← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 138

Sashe 50

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"NAHIDT" ta fada da dan karfi tana zarro ido sannan ta shiga saukowa da gudu gudu ta nufo NAHIDTH da ta mike tsaye itama tana kallonta.

Hannaye suka budewa junna tamkar wa'inda suka shekara basu ga junna ba sunna kyakyata daria suka rungume junnansu
Da muryar dariya da kuka kuka da ihu ihun farin ciki ta ce" Nahidht, i miss you, i miss u so much, sai ina ji kamar zan yi hauka idan na waiga ban ji ihunki ba, kin ga saura kiris ya sakeni na dawo abina, ina missing din muryarki"

Nahidt ta dagota daga jikinta tana kallonta ta ce " Ke tsaya dan ubanki Ya sako ki?"

SHUWWAR ta dan kifta ido tana kallonta ta ce" No ba haka nake nufi ba."

Nahidt ta kama hannunta ta jata sai saman lumtsumemiyar kujerar dake girke suka lume abinsu tana kallonta ta ce" Farka dan ubanki, na ce farka!, Idan ya sakekima babu inda zamu tafi! Ke ashe baki da hankali? Har yanzu kina kan bakanki na ya sake ki? Shi yasa kike zaune da zani a saman rigar barci da safiyar Allah? Ina matsatsu firgitatun kayanki ne? Ko na barcin wannan ai ya yi sutura, Shuwwa kar ki ce min bakya kwana a dakinsa tunda kika zo?"

SHUWWAR ta zuba mata ido bata ce komai ba a kasan zuciyarta tana ayana' Du tunani take wannnan mutumen wani mutun ne mai sauki kai ko? Ko du ji take kowani namiji da zarar ka saka matsatsu ka yi tafiya a gabansa zaka dauki hankalinsa ne?, Bata san cewa wannan mai kama da aljannun ya fita taurin kai bane, bama wannan ba bata san cewa baya cikin burikanta ne?'

"Kina nufin har yanzu baku yi....." Nahidt ta fada tana kallonta da zarro ido.

SHUWWAR ta dafe hab'arta tana fadin" kin ga matsalata da ke fa kenan, kin gani fa ko?"

Nahidt ta taba hannu tana fadin" Ko bashi da lafiya? Ko kece yar iskar? Shuwwa mijinki ne fa? Kwana har biyu daga ke sai shi a cikin gida ko shedan din bai samu galaba a kanku ba hala? Innalilahi na shiga uku na lalace Shuwwa du uban kudin da na kashe na dudura maki magungunna har yanzu bai fara kaikaitawa ba? Ke ina safarki? Ban hannaki zama ba safa ba?, Wayo duniya Shuwwa kina kallon kato yana shiga yana fita koda baya so ki masa dole mana?"

Wannan Karro SHUWWAR sai kawai ta zuba mata ido ta gaza ce mata komai sai da ta dasa aya ta ce" Wai me ya kawo ki ne?"

Nahidt ta dan kalleta, ta dan yi tsam sai kuma ta gyara zamanta tana murmushi ta ce" Na k'auro fa, ai mun ma yi magana da shi kin ga ya sa an saukeni baki ga yadda aka amshi kayana aka min maraba aka ce ga dakina da komai da komai, Shuwwa kin samu duniya Allah baki k'iyama."

Shuwwar ta zaro ido tana kallonta ta ce" Kin k'auro ina?, Ni da nake shirin tafiya sai ki k'auro? Waye ya sauke kin ? Ba dai wancen dunkum d'in ba kau? Nahidt tsakani da Allah me yake yawo a kwakwalwarki ke kin san ai ba zama zan yi da mutumen nan ba, na san kin gane da ba zama zan yi da shi ba, shine zaki kauro kema?, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une Nahidht ina yayan namu yake yo? Gaskiya sai dai mu koma wajensa tare, waima me yasa baki zauna a wajen yayan namu bane?"

Nahidt ta zaro idanuwanta da fada fada ta ce" Ke da barin gidan kun ci uwaku! Na ce kun ci uwaku!, Kuma da kike cewa wai ina yayanmu yana nan baima san na kauro ba, ni ba zan iya zama a gidansu ba sai kumbiya kumbiyar munafurci suke yana sando baya so a ga zai je dakin Fauziya, itama wai ni take jin kunya dan wani tsohon munafurci, ke ni gidansuma ba hayaniya walahi ni kuma na saba ana haya haya ko yayane kau? Shuwwa wai ko dai korata kike ne? Kudi kika yi kike korata ne?"

SHUWWAR ta rafka tagumi da hannayenta bibbiyu tana kallon yayar tata, wai irin abin nan take yi na daukaka karamin abu dan ta sakata a uku, wai da wani yare NAHIDT take so ta kwatanta mata dala dala waye MUHAY ne?, Da yaya take so ta kwatanta mata shi din ba kalar maza yan soyaya bane? MUHAY bai yi kama da wanda zai iya tatalin mace ko ya nuna mata yana sonta ba, domin shi matan suke yiwa haka ta yaya shi zai fara yiwa wata? Shikenan ita sai ta zama banza a banza kenan? Ta zauna da k'aton sai dai ita ta ringa rarashinsa shi ba zai rarasheta ba? Ai ba haka bane rayuwa gaba daya ba haka bane ba, ita burinta ta samu namijin da zai kasance mai yawan maimaita mata kalmar so, wanda zai ringa fada mata ba dare ba rana cewar itace so dinsa, wanda zai zama tamkar redio idan tana gefensa, aman wanna mutumen idan ya budi baki dan ya mata masifa ne, a kwana biyun nan da ta yi da shi zata iya cewa kyautata masa b'ata masa rai yake!

A hankali Nahidt ta ce" Da kin san abinda ya koro ni gidan nan da sasafe da baki nemi na koma ba, dan na san ranki sai ya baci Shuwwa."

Shuwwar ta cire taguminta tana kallonta ta ce" Wani abu aka yi maki?"

Nahidt ta sauke ajiyar zuciya tana aron jarumta zata fara magana wayarta ta shiga kuka.

Kin dubawa ta yi domin a tunaninta yayansu ne ko Fauziya, bata san cewa Malan bane, da ta dauka ta gindaya masa sharudan da ta gama zanawa ranta sannan ta fada masa ya ji kunya wollah, ta danne wayar ta hade hannayenta ta ce" Abanki, Shuwwa Abanki ne ya ba matarsa waya ta zageni ta ce min karuwa?"

Gaban SHUWWAR ne ya fadi tana kallonta ta ce" Aunty, kalle ni, kalle ni, dan Allah ki fada min gaskiya kin ji? Aban nawa?"

Nahidt ta taba hannu tana fadin" To karya zan maki ne?, Na rantse da Allah tsakiyar dare muna maganarki da shi jiya kawai ya tashi ya kai mata wayar dakinta ta aniya duran ashar harda mamanmu da abanmu ta zaga, ta kuma ce min karuwa wai ina kiran mijinta tsakiyar dare!"

Zuciyarta ce ta fara tafasa a zaunen da take tana kallon auntynta ta dan wara zamanta tana kallonta ta ce" Nahidht, dan Allah ki rufa min asiri ki fada min yadda abin ya kasance kin ji? Kar ki saka na aikata abin kunya, domin idan matar nan ta taba ni ta kwana lafiya banda ke, bana tunanin zan iya kyaleta a yau Nahidt, me ya hadda ku waya da Abahna? Kin tabata shi ya kai mata waya? Abana ba zai aikata haka ba Nahidt, ki fadan yadda abun ya kasance."

D'auke hannunta ta yi daga na ta hannun da mamaki ta kalleta tace "Kai! Shuwwa a ganinki k'arya na fad'a? Zan miki karya ne dama ? Wallahi gaskiya nake fad'a miki, ke abun kunya fa Abanki ya riga daya aikatashi, sai dai fatan kiyaye na gaba kawai."

A zafafe take kallonta har ta muskuta ta gyara zamanta, wara k'afafunta tayi sosai irin zaman nan wanda ko masifa kake za ka ji dad'in jijjiga jikinka yanda kake so, hannun rigarta d'aya ya fad'i har ya sauko kan damtsenta, ba wai dan ta mata yawa ba sai dan kalar zaman da ta yi ta dafe hannunta d'aya akan cinye.

Kafin ta ce wani abu suka ji takon saukowarshi daga sama, da d'an sauri sauri yake saukowa saboda wasu takardu da ya ke son ba wa d'aya a cikin yaransa ya kai masa ofice.

Sam bai kula da tsiyarsu dan yi yayi kamar bai gansu ba ya nufi hanyar ficewa daga falon gaba d'aya, a yanayin neman fitina da rigima ba tare data gyara zamanta ba tace "Ji mana."

Har zuciyarshi bai yarda da shi take ba, dan haka ya wuce abinsa har ya kama k'ofa zai fita ta d'aga muryarta yanda zai ji ta ya kuma fahimceta tace "Ji mana malam soja."

Cak ya tsaya hannunshi na kan hannun k'ofar amma ya kasa jawowa ya bud'e, a saib'ance ya juyo ya zuba idanunsa akan ta.

Nahidt da ke kallon Shuwwa da mamaki ta rarako ido ta rufe baki mamaki na neman kasheta tace "Muhammadu Rasulillahi sallalahu alaihi wa sallam! Allah ka jik'aina tun man mutu ba."

Sassauta muryarta tayi a hankali tace "Shuwwa ashe dai haukan da na ji ana rad'e rad'i a kan ki gaskiya ne? Yanzu ke dan ubanki wannan d'in ne daga zaune kike kira da ji mana...Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"

Zunbur ta mik'e ta d'auki mayafinta tace "Bari in koma d'akina, wannan lamari na ki sai addu'a."

Kallon fuskar Nahidt yayi sanda ta kawo kusa da shi, d'an kaucewa yayi kad'an tare da sakin hannun k'ofar ta rab'a ta fita, saida ya ji ta rufe k'ofar ya dawo da dubanshi a kan ta.

Tasowa tayi tana gyara hannun rigarta daya fad'i ta kai kusa da shi sannan ta tsaya, kallon fuskarshi tayi tace "Dama ina so zan fita ne anjima, zan je wajen Abana."

Gefensa ya d'an kalla yana sakin murmushin gefen labb'a mai ciwon gaske, yayin da zuciyarsa ke ci gaba da raya masa duk Dady ne ya ja masa wannan wak'i'ar, amma yanzu zai wa tubkar hanci ta yadda za ta banbance aya da tsakuwa.

Damatsenta ya damk'a da k'arfin da ya san za ta iya d'auka, ihu ta saki na balakin daya ziyarceta amma sai ta ji bakinta ya sake yin d'uff ta kasa furta komai.

Gaba d'ayanta ya d'agata, irin d'agawar nan dake raba mutum da k'asa, kuma gata a hannayenshi ya rik'e damatsenta, wutsil wutsil da ta ji k'afafunta na yi a doron k'asa yasa ta duk'ar da kanta dan ta tabbatar wai gaske d'agata ya yi, duk'awar da ta yi ce ta sa hular kanta fad'owa har saida ta shafi fuskarshi kafin ta dire k'asa.

A kid'ime ta d'ago dan ta kalli fuskarshi ta rok'eshi Allah Annabi ya sauketa k'asa dan yanzu ta tabbatar a sama take.
Chapter 50 · 0% Book details