← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 138

Sashe 132

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Jikin hajia ne ya kwashi bari, ta dora hannunta a saman kai harshenta na rawa ta ce" Dan Allah dan annabi ku bari, Innalilahi NAHIDt saketa mu je saketa, dan Allah saketa mu tafi"

Nahidt ta kalli hannunta da Hajiar ta rike tana ja ta yi wani yannayi da fuskarta ta ce" Hajia bari mana kema, baki ga tun dazun so take ki kauce ta dakeni ba? Hajia Duka? La'ila ha ilalahu ai yanzun kuma sai dai na ruwan sama ba dai na dan Adam ba!, Idan takamarta miji ni sai na rantse na fita son Aban shuwwa, Kuma ke furera bara na zube maki zance irin na mahaukata nima kishinki nake ji, abinda kike kishin nan nima ina yinsa kamar na yi hauka, da so samu ne kawai ya daina taba ki kwata kwatama ni ba abinda ya shafeni , Sai dai na san cewa na makaro kuma ko wata zai karro bani da yadda zan yi, ko ba komai gayen da kudinsa da lafiyarsa kayan aiki na amsawa da zarar sun ga nama shikenan sai mu yo son kai mu dane shi? Ki rike da kyau a kunnenki NAHIDt ta yi bariki, ta kuma ajiye bariki ba yau ba, aman tama tare da dabi'u irin na bariki a jinninta , bale an zo kan gabar da idan na buga tsuguni Malan ya dana lada zan samu? Me ya fi raina ga lada ga mando!, Ki zage damtse iya karfinki ki amshi kaya a lokacin da ya dace, bayan wannan baki da yadda zaki yi da ni, idan kuma kin nace bismillah, na baki dama daga yanzu gar mu mutu ki bi dukkan hanyar da zaki bi dan kasheni, na tabata dukkan abinda zai sameni mukadari ne, babu wanda ya isa ya hanna, aman fa kika kuma nuna zaki taba lafiyar jikina sai na zane ki da belt!"

Tana gama fada ta cikata da karfin balaki hakan ya sa ta kai kasa du irin jikinta kuwa sai gata tana haki kamar wace ta yi tsere, dama Furera ba wani karfin ne da ita ba kawai kaifin bakin ne, gashi bata tauna maganarta da zarar ranta ya bace komaima fadi take yi dan ta huce

Hajia kam yau ta ga abu gannin idannuwanta kuma kunnayenta sun jiye mata abu iyakar jinsu

Jikinta na rawa ta rasa inda zata yi, da sauri ta juya ta bi bayan Nahidt din bayan ta ba Furera hakuri

Tana zuwa ta tarda Nahidt din na kokarin bude falonta, tana budewa ta shige da Bismillah a bayane hakan ya sa Hajiarma bin bayanta a sanyaye ta ce" Nahidt ?"

Nahidt ta dakata ta juyo a hankali tana kallonta

Hajia ta ce" Dan Allah ki yi hakuri kin ji? Kar ki ringa biye mata dan Allah, kin san ita Furera wani sa'in tana da irin haka, aman da zarar an kyaleta shikenan komai sai ya wuce, dan Allah kar ki biye mata ku ringa kishi irin na jahiliya kin ji?"

Nahidt ta yi murmushi tana nuna hajia wajen zama
Hajia ta je ta zauna itama ta zo ta zauna a gefe a nutse tamkar ba ita ba ta ce" Hajia, ki yi hakuri, kula shirmen yade yaden magana daban, taba mutunci daban....."
Ta furzar da iska ta ci gana da fadin" Wani lokacin marar kunya na ci gaba da yada rashin kunya ne da tunanin ya zama dole a yi hakuri da halinsa a saurareshi, baya sasauci a rashin mutuncinsa baya tunanin idan shi aka yiwa yaya zai ji a zuciyarsa ne? Sai ki ga har ya zamto abin tsoro a waje bayan mayar da shi wata tsiya da aka yi ya sa yake daukan kansa a haka, da watsi aka yi da shi aka nuna masa shima mutun ne irin na kowa da ya maida kansa mutun irin na kowa din!"

A hankali ta riko hannun Hajiar ta ce" Hajia ban zo gidanku dan mu ringa raba hali da kowa ba, haka kuma ban zo gidanku da wani ya ringa ci min mutunci ba, idan takamarta na yi bariki inaga wannan rayuwata ce da makomata, yau tunda har na yi aure ana iya yi min uzurin zama da ni da ido koda ba'a bini da fatan alkhairi ba, Hajia ta jima tana wulakantani a anguwar nan, ta wulakanta min gudan jinina da nake da a lokacin wace a kanta babu abinda ba zan iya yi ba dan na kareta, dimin nice mamanta, nice babanta, nice komanta..........Hajia haka take shiga tana takawa aman dalilin mai mutunci da ya rabe mu sai na kawar da kaina na kyaleta, aman yanzun bana tunanin zan iya kyaketa ta ringa min haka du haduwarmu, Idan haka ya ci gaba tana iya yi min a gaban jama'a, haka kuma tana iya mayar da ni tamkar mahaukaciya, ....... hajia ni na rayu ne da kwatar yancina da kuma soyayar makusantana, sannan na rayi ne da yakar mai yakina......................ba zan ce maki komai a kan zamantakewata da ku ba, abinda na sani shine zan zauna zuciya daya da kowananku hajia, mu'amalata da kowanenku kuwa zai danganta ne da yadda ya mu'amalanceni, ni ba makiyiyarta bace, ni kishiyarta ce, dole akoy kishi a zukatanmu mu dukanmu.....aman idan har bata iya gyara nata halin ba lalle zamu kwasheta da ita!"

Hajia ta ringa sauke ajiyar zuciya a sanyaye ta ce" Allah ya sanyaya, Allah ya kashe fitinar komai kankantarta, in sha Allah babu abinda zai ci gaba da faruwa sai alkhairi......................, Nahidt dakinki ya yi kyau sosai masha Allah, Allah ya sa a mora lafiya "

Nahidt ta daga kanta tana murmushi tana bin dakin da kallo ta amsa da amen ya Allah, ita kanta ta yi godiya da Allah da ya nuna mata wannan daula a matsayin tata, ta kuma jinjinawa mijin Shuwwa dinta, asge har haka ya yi bajinta? Lalle kanwarta ta samu miji sai fatan zaman lafiya......ai kam zata kirayesu yau ta ce da shi Aba ko zai yi dariya, shi kansa da kafarsa shi babanta ne kkai jama'a.........

Yar hira suka ci gaba da dan tabatawa da hajiar kafin take mikewa ta mata salama ta tafi cike da son tambayarta me take anfani da shi wa hannayenta suke da laushi haka ne? Zata so sannin abin itama ta nema ta jaraba, domin kuwa ita kam ta san darajar gyara, shekarunta a hamsin kadan ne babu aman a duniya idan ka ga Hajia na gyaran jiki sai ka sarra mata, takan je saloon a wanke mata kanta a busar da shi a mata kitso duk sati uku, sannan ta kirayi mai kunshi ta zo ta yanyara mata kunshinta bale na salatif, haka kuma bata wasa da gyaran jiki irin na lalle, ga kuma uwa uba tsafta da kanshi, bata iya hada turaren wuta ba aman fa bata jin ciwon cire kudinta ta sayi turarukan wuta da na humura masu daraja ta shafa ta kuma turara a dakinta.......wannan dalilin na daya daga cikin abinda ke saka Malan manta cewar wai Hajia ta girme shi, to gaskiya ta san darajar kanta ta kuma san tasaa haka kuma tana aiki da sunna, tana kamantawa sosai da sosai shi yasa yake karba yake kuma godiya da yabawa, ga ladabi da biyaya bata taba daga maganarsa ko mecece, ta fa gama da Malan shi yada NAHIDt ta yiwa Allah godiya da ba da Hajiar zasu goga ba, irin kishi da hajia irinsa ne ke saka mutun kuka da idannuwansa, ba zaka iya ba abin mai girma ne, sai jajirtaciyar mace zata iya

Bayan salarr isha'i

Tunda take maganar tana hawaye yake sauraronta da mamaki kafin ya Kalli Hajia sai kuma ya kalli NAHIDt dake zaune Idannuwanta a kasa tana ayana' Zuki kai Furera an iya sherata, wai na zaneta ni? Wai kuma muka yi mata taraya da hajia'

A nutse ya furta" Asha, Subahannalah subahannalah, me nake ji haka duka kuma? Kuma taraya? Me ya faru ne Nana Maryama?"

Hajia ta hadiye yawun bakinta a sanyaye ta ce" Aya Akaramalahu Allah ya huci zuciyarka, eh an dan samu matsala ne aman kuma bai kai ga dukan bama, aka kuma kashe wutar"

"Wace wutar aka kashe Hajia bayan kun min taron dangi?" Ta fada tana kallonta da sake fashewa da kuka ta dora da fadin" Cewa ta yi haduwa goma cin uwa goma Malan"

NAHIDt ta wangale baki da mamaki tana ta tuna anya a maganarta ta fadi haka kuwa? Sai kuma ta boye murmushinta tana ayana' Dama na ce maki haka walahi, maganar ta min dadi'

Malan ya kai dubansa kan NAHIDt da ta masa mugun kyau cikin yahiga ta atampa ta sha dauri da sarka da dankunnayenta masu kyau abinta
Ya dan tsatsareta da ido a sanyaye cikin wani salo mai saka zirya a cikin jiki bayan ya ji ta tsirga masa har kwakwaluwa ta tada kwadayinsa tare da jin son gagauta kasancewa da ita a daka dan ta kuma ba sahiba kula irin ta kulun ya furta" Sayadah "

A hankali ta dago idannuwan nata ta sauke a saman fuskarsa, haka itama Furera ta sauke a saman fuskarta dan ta ji wani sabon salo wai Sayadah yanzun yar barikin ce ta koma sayada a duniyar Malan?

Malan ya dan yi gyaran murya ya ce" Wai kin daki yar uwarki?"
Hajia ta gumtse bakinta dan har ga Allah daria abin ya bata, yo Furerar ta yi trela kawai sai tace an daketa? Da ita watace ko dukan nata aka yi sai ta boge dan kar a yi mata daria, hakan ya sa ta sada kanta daga dubansu tana ta hanna kanta fashewa da daria
Chapter 132 · 0% Book details