← Book details Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 138

Sashe 13

Alkalamin Kaddara ta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Fuskarta ta hade sosai tana kallonsa ta ce" Ban amince ba "

Daga shi har SHIEF OF ARMY fuskar tata suke kallo a lokacin da ta mike gaba daya tana sake fadin" Ba zai yiwu ba, ban amince da haka ba" ta fice a dakin gaba daya ta nufi bangarenta kanta tsaye hakan ya sa suka bita da kallo kafin MUHYIDEEN ya maido dubansa kan Father dinsa ya ce" Father sai ka barta ta tafi kuma?"

Murmushi SHIEF OF ARMY ya yi yana fadin" Ban san abin ba zai birgeta ba, da ba ta haka muka hayota da shi ba son, aman zamu bita da laluma ka san mata da sarauta gashi dama mamanka da tata sarautar ta tagwaitaka dake mintsininta ana zaman kalauma sai ta ji tana sha'awar rigima da mutane"

Shima murmushin ya yi yana sake maida kansa gefe da barin da Father dinsa yake yana dan dana yatsarsa manuniya tana dan bada kara kadan kadan

SHIEF OF ARMY ya karra gyaran murya ya ce" Ka binciketa waye ya sakata zuba maka abin nan a tea?"

Kansa ya dago yana kallon wajen da yake yana girgiza kansa ya ce" A kasan zuciyata nake jin idan na ji wanda ya sakata hankalina zai tashi"

Da mamaki ya ce" Aman wannan dalilin ne kawai zai hannaka matse mata waje har sai ta sanar maka wanda ya sakata aikata maka haka? Ko kana zargin wani ne baka fada min ba? Muhyideen me yasa ka cika son yin wasa da lafiyarka har da ranka, me yasa ba zaka iya fitowa ka fada min me yake cikin zuciyarka ba?"

Kansa ya dago ya sake kafe fuskar aminin mahaifin nasa da kallo kafin ya furzar da iskar bakinsa yana maida kansa kasa ya furta" Ka yi hakuri Father"

Ya jima yana kallonsa bai iya furta ko A ba , sai da ya gama tunani a kansa kafin ya ce" ka san menene ? Nakan afka wani tunani daban a kanka da irin yadda kake mu'amalantata, na san akoy hali zanen rai, aman kuma nakan ji tunani kala daban daban na shigowa cikin zuciyata a kan mu'amalar dake tsakanina da kai, SON anya ka daukeni a matsayin uba a gareka kuwa?"

Muhyideen ya dago da sauri jin furucin Aban nasa
Yana kallonsa ido cikin ido ya lumshe manyan idannuwansa ya ce" Kai ubana ne, kana da dukan damar da uba yake da a kan y'ayansa, idan ka umarceni na maida wata a cikin matan da na saka ko wacece zan Maida, haka idan ka auren wata ko wacece zan zauna da ita har zuwa lokacin da Allah zai katse zamanmu, na san lamurana a duhu suke, bani da wanda nake zargi a abinda nake gani , asalima ina gudun tsananta bincike a kan hakan, zuciyata ke raya min abinda zan ji na iya daga min hankali, shine kawai Aba"

Ajiyar zuciya SHIED of army ya sauke yana jin kaunar MUHYIDEEN har cen kasan zuciyarsa kafin a nutse ya ce" Na gode yarona, in sha Allah watarana zaka zauna da mace zama mai tsayi, ni na san da haka, kuma ina rokar haka a wajen Allah a kanka, domin auri sakin bashi da anfani haka kuma cikar halitar D'A namiji ya kasance da mace a gefensa........ka je ka fara rarashin mahaifiyarka, a kulun ina sake tunasar da kai ko me kake yi, ka guji daga mata hankali, domin hakan na iya taba komai naka duniya da kiyama, sannan ka daina yi mata shiru idan tana magana ka ringa kokarin amsata ka ji? Ta tsani shirunka ko yayane yana daga mata hankali ainun"

Murmushin da shi ya san ya yi abinsa ya yi kafin ya mike a nutse ya juya cikin tsaftar jiki da ta tafia, cikin kamshi mai nutsuwa da naci, cikin tafiya ta kasaita tamkar wani dan sarki ya bar bangaren ya fito yana sauke ajiyar zuciya hadi da kallon sararin samaniya yana gannin gajimare da ya lulube rana hakan ya haifar da dan lumshi lumshi kadan a garin

"Barka da safia yaya" daya daga cikin y'ayan CHIEF OF ARMY ta fada da kashe murya sosai da kuma sake sada kai bayan dukawar da ta yi again

Kansa ya maido kanta ya yi mata kallo na dan sekwani ya ce" ar u seek?" Domin shi sai ya kamar wata mai ciwo dan gaba dayanta a hade ta Duka din

Dagowa ta yi da sauri tana kallonsa , haka kuma lokaci daya ta ce" Lafiata kalau yaya"

Bakinsa ya tabe ya shiga takawa yana kallon sojojin dake bada tsaro a cikin gidan wa'inda du idan ya karaso sai sun sara masa sannan sun yi jira ya basu damar sauke hannayensu sannan su ci gaba da shawagi a cikin gidan har ya bacewa ganninta

Idannuwanta ta lumshe a bayane ta furta" Ya Allah ka malaka min bawanka , koda yana auri sakin ina so , koda dukana zayana yi ina so"

Yayarta dake hangenta tun dukawar da ta yi ta gaishe da yayan nasu ta gama cika da haushi da mamakin yarinyar, uwa uba da ta ga kamar ya bata amsa yau sai hankalinta ya tashi ta fito ta karaso a lokacin da ya bar wajen tana fadin" Ashe shirmen adu'ar da kike yi kennan ko?, To ki hada da idan na mutu domin ai kin san baban goro sai magogin karfe, Iko da iko yake haduwa ba da yar talaka ba, kin san mahaifiyata ko y'ar waye a kasar nan, nice daidai da sarautar MUHYIDEEN ba kowace y'a ba, ki ringa daidaita adu'ar taki kina fadin aman idan na mutu domin idan da raina kin san ban yi kama da wada zata bar yar da aka auro uwarta dan tausayi ta kwace mata miji ba"

Sosai magangannun nan suka doketa, hakan ya sa ta murje idannuwanta ta dubeta itama tana fadin" Ashe kuwa da an fadi ba nauyi, da an yi kukan rashin yar masu sarautar duniya a gidan SHIEF OF ARMY, ni aunty wani lokacin saima ki manta cewa da Uba ake ado ba da riga ba walahi!, Gaki ke kuma manya sun ce ba shegiya bace bale na fahimci yadda kika cika bugub kirji da dangin iya..........koda yake ba kowa ne ya yarda cewa dan adam haka yake zuwa duniya ba da tare da an hado masa da jarin sisi ba, Allah ne ya azurta shi..........................kowa ya nemi sa'arsa ta hanyar da ya ga zata gyara shi, aman ki sani marar gatan nan dai nice, kina ji kina ganni zan fi kowace y'a dace da zama matar LIEUTENANT GANARAL MUHYIDEEN MUHAY"
Tana gama fada ta yi tafiyarta ta bar yayarta tsaye baki sake tana kallon hanyar da ta bi kafin itama ta yi kyaptu ta furta" Mu zuba mu gani"

___________________________________

Tunda ya zauna ya tankwashe kafafuwansa ya sakata a gaba ta hade fuska tamau tamkar bata taba yin daria ba

Sake kure fuskarta ya yi da kallo irin na kauna da begen mahaifiyar tasa

Du yadda take cire kai tana sake hade gabas, da yama, kudu da arewa dan kar ta saki ya samu damarta abin ya gagara domin daga karshe sai da ta kafe shi da kallon itama tana fadin" Kai bara ka ji ba sakani da ka yi a gaba ba ba inda zaka je, na ce ba inda zaka tafi"

Murmushi ya yi fafaden murmushin da ya bayanar da tsaftatun hakoransa a hankali ya ce" Na yarda "

Tsai ta yi lokaci daya tana kallonsa
Ya yarda fa ya ce?
Kai tsaye ya yarda da maganar nan? Ina da wata a kasa, ta tabata da wata a kasa, akoy abinda suke shirya masa shi da Abansa dan haka ta nuno yatsarta manuniya a kansa tana fadin" Ka ga MUHAY ka fito sak a mutun ka fada min abinda yake cikin zuciyarka, tafiyar nan ce na ce bana so ba zaka yi ba, a kan me ka hakura haka kai tsaye? Meye kake shirya min ne?"

Tsakani da Allah da ya iya daria irin ta kyakyacewar ban, to da babu abinda zai hanna shi kyakyacewa da daria a gaban mahaifiyarsa, sai dai duda haka a hankali ya ringa alamu na zuciyarsa ta shiga cikin shauki da farin ciki harma ya iya budar bakinsa ya ce" Mama, kika ce bakya so, na ce shikenan na fasa kuma sai ki ce da abinda nake shiryawa? Nake shiryama mamana kuma?"

Fuskarsa ta sake kurewa da kallo tana kankance idannuwanta tana shiga shauki na kallon yaron nata na bayanar da farin cikinsa a sanyaye ta ce" Na sani ne? MUHAY sha nawa kana fitowa a haka ba'a san gabanka ba bale bayanka?"

Ajiyar zuciya ya sauke yana fadin" Koda wani bai sani ba, banda Umuna, tunda kika ce bakya so na fasa ba zan je ba"

Mtsssssss haka kawai take ji a kasan zuciyarta ya dai ce ya fasa ne, yana iya fita a kowani lokaci ya yi tafiyarsa, hakan ya sa ta sake kureshi da kallo har ya sada kansa kasa a sanyaye ya ce" Aman idan har kin ji kin aminta, ba yanzu ba ko nan da shekara goma ne, idan ina daya daga cikin masu rai, kikai shawara kika ga ya cencenci na je garin nan dan na samu lada, idan kika ce MUHAY ka je Allah ya yi maka albarka , zan je Mamanah"

Yan yatsunta biyu ta hade har suka yi dan karra tana fadin" Ha, na sani, ni na san baka bar maganar ba, ni zaka yiwa wayau MUHAY ?"

Kansa ya girgiza yana sake saka idannuwansa cikin nata yana alamun da yake sakata saurin amince masa da abu

Kai ta cire tana cire idannuwanta a cikin nasa tana fadin" Ba zan taba amincewa da nisan aiki irin wannan ba, kawai ka cenza shawara"

Murmushi ya yi ya mayar da bakinsa ya dinke , hakan ya sa ta ringa yin murmushin itama na doguwar maganar da ya yi yanzun, ta tabata da ace ba a kan aiki bane ba zai yi magana haka ba
Chapter 13 · 0% Book details