← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 138

Sashe 66

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748
Amina Maikudi Abdullahi
GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar
08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Kafafuwansa ya janye gannin so take ta fada masa a kausashe ya ce" Ki kula mana ".................sannan ya sake jan bakinsa ya yi gumm yana kallonta

Nikaf din ta cire itama tana kallonsa da kikifta ido, irin alamu na gaskiya da gaskiyar dake tare da ita,

Ajiyar zuciya ya sauke ya sake kallon wajen diner ya ga wayam, yau babu komai, bayan kwana biyu yakan taba dukan abinda ya samu na tabawa, sannan ua dora shayinsa , sai dai yau matar nan ta yi aiki irin na mata bata yi girki ba

Mikewa ya yi ya dauki kayansa ya juya ya shiga haurawa sama, ita Kuma sai ta samu kanta da raka shi da kallo har ya bacewa ganninta tana hangen hanyar da ya bi

Wani gwauron ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da NAHIDT ta ce" Ke Shuwwa"

A dan firgice ta juyo tana kallonta

Murya ciki ciki ta ce" Yaya kuka rabu? "

SHUWWAR ta sake kallon hanyar da ya haye din sannan ta juyo wajen Nahidt tana sauke wata ajiyar zuciyar again ta ce" Cewa ya yi ki kula mana, shikenan ya tashi ya yi tafiyarsa, bayan na barshi da gidansa yana jirana a waje, ya shigo ban yi gyare gyaren komai ba, uwa uba ban yi girki ba, Nahidt anya ba dana min tarko zai yi ta yadda ina shiga sama zan ji kaina ba a jikin jikina ba?, Kin san fa sojoji dukan matansu suke yi, anya ba tarani yake yi ta yadda laifina zai kai na ya batar da ni shikenan kowama ya huta?, Zuwa yanzu na fara tsoron kyaliyarsa da kawar da kansa a kan neman fitinata"

Nahidt ta shiga kwabe hijab din jikinta tana fadin" Yanzun dai tashi kike yi ki fada kicin, ni kuma bara na yi sallah na fito na shiga gyaran falon, Shuwwa an fada maki kowani namiji ne bai san darajar mace ba kuma bashi da ilimin adini ne? Dan kawai yana Soja baa hakan na nufin yadda yake da tsauri da tsagera da mararsa ji a waje zai kasance mai aikata haka wa iyalinsa, mau be kina auren namiji mai daraja, mai mutunci , wanda zai koya maki son kanki da kanki , mutunta kanki da kanki, uwa uba ya koya maki zama da namiji mai daraja , ya karyata hasashenki, ya birkita zuciyarki da dumin kaunar Soja!"

Tunda take kalaman ita kuma kallonta take yi har ta dasa aya
Ajiyar zuciya ta sauke tana dan girgiza kanta ta juya ta nufi hanyar kicin din tana tunanin me ya dace ta girka masu sasauka a gidan duba da sun yi dare?

Mayafinta ta cire ta ajiye da jakarta mai dauke da wayarta sannan ta karasa wajen frij mai dauke da danyan nama da su kifi, da su naman talo talo

Naman talo talon ta samu ta ciro da kyar ta nufi wajen ruwa ta dauki roba ta saka shi ta kunna masa ruwa sannan ta barshi ya saki da kankarar da ta dafke shi
Wajen dankalin turawa ta koma ta debo mai yawa sannan ta kawo abin bare bayan shima ta ajiye da wata robar da zatana zubawa idan ta bare

Harhada kayan jajage ta yi su tarugu, koren tatasai, da tafarnuwa ta jajaga su sosai sannan ta zuba su a cikin kwalba ta zuba masu Mutarde da mayonaise da garin magin tafi da gidanka da bakin poivre da fari da dan mai ta cakude su sosai sannan ta kawo su ta ajiye wajen kayan aikinta

Naman nan ta cire a ruwan nan ta sake masa wani ruwan, ta samu ta wanke shi tass sannan ta zuba shi cikin abin tsanewa ta sake komawa wajen dankalin nan tana ferewa tana sakawa cikin ruwa da sauri da sauri
Sai da ta kusan rabi sannan ta koma wajen naman nan , zuwa lokacin ya tsane ruwansa tassss, hakan ya sa ta shiga tsatsaga jikinsa duba da manyan yanka ne sosai har uku ta ciro, bata cicira shi kannanu ba sai dan tsatsaga jikinsa da ta yi sosai ta kawo wannan jajagen da ta yi ta shiga shafa masa lungu da sako sosai tana shafe shi da shi
Su dukansu ta yiwa haka sannan ta dauka ta saka a frij wajen yin sanyi ba wajen yin kankara ba ta rufe ta koma wajen dankalin turawanta

Ba ita ta waiga wajen naman nan ba sai da ta gama bare dankalin turawan nan tass sannan ta yanyanka shi dukanshi, zuwa lokacin ta dauki kusan minti talatin ta zuba dankakin turawan a cikin babar roba mai tiloli dan ya tsane ruwansa shima gaba daya sannan ta koma ta ciro naman nan
Anfanin saka naman da ka shafawa jajagen nan a frij shine kayan zasu ratsa shi sosai ta yadda dandannonsa zai fi fitowa sannan zai fi gasuwa komai taurinsa domin hadin nan na saka namaa ya yi laushi ya yi gagawar gasuwa

Abin gashinta ta ajiye ta dauko takardar da ake siyarwa ta gashin nama ko cake t yanka ta saka a cikin abin hashin sannan ta dauki mai ta shafa sosai ta dora yanka biyu ta koma wajen foor dinta da ya gama daukan zafi a 250 wutar sama da ta kasa ta bude shi ta saka naman ta rufe sannan ta rage karfin wutar zuwa 200 dan kar naman ya dauki hanyar konewa bai gasu da kyau ba sannan ta komawarta wajen dankalin nan ta kunna wuta ta dora kasko ta zuba isashen mai sannan ta juya wajen kayan tea dinsa ta shiga harhadowa dasauri da sauri dan ta dora shi gefe shima ya dafa kansa a kan lokaci
Man nan na yin zafi ta yanka albasa karama ta jefa cikin man suyar, hakan na saka dankalin turawan bada wani kanshi mai dadi da dandano
Zuba mai yawa ta yi tana tsaye a gabansa har ya fara ja ta juya shi ta yadda dayan barinma ya dauko jan sannan ta rage wutar ta kwashe shi cikin abin tsanewa, da gagawa kuwa sai ta kawo gishiri na cikin kwanko garin nan ta dan yayafa da zafinsa ta juya shi ta yadda gishirin zai gamu a jikinsa gaba daya sannan ta zube sauran a man ta bar wanda ta kwashe din ya idasa tsane mansa bayan ta yafa kyale mai tiloli gudun wani abu ya fada kafin ta kawo abin zubawa

Nan da nan ta gama aikinta, a awa biyu danma aikin hannu daya ne kuma sai da ta bari ya gasu sosai , zuwa lokacin har ya dawo daga sallar isha'i yana mamakin aikin da yayarta ke sha ba ji ba gani falon ya dauki kanshi an gyara ko'ina masha Allah ya haye sama yana dan dafe cikinsa domin har ga Allah shi baya wasa da cikinsa sam

A hankali take tafia da kayan da ta jera tana adu'ar Allah kaita dinern lafia har ta fito suka hade da Nahidt
A nutse ta ce" Wauh, Masha Allah......Shuwwa wadinnan plat din fa da kayan shayin?"

SHUWWA ta ce" rufa min asiri na ajiye kafin na barar sai na kaiki ki gansu, kulun su ke sake sakani yin sabon girki da su walahi"

Nahidt ta ajiye turaren wutar da take yawo da shi ta kama mata gaban tana fadin " ki rage kayan mana kar garin hawa ki zubar"

SHUWWAR ta ce" Hawa ina kuma? "

Nahidt ta dubeta a tsanake ta ce" saman mana, ko ba dakinsa zaki kai masa ba?"

SHUWWAR ta girgiza kanta
Nahidt ta yi Murmushi tana fadin" mu ai a nan zamu ci ko? Muna so muci cikin sakewa ko? Ki kai masa Kawai mu sai mu baje a nan , domin kanshin gashin nan na halaka min yawu"

Yar dariya ta yi ta gyada kanta ta juya hanyar hawan a hankali tana hawa tana adu'ar Allah ya kaita lafiya da tunanin ko ya ci? Har ta haye sannan NAHIDT ta yi murmushi tana girgiza kai a ranta tana ayana'gidan rigima kennan, da ban yi mata dabarar ba, ba zata Kai ba"

A hankali ta samu ta bude ba tare da ta nemi izini ba domin kayan dake hannunta ko budewar Allah ne ya taimaketa ta iya budewar

A hankali ta shiga da salama a saman lebenta kasa kasa ba tun karfi ba dan kar ta saki farantin

Idannuwanta suka sauka a saman kansa yana zaune saman wata lalausar kujera ya mike kafafuwansa da alkur'ani mai girma a hannunsa yana karatu cen cikin kirjinsa

Samun kanta ta yi da zuba masa ido , ga wani sansanyan kanshi na tashi a dakin wanda ga dukan alamu turaren ruwa ne ya saka mai sanyin kanshi dan yaa ji dadin zaman

A hankali ta karasa ta samu ta ajiye masa a gefensa ta sake zuba idannuwanta a saman gashin da ya lulube kafafuwansa
Haka kawai ta ringa bin jikinsa da kallo dan neman rigima har sukai ido hudu da shi, wanda hakan ya sakata dan hade fuska tana basarwar nan kamar kallonsa ba dan wata niya ta kalleshi ba ta yatsina fuska tana cije lebenta na kasa hadi da juyawa gaba daya ta mike da niyar tafiyarta dan ta kula kallon nan nasa kamar yanai mata kallon kyama ne!

Ajiyar Zuciya ya sauke yana girgiza kansa kasa kasa ya ce" My bed 🛏️"

Turus ta yi ta juyo ta kale shi na yan sekwani sannan ta cire kanta ta nufi wajen gadon
Chapter 66 · 0% Book details