan Allahn

A rikice ABDUL Mutalab ya ce" SHUWWAR da gaske wannan mijinki ne?, Aman ai aunty ta bani wata uku ta ce zaki gama ida hankalinki ya kwonta sai mu je mu yi tambaya idan har kin halata a gareni na aureki ko? Shine kika yi aure ban sani ba?, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une"
Ya karashe yana mai fashewa da kuka lokaci daya mahaifinsa da Mahaifin Sudais suka kwashi salalami sunna kallonsa
Mai shinkafa ya kai masa rankwashi yana fadin" Kai dan ubanka ni fa na aureta, muhadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam dama ana haka aa hausa?"

Mahaifin Sudais ya ce" Elhaj Mustafa dama itace na halarci daurin aurenta a kofar gidansu da kai?"

Mai shinkafa ya gyada kansa yana fadin" Allah ya taimaki malan ai wannan da kake gani nine na aureta , a lokacin da na fuskanci wacece marikiyarta na saketa dan ba zan iya hada zuria da ita ba, shine ta min dibar albarka da maganar kudin nan da yalabai Maman sani ya yi bayani a kansu ta dauko su a dakina a gidana , ni kuma sai na ba yaron nan salahun ya maka min ita a wajen sojoji a amso min hakina kar ta kashe, ashe ka ga yaron nan daya da na malaka ya hadu da sharin mace wai ya taimaka mata kar a rufeta ya ce matarsa ce? Ka ji yadda aka yi, a ranar da aka daura mana aure......................." Baki daya abinda ya faru mai shinkafa ya kwashe ya sanar dala dala wanda hakan ya saka MUHYIDEEN dake sauraro jin takaici a zuciyarsa domin shi du a tunaninsa sato kudin ta yi shi yasa ya sake bi ta kanta dan idan har satowa ta yi ya tabata ba ita kadai bace barauniyar ba zara rasa yan tayata aikata satar ba, da ya samu reshensu kennan da ya more ya ringa kamo su daya bayan daya, aman abin takaici sai yake jin wannan tsohon shi ya dauko mata kudin da kansa dan bashi da gaskiya ba wani dan yana tsoron taa masa shari ba

Da wani takaicin ya mike yana daukan wayarsa ya kalli Lieutenant Maman Sani da ya sara masa yana fadin" Ashe bata lokaci ne, ka bata takardarta ka salame su, bara na shiga cikin gari"

Daga haka ya zagaye ya yi tafiyarsa ya bar Lieutenant Maman Sani da alkakai domin a lokacin Shuwwar ta yi saurin matsawa kusa da mijinta tana doke hannun Abdul da ya matso yana rike hijabinta yana fadin" Ki ce ya sake ki ni kike so ba shi ba"
Ta ce" Elhaj yanzu saboda kudin da ban ci ko ficika a cikinsu bane ka saka aka daukoni aka kawoni nan a gaban mijina da mahaifinsa kana neman wulakanta min aurena? An fada maka duniya irinka ce da banda san kanka babu abinda ka iya?, Allah sai ya saka min fadan da ka hadani da mijina a kan shirme"

Da dan karfi ya ce" To rasa kunya, to uwar mararsa kunya, an fada maki ni na neme ki ne? Wanda ya fitan nan shi ya sa aka kawo mu baki dayanmu nan ba wani ba, ni na neme ki? Haba SHUWWAR ko a hanya ai bana tunanin fatan haduwa da ke, Kai abdul idan ka kuma tabata zan tsine maka albarka, hala hauka make zan hada jinni da wannan yarinyar?"

SUDAIS kam wata ajiyar zuciya yake saukewa saboda jin abinda ya faru, shi fa dadima ya ji cewar da gaske ne ashe da ta ce maza babu abinda ya shiga tsakaninta da mazan da take aure duda matar Malan ta ce barinta hudu

A sanyaye ya ce" Allah dai ya sanyaya, in sha Allah zan kawo maka kudin da kaina a yi hakuri Sir mu koma gida"

Mahaifinsa da mamaki ya ce" Ku koma gida? Ku koma gida da wa SUDAIS? Kana nufin nima zan ga kashi da rana da dare na zo na saka kafa ne? Kana ganni dai a gabanka komai yake faruwa ba wai fada maka aka yi ba, a gaskiya wannan ba uwar jikokina bace, nima kai daya ne namijin ba zan iya wannan saken ba, ka bata takardarta ka dawo gida, idan ka ki aikata haka zan yafeka duniya dan na kula bata yiwa maza da sauki ga Elhaj da dansa ana kace nace bayan mu da muke abokanan kasuwanci mun san irin biyayar da ABDUL Mutalab ke yiwa mahaifinsa?"
Yana gama ya mike tsayinsa yana yiwa sir salama ya fice a office din

A haka Mai shinkafa yaa tisa keyar nasa Dan dake tirjewa suka fice suka bar SUDAIS da matarsa da sukai mutsuwar tsaye

Yana juyowa gabanta ta zube gwuiwoyinta kasa tana hada hannayenta bibiyu ta ce" Dan Allah, dan Allah kar ka yi, kar ka sake ni, kar ka yi mugun aikin nan, ka bari mu fadawa malan su hadu da datijawan anguwarmu su je su ba Aba hakuri na tabata zai dangana ya barmu mu yi aurenmu, SUDAIS ina sonka kar ka sakeni, kar ka mayar da ji bazawara dan Allah"

Tana fada hawayenta na barkewa a saman fuskarta, hannayenta a hade wahe daya ta yada suke bari ba ji ba gani
Chapter 19 · 0% Book details