Sashe 75
Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya saurara gannin yadda ta kwalalo idannuwanta waje gaba daya, sannan ta dafe kirjinta gabanta na faduwa jikinta na rawa
A sanyaye ya ce" Na so ki fi karfinsu, da suka kirayeki ki ce da su ke yar malam ce, gidanku alkur'ani kuka rike, ki yi anfani da sanninki cewar dukkan tsanani yana tare da sauki, ki maka ni da adu'o'i , da ta yiwu yanzu nan dinki ya tasa......." Ya fada yana shafa cikinta a hankali ya sake kallon fuskarta ya ce" Sai dai kashhhhhhhhhhhh............."
Daga haka ya saketa ya juya da niyar shigewa dakinsa na barci, sai kuma ya juyo a dan kausashe ya ce" Kuma itama ba sonta nake yi ba!"
Daga haka ya shige ya zauna bakin bed yana maida numfashi sannan ya dauko wayar da yake sauraro da ita ya zauna zaman jira
A haukace ta kashe kayan da wani irin sauri cikinta na juyawa ta yi bangarenta
Tana shiga bayi ta zarce da wayar da suke magana ta haye saman salga jikinta na masifar rawa
Ko idasa sauye abinda ya murda mata cikin bata yi ba kira ya shigo wayar tata
A jirkice ta wawura dan a kasa ta ajiye ko zata iya zubar da abinda ke cikinta ta daga ta saka a kunnenta
"Bani albishir din ya ci" aka fada a zakwonce
Kuka ta fashe da shi bakinta na rawa ta ce" Walahi ya sani, walahi ya san abinda muke aikatawa, kuma ya san ko ku su wanene "
Gaban mai kiran ne ya kwonci kwonci ya bada rarararassss ras ras ras rassssssssssssss, shiru ne ya dauki wajen na dan lokaci kafin kitttttt a kashe kiran
MUHAY dake zaune a saman gadonsa ya yi dan murmushi ya ajiye wayar a aljihunsa ya mike a nutse ya fito ua fice bayan ya duba agogo da tunanin Allah ya sa Mamah bata yi barci ba yanzun
Dadadan kanshin turaran da ya kasa gane na ruwa ne ko na wuta ya daki hancinsa a lokacin da ya bude falon
A hankali idannuwansa suka sauka a kan kayayaki manyan bokitai manya manya sosai , ga wasu manyan ledoji shake da kaya a cikinsu, ga manyan galoli masu dauke da turarukan ruwa, harda su turmin karfe da tabaryarsa da katon ludayi a ajiye a saman cikinta, ita kuma ta yi barci a ringyeshe saman doguwar kujera kafarta daya a kasa dayar a mike sambal saman kujerar
Yanzunma dogon wando ne a jikinta har kasa , kuma damame ne , sannan rigar dake jikinta gwara ta jiyan ta fi arzikin rufewa dan dai a sake take rigar sannan barcin da ya kwasheta ne ya saka rigar dagewa har cikinta ya bayana a fili
Aiki ne suka raba, duba da suka ce da Mama sun iya hada turaran wuta ta saka suka yi list aka kawo shine fa ta zabi aikin harhada turaran da itacen turaren, su kuma suka shige kicin Nahidt zata kiyawa Mama yadda ake soya garin turaren da kuma icen da suke sim soyawa kafin su hada shi, shine ta fara barci ya kwasheta domin gajiyartama ta gaji yau din nan kokarine take yi karfi da yaji dan Nahidt ta fada mata cewar karfa ta ja abinda maman sojan cen ta tsaneta ko ba komai a rabu ana begen junna ya fi a rabu da ana tsine hali, shi yasa ta dage take kakau da komai, balema Maman kanta gaba daya ta tare a tare da su da dukkan motsinsu da nan nan da su, har mamakinta suke yi yadda komai suka yi sai ya sakata sakin murmushi
Kansa ya cire daga wajen kicin da yake jiyo dariyar Nahidt da ta mamansaa da mamakin lamari na mata ya dan dafe jikin kujerar yana auna awanin da suka yi tare, aman shine har suka sake da junna haka suka zama kamar wasu da suka jima da sannin junnansu? To shi ta yayama zai iya sakewa haka da mutun daga haduwa?
A hankali ya mika hannunsa dan ya dauke ludayin dake saman cikinta dan harda turare a jikinsa ta dora a saman jikinta ta yi barci
A zabure ta farka tana rike Ludayin tana fadin" Idan aka hade ruwan da itacen aka barsu suka kwana sun fi tsumuwa sosai ta yadda idan akai sauran hade haden kayan kamshin zai kasance kamshinsa mai kama daki.......... Lah da kaine???????" Ta karashe da dan nuna alamun mamakin da shine take gayar maganar nan, ita ta zata ai su Nahidht ne
Hannayenta ta daga a hankali ta shiga yin mika wace barcin da ta fara ne ya hadasa mata ita ba wani abin ba
A hankali ya bi hamatarta da kallo wace ya yi mamakin ganninta sumul kakal ba dis din gashi sannan ba alamun dati a tatare da ita, sumul din wajen abin sha'awa kamar ba hamata ba da kuma kirjinta da ta bankaro dan yin hamarta mai ma'ana ( Maganin bakin kasan hamata, wani lokacin zamu ga mutun ko fari ne hamatarsa tana da dan duhu, idan kuwa yana kwaikwaita kwaikin hamatar tana da baki marar kyau, idan kuma shi din baki ne wahen hamatar yakan fita daban sosai, idan aka taki rashin sa'a mai gidansa ba abinda ke haukata shi irin ya ringa gannin uwar gida na mika ai ba dadi ka ringa daga hannaye hamata na neman saka amai koda bata hamami, maganin wannan da shi da bakin raba rabar kafafuwa, watau cinyoyi wajen dake haduwa shine BICARBONATE, zan hada posting din da hoton nawa Bicarbonate din, zakina yanka lemun tsami ki dan zuba garin bicarbonate kadan sai ki shiga darza a hankali a hankali, ba tashi daya ko yi uku zai cire maki abin nan, idan kikai naci zaki ga kyakyawan result , bashi da effet secondaire in sha Allah)
A hankali ya kawar da idannuwansa a kan hakan yana girgiza kansa ya mike ya koma saman kujerar dake facin din wajen da take zaune ya zauna har sai da ta gama ta diro kafafuwanta kasa tana dan murmushi ta yi zama irin na turi barotao, watau ta wara kafafuwanta ta girka duwawunta ta gantsare kugunta hakan ya bada wata kala ta neman fitina ta dan sake yin murmushi ta shiga ci gaba da aikin tana fadin" bari dai na gama aikin nan kar kilu ta janyo mini bam gani yar marainiya da wahala ake samun masu jin kan marayu a kasar nan"
Kansa ya maido kanta bayan ta karashe maganarta ya zubawa zamanta da aikin dakan da ta fara yi masa ido yana kallonta
Kai ya dan girgiza kasa kasa ya ce" Dakata "
Tana dakan ta dago tana kallonsa hadi da dan dage gira daya ta dan kuga tama fadin" Ka ce?"
Ikon Allah, shi kawai ya tsaya kallo idannuwansa cikin nata, a hankali kuma sai ta fara rage karan dakan harma ta tsayar tana gyada kanta ta ce" Da a layin gidanmu ka taso saudiya ban san yaya zaka kare da ciwon kan hayaniya ba, mu fa a cen idan ba'a tashi da hayaniya ba kowa fara shan jinnin jikinsa yake yi, gaskiya hayaniya ai rayuwa ce, yalabai aman baka taba harba bindiga ba kau?"
Shi kam ta daina bashi mamaki yanzun, ya riga ya san mai iskokai dole za'a samu irin halayan nan a tatare da shi
Hakan ya sa bai ba abin damuwa mai yawa ba ya ce" da me kika je kasuwa?"
Dan yin tsai ta yi tana kallonsa , sai kuma ta kalli jikinta ta ce" Au, da hijab din mama ne"
Bakinsa ya tabe ya mike ya juya ya yi tafiyarsa a falon ya koma bangarensa
Summa dare suka cika kafin su nemi wajen kwonciya
A lokacin da Mama take ta sinsinar hannayenta tana mai jin farin cikin yau itace zata koyi yadda ake yin turaran wuta ta ce" Kennan mahaifiyarku ke yin na siyarwa?"
IBTISAM ta kalleta, sai ta yi murmushi tana dan girgiza kanta ta ce" Na turara dakinmu ne take yi, Abanmu ya hannata siyar da turaran wuta...... "
Nahidt ta yi yar dariya itama tana cewa" Mama ai ko cimar larabawa da take yi na amare idan zasu yi taro ana biyanta baya so, ya fi so ya fita ya nema"
Mama dake hankalce da yannayinsu na sun shiga a yannayi na bege da kuma missing din iyayensu ta furta" Allah ya sa sun huta "
Shuwwa ta kalleta da yannayi na abinda take ji daga zuciyarta ta ce" Bamu ga gawarsu ba fa, sannan bamu ga kabarinsu ba, kabarin da ta nuna mana ba nasu bane, ba nasu bane"
Nahidt ta mintsineta tana girgiza mata kai dan ta ankarar da ita a gaban wa take son fara gardamar tata ta mahaifansu basu rasu ba, ta maida harshenta yaren buzanci ta ce" ki farka a gaban sarakuwarki kike!, Ki daina wannan abin naki, IBTISAM da basu rasu ba kina tunanin akoy abinda zai hanna su neman mu ne?, Da sunna yare kina tunanin kulafurcin soyayar da Abanmu ke mana zai iya zama dukan lokacin nan bai neme mu bane? Sai kin mutu kin je kiyama zaki yarda sun jima da barin duniya ne?, Ya RAB kar ki yi ta fara tunanin mahaukaciya ce ke mana!"
Shuwwa ta lumshe idannuwanta hawayenta suka zuba da yaren larabci ta ce" kina tunanin zan ji kunyar a ce da ni mahaukaciya a kan abinda nake ji a zuciyata ne?, Me yasa zan yarda sun rasu bayan ban ga gawarsu ba?, Har aka kamo mu daga saudiya muna zuwa neman gannin ainahin kabarinsu, ke din da kin yarda sun mutu komai kukan da zan maki zaki yarda ki bini ne? Anmy da abihna basu mutu ba! Idan sun mutu ki maida ni ki nunan kabarin da hankalina zai dauka cewar na iyayena ne, a jikina ban ji ba cewa sunne a kwonce a cikin kasar nan!"
Nahidt zata bata amsa itama rai a bace a sanyaye Mama dake binsu da kallo tana ta hanna kanta zubar hawaye da yaren buzanci cakule da larabci ta ce" Me ya faru da ku?, Me ya faru da ku y'ayana?, Ku fada min dan Allah me kuka gani a rayuwa?"